← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 118

Sashe 72

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sai da suka shiga Mota sannan Neehal ta dubi Ameen ta ce "Yaya ina zamu?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Siyar dake zan yi." Jin haka yasa ta ja bakinta ta tsuke. Har suka ƙarasa wani had'ad'd'en Bakery dake cikin Nasarawa babu wanda ya ce uffan. Ya yi parking ɗin Motar ya fito itama ta biyo bayan shi suka shiga gurin. K'amshin abinci irin me tsinka yawun nan ne ya fara musu welcome. Gurin ya haɗu sosai kuma babu hayaniya ko kaɗan. Suka zauna a kujerun dake zagaye da table suna fuskantar juna. Ameen ya ɗauko wayarsa ya shiga latsawa, ita kuma ba ta fito da waya ba ta baro ta a gida, kallon gurin kawai take cike da burgewa. Wani ma'akaicin gurin ya kawo musu takarda mai ɗauke da duk wani abu da suke siyarwa a gurin tare da price ɗinsa. Ameen ya karɓa ya duba tare da selected ɗin abun da za'a kawo musu. Bayan mintuna biyar ma'aikacin ya dawo ɗauke da madaidaitan plates guda biyu a hannunsa, a gaban Neehal ya ajiye su duka kamar yadda Ameen ya ce masa. Neehal ta kalli snacks ɗin yawunta na tsinkewa saboda k'amshin daya bugi hancinta. Plate na farko meatpie ne a ciki da Spring rolls da samosa. Plate na biyu kuma Pizza and shawarma ne a ciki. Sai kuma Juice and bottle water a gefe, sai tissue. Ba tare da Ameen ya kalle ta ba yana cigaba da latsa wayarsa ya ce "ki yi sauri ki ci." Ta dube shi ta ce "Kai fa?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Ba ta kuma cewa komai ba, ta yi Bismillah ta fara ci cikin nutsuwa. Cin abincin Neehal babu sauri, kafin ta gama fiye da mintuna ashirin sun wuce, kuma bai fi rabin abun da aka ajiye mata ta ci ba. Bayan ta gama, ya je ya biya kuɗin tare siyan wasu snacks ɗin, a leda biyu aka yi masa packaged, ya karbo suka baro gurin. Daga nan gurin shan Ice cream da siyar da su chocolate ya kai ta, suka shiga ya ce ta ɗibi abun da take so. Neehal masoyiyar choculate da wafer ta diba son ranta ya biya kuɗin suka fito suka nufo gida, lokacin har an yi isha'i. Suna hanya Hafsah ta kira shi, da ya duba ya ga ita ce sai ya ƙi d'agawa. Sun kusa zuwa gida ta ji Muryarsa ba tare da ya juyo ba ya ce "Ko mu ƙara zuwa wani gurin?" Neehal ta ce "A'a dare ya yi." Ya ɗan kalle ta ya ce "Ko dai wannan saurayin naki ne zai zo kike sauri ki koma gidan?" Ta ce "A'a wallahi, ka san idan muka daɗe Mama za ta yi faɗa." Ya ce "Hmmm." Kawai. A parking space ya ajiye ta bayan sun ƙarasa gida, ya bata ledodin ta ya ce ta gaishe da Mama shi ya wuce, ta yi masa godiya sannan ta nufi part ɗin Mama. Tana jin zuciyarta ta mata sanyi akan bata mata ran da Haj Saratu ta yi. Sosai ta ji daɗin fitar nan da sukai, ko dan ta daɗe bata fita irin guraren nan ba ne? 

Ba ta tarar da su Hameedah a falo ba, da alama sun shige ɗaki, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yay mata ba. Ɗakin Mama ta nufa ta tarar da ita tana shirya kaya a wardrobe. "Mama na dawo." Ta faɗa tana zama a gefen gado. Mama ta ce "Sannunki da zuwa, ina Ameen ɗin?" Ta ce "Ya wuce gida." Mama ta ce "Ina kuka je ne?" Neehal ta ce "Wani Bakery ya kai ni, sai kuma muka biya muka siyi Ice cream." Mama ta ce "Shine dan wulaqanci ba zai je da Matarsa ba sai dai ya zo ya ɗauke ki." Neehal ta yi dariya ta ce "Kai Mama, itafa ta zama cuss yanzu tunda matar Aure ce, da ƴan mata ake fita, kuma itama ya siya mata nata, kema ga naki ya ce na kawo miki." Mama ta ce "Ko ma da jarirai ake fita daga yau ya dinga fita da matarsa." Mama ta ƙarasa zancen tana duba ledar da Neehal ta ajiye. Neehal ta miƙe ta ce "Bari na je na yi sallah." Mama ta ce "Tom." Tana shiga bedroom ɗinta ta dauko wayarta, kamar yadda ta zata missed call ɗin Sadik ta gani har biyu. Tana ƙoƙarin bin bayan kiran nasa wani kiran ya shigo amma da new Number. Ta d'aga ba tare da ta ce komai ba. Muryar Amrah ta ji ta ce "Hello Aunty." Neehal tana murmushi ta ce "Sweetheart, ke ce? ya kike?" Amrah ta ce "Lafiya k'alau Aunty, yaushe zaki zo?" Neehal ta ce "Soon In sha Allah, ina Afrah?" Ta ce "Tana toilet tana tutu." Neehal ta ce "Ina Ummi da Aunty Zahra?" Amrah ta ce "Suna gida, mu kuma muna gidan Daddy." Neehal ta ce "Anan zaku kwana?" Ta ce "A'a, idan Afrah ta fito daga toilet Daddy zai mayar da mu gidan Ummi." Neehal ta ce "To ƴar gidan Daddy ina Daddy'n?" Amrah ta ce "Gashi nan, yana jinki." Ta ce "To ki gaishe shi." Muryarsa ta ji a maimakon ta Amrah, cikin marairaicewa  ya ce "Uhm, ke baza ki gaishe ni da kanki ba kenan?" shiru ta yi, jin muryarsa a bazata ya sa ta ji wani abu a cikin zuciyarta, har da lumshe idanunta ba tare data sani ba, tare da tunanin a ina kuma ya samu Numbern'ta? 'A gurin Zahra.' zuciyarta ta bata amsa. A kasalance gami da shagwab'arta ta ce "Ina yini." Ya kwaikwayi muryarta ya ce "Lafiya k'alau Aunty, ya Mama." Ta turo baki gaba kamar yana kallonta ta ce "Tana nan k'alau." Ya ce "My regard to her." Daga haka ya miƙawa Amrah wayar jin Afrah tana kwad'a masa kira daga toilet. Suka ci-gaba da hira da Amrah tana bata labarin school ɗin da aka mayar da su, har Afrah ta fito daga ta karb'i wayar tay ta mata surutun ta ita ma, ganin dare yana yi Ahmad ya ce su mata sallama zai mayar da su. Bayan sun gama wayar ta bi wayar da kallo kamar zata ga yaran a ciki. Sosai take jin kewarsu a cikin ranta, musamman in ta zo bacci sai ta ji gadon ya mata faɗi ita kaɗai, ta saba da, da twins manne a jikinta. Tashi ta yi ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da dauro alwala ta fito ta yi Sallar isha'i. Bayan ta idar ta kira layin Sadik amma bai ɗauka ba, hakan yasa ta kunna data ta shiga yanar gizo. Jimawa kaɗan Sadik ya kira ta, ta d'aga da sauri dan yau gaba- ɗaya ba su yi waya ba, ta yi kewarsa ba kaɗan ba.
Chapter 72 · 0% Book details