Sashe 62
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren Sadik kuwa tun ranar da ya yiwa Neehal text bata masa reply ba kuma yana kiranta bata ɗauka, sai hankalinsa ya tashi. Gaba-d'aya ya ji duniyar ta masa zafi, ga wani sabon son ta dake ƙara mamaye masa zuciya da gangar jiki. Cikin kwanaki kaɗan ya rame saboda damuwar da ya saka a ransa. Hotunan Neehal su suka zama abincinsa, dan kodayaushe cikin tasa wayarsa a gaba yake yana kallon pics ɗinta. Duk wani program da take a gidan TV kuwa ba ya wuce shi. Mahaifiyarsa ta tambaye shi me yake damunsa haka duk ya fita daga hayyacinsa? Sai ya ce mata "Wani case yake ne mai wahala, ta taya shi da addu'a kawai." Ganin abun Neehal bana ƙare ba ne shine jiya ya shirya ya je gidansu Haneefah, ya faɗa mata duk abun da ke faruwa, Haneefah ta kwantar masa da hankali ta ce zata je ta samu Neehal ɗin, kuma ta san ta yanda zata ɓullo mata kar ya damu. To bayanin Haneefah ne ma ya ɗan kwantar masa da hankali. Yau kuma yana masallaci ya ji message ya shigo wayarsa, ya yi zaton ma kamfani ne amma da ya duba sai ya ga Neehal ce ta turo masa. Jikinsa har rawa yake yi wajen shiga ya karanta message ɗin zuciyarsa cike da fargaba. Wani sanyi ya ji ya ratsa zuciyarsa gami da farin ciki mara misaltuwa ganin abun da Neehal ta turo masa, a fili ya furta Alhamdulillah yana sakin murmushi shi kaɗai. Duk wannan murnar da Sadik yake ba fa wani abu Neehal ta ce masa ba a cikin text ɗin. Ta tambayi lafiyarsa ne kawai, a ƙarshe kuma ta nuna tana son ganinsa Yau idan babu damuwa. Amma shi a gurinsa hakan alamun nasara ne, dama tun d'azu zaman jiran kiran Haneefah yake domin ta sanar masa yadda suka yi da Neehal ɗin, sai kuma ya ga text ɗin Neehal ɗinma a lokacin da bai taɓa tsammani ba. Cikin sauri ya tashi ya nufi gida, jikinsa har rawa_rawa yake dan zumud'i. A hanzarce ya shirya cikin wani yadi milk colour ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin k'amshi ya fito ya ɗauki hanyar gidansu Neehal.
Itama Neehal ɗin ba'a barta a baya ba, wanka ta yi ta shirya cikin wata gown purple colour wanda ta zauna das ajikinta, ta kuma haska farar fatarta. Ta shafa powder a fuskarta gami da White lipsticks a lips ɗinta. Ta yi kyau sosai fuskarta sai annuri take, ita kanta ta san She Missed him over, zuciyarta cike take da d'okin ganin kyakkyawar fuskarsa ɗauke da murmushinsa da ba ya rabo da shi kodayaushe. Tana jin wayarta ta yi ƙara ta ji gabanta ya ɗan faɗi, kamar yadda ta yi zato tana dubawa ta ga shine, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga amma ba ta ce komai ba. Lumshe idonta ta yi tana sakin ajiyar zuciya a hankali jin muryar Sadik yana mata sallama, a sanyaye ta amsa masa masa. Yana jiran ta a waje kawai ya sanar mata sannan ya kashe wayar, kamar ya san kuwa da ya ce wani abun ba zata iya ce masa komai ba. Ta yafa mayafinta sannan ta fito falo, anan ta tarar da Mama ta tasa su Amrah a gaba suna Assignment. Kanta a ƙasa ta ce "Mama zan sauka ƙasa Yaya Sadik ya zo." Mama ta bita da kallo sannan ta ce "Okay ki gaishe shi." Su Afrah sarakan son yawo suka bi ta da kallon a tafi da su, Neehal tay murmushi ta shafi kuncinsu sannan ta fita. Inda suke zance da Anwar ta saka aka kai musu kujerun roba, tunda yau Sadik ɗin ya ƙi shigowa falo. Allah sarki rayuwa har ta tuna da sanda Anwar yake zuwa zance, ta hango zuwansa na ƙarshe gidan, sai ta ji zuciyarta ta mata rauni kamar zata yi kuka. Sai da ta mayar da k'wallar data tarar mata a ido sannan ta ƙarasa gurin cikin sanyin jiki. Tun da ta taho ya ƙura mata ido cikin shauƙin k'aunarta yana sakin ajiyar zuciya. Sai ya ga kamar ta ƙara kyau da iya tafiya a kwana biyun da bai ganta ba. Kanta a ƙasa ta ƙarasa tare da yin Sallama cikin siririyar muryarta. Sadik ya amsa mata cikin kulawa da k'auna yana jifanta da wani irin kallo da murmushin nan nasa manne a kan fuskarta. Ta zauna cikin tsananin jin kunyarsa akan abun da ta yi masa, kuma dama can ita naturally ɗinta tana da jin kunyar wanda take so. A hankali ta ce "Ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau sarauniyar birnin zuciyar Sadik." Ta ɗan kalle shi amma ba yanda za su iya haɗa ido ba, sai ta ga ya ɗan rame duk da manyan kaya ya saka. Tausayinsa ta ji ya cika mata zuciya. Ganin yanda ta takure ta hana kanta sakewa sai Sadik ya fara da zolayarta da ya saba, har ya samu ta ɗan fara sakin jiki amma duk da haka ta ƙi d'ago kanta ta kalle sa. Cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah Yaya Sadik ka yi haquri da abunda na maka, nima ba son raina ba ne, sai dan wani dalilin daban." Sadik ya yi murmushi mai sauti ya ce "Kar ki damu Neehal, tun farko dama na fahimce ki kuma na san haka zata faru, dan haka wannan ba komai ba ne, ki manta kawai. Alfarmar da kika mun ma har na samu ganin kyakkyawar fuskarki a yau ya tabbatar mun da ina wani matsayi a gare ki, ko da kuwa matsayin mai goge miki takalmin ƙafarki kika bani zan yi farin ciki da hakan." Neehal ta d'ago da sauri ta kalle sa, ya kashe mata ido ɗaya wanda yasa ta ji tsigar jikinta ta ɗan tashi hakan yasa ta yi saurin mayar da kanta ƙasa. Ya cigaba da magana da faɗin "Kina mamaki dan na ce miki ko da matsayin mai goge miki takalmi nake a gurinki zan yi farin ciki sosai da hakan? Neehal a yanda nake jin sonki a cikin zuciyata ko da bawanki kika mayar da ni zan yi farin ciki da hakan sosai, ni indai zan kasance dake a kodayaushe ina ganin kyakkyawar fuskarki to zan yi farin ciki gami da alfaharin haka." Neehal ta ce "Haba Yaya Sadik ka daina faɗar haka, matsayin da kake da shi a gurina kafi ƙarfin na mulke ka sai dai kai ka mulke ni." Cikin jin daɗin kalamanta ya ce "Are you Sure! Neehal matsayina har ya kai haka agurinki?" Ta yi murmushi tare da rufe fuskarta da hannunta. Kafin Sadik ya tafi yau sai da suka gama fuskantar junansu yanda ya kamata, har tahirinsa ya bata a tak'aice. Har sai da Mama ta kira ta a waya sannan suka yi sallama ya tafi bayan ya ce ta gaishe da Mama, tun da a suruki ya zo gidan yau ya ƙi shiga ciki.
Soyayya sosai Neehal da Sadik suke, Haneefah kuwa ta samu abun tsokanarta, matar Barrister ma ta koma ce mata. Mama ma tana lura da ita a kwanakin nan Sadik ya bar Friend or brother ya koma Habibi. Ta kuwa ji daɗin hakan sosai, sai ta ƙara dagewa da k'aimi gurin yi musu addu'a akan Allah yasa Sadik shine mijin Neehal. Sadik ya iya tafiyar da mace yanda ya kamata, ga tarin kyautatawa da daɗaɗan kalamai wanda suke ƙara dulmiyar da Neehal a kogin k'aunarsa. Ranar Asabar ta kasance ranar farin ciki ga kowane musulmin duniya, saboda tashi da azumin watan Ramadana mai girma da ɗaukaka da akai. Ranar da aka ɗauki azumi na Shida su Mama suka tashi zuwa ƙasa mai tsarki ita da Aunty Sadiya dan yin Umrah. Gidan Aunty A'isha su Neehal suka koma kafin Mama ta dawo, wannan karon har da su Dije suka tafi. Mama ta yi addu'a sosai a gaban ka'aba akan Allah ya kawo ƙarshen ƙaddarar Neehal gami da tona asirin duk masu hannu a kisan su Anwar............
*TWO MONTHS LATER*
Neehal ce ta fito cikin shirinta na tafiya school, a kitchen ta tarar da Mama tana yin lunch, ta cewa Maman. "Mama zan tafi school." Mama ta ce "Har kin gama karatun?" Da yake Neehal ɗin sun fara exam ɗin second semester level three. Ta ce "Eh, na ga 2 ta wuce, kuma ƙarfe 3 zamu shiga exam ɗin. Mama ta ce "Allah ya kiyaye ya ba da sa'a, ki biya fa ki dubo Yayanki kar ki manta." Neehal ta ce "Zan je Insha Allah, zan kira Haneefah ma idan tana free sai mu je tare, idan ma tana School ɗin sai mu wuce ta can kawai." Mama ta ce "Shikenan ki masa sannu." Neehal ta ce "Zai ji." sannan ta juya ta tafi. Kamar kodayaushe tsawon watanni ukun nan da suka wuce kullum Neehal ta fita sai Motar nan ta bita a baya, idan zata school,aiki,shopping da unguwa duk tana biye da ita a baya. Ita har mamakin ma yanda mai Motar yake sanin time ɗin fitarta dana dawowarta take sai ka ce aljani. Kuma har yau bata taɓa faɗa wa kowa ana bin ta ba, Ubangijinta kawai take faɗawa, dan babu mai bata kariya sama da tasa. Bata son kuma ta d'agawa Mama hankali shi yasa bata faɗa mata ba, duk da a zahirin gaskiya a tsorace take da bin ta da ake yi ɗin. Watarana ta kai su Afrah shopping a hanyarsu ta dawowa motar tana bin ta sai ta ce a ranta bari ta gwada wani abu. Parking ta yi a gefen titi ta kulle su Afrah a cikin motar sannan ta shiga wani shago da ake sayar da zobuna da agogo, ta ɗauki zobe ɗaya ta siya duk da bata fito da niyyar hakan ba. Bayan ta fito daga shagon ta kalli titi ta bayanta ko zata ga motar nan amma bata ganta ba. Amma abun mamaki bayan ta shiga tata motar bata fi 3 minutes da fara tafiya ba ta hango motar tana bin ta a baya. Hakan ya tabbatar mata da abun da take tunaninta akan wani ne yake bibiyarta, kuma koma waye Allah ya fi shi.