← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 118

Sashe 105

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Neehal sun koma school inda suka ɗora karatunsu na final year first semester, 8 weeks da suka wuce, and now suna shirye_shiryen fara first semester level Four exam. A ɓangaren soyayyarta da Ahmad da Sadik kuwa kowa yana nan yana zuba mata gwanintar shi, ita kuma ta dage da addu'ar neman zaɓin Allah. Every weekend sai Ahmad ya zo Kano ya gan ta, sai da randa aka samu wani akasi ne ba ya zuwa, jiki da jini sai Allah. wani Ikon Allah ba su taɓa haɗuwa da Sadik ba, sai dai sun haɗu da Ameen ba iyaka, dan shi kullum sai ya zo gidan da daddare. Har wata rana ya kasa haquri ya tambayi Mama, wai me Ahmad yake zuwa yi gidan ne, A tak'aice Mama ta ce masa zumuncin Allah yake zuwa. Kafin Neehal su koma school ta je Gombe ta kwanar musu biyu, haka ma ta je Abuja gidan Yayan Dad da gidansu su Hameedah, har gidan su Ahmad ta je. Ta ga karamci da k'auna a gurin ahalin Ahmad, twins suka dinga murna Aunty ta zo gidan su. A ɓangaren Sadik kuwa, bayan mahaifinsa ya gudanar da binciken da ya ce zai yi ya zo ya sanar musu cewar gaskiya ne abun da Umma take faɗa akan Neehal. Hajiyarsu da Kawu suka ce dole sai dai Sadik ya rabu da Neehal ya nemi wata yarinyar ya aura. Shi kuma ya ce ba zai iya ba, dan ba zai iya rayuwa babu ita ba, ya ƙi ci ya ƙi sha, ya tada hankalinsa, damuwar da ya sanya wa ransa gami da yunwa suka taru suka haifar masa da ciwo mai tsanani, wanda har ya kai shi ga kwanciya a gadon asibiti. Hankalin Maamah dana Abba ya tashi ba kaɗan ba, Maamah ta kira iyayenta ta sanar musu halin da ake ciki. Mahaifin Maamah da ya zo duba Sadik ya ji abun da yake faruwa yay ta faɗa, ya ce wannan ba hujja ba ce wadda za'a hana Sadik auren Neehal, da mutuwa da rayuwa duk a hannun Allah suke, sai ya rabu da Neehal ɗin kuma idan kwanansa ya ƙare dole ya tafi, dan haka shi zai tsayawa Sadik ɗin a auransa da Neehal, tunda ita yake so. Wannan magana ta Abeey (mahaifin Maamah) ita ta sanyayawa Sadik rai gami da ƙwarara masa gwiwa, har ya fara kwantar da hankalinsa ya samu lafiya. Hajiya da Kawu kuwa suka ce babu saka hannunsu a wannan al'amarin, dan haka duk abun da ya faru da Sadik babu ruwan su. Abeey ya ce "Babu abun ma da zai faru Insha Allahu sai Alkhairi." Abbansa kuwa bin al'amarin kawai ya yi da addu'a, dan ita ce mafita. Sadik ya so tun lokacin a zo a yi maganar auran su da Neehal, amma Maamah ta dakatar da shi ta ce, ya bi komai a sannu, ya bari ya ƙarasa ginin gidansa and kuma akwai lefe, dan haka idan ya gama shiryawa sai aje a yi maganar auren, a saka lokaci ƙanƙani a yi a wuce gurin.

A month ɗin da ya wuce ne asirin Safeenah wadda tasa aka sace su Afrah ya tonu. Ta hanyar Gaye wanda jami'an tsaro suka samu nasarar kama su shi da yaransa akan dukan da suka yiwa Saudart. Bayan an kama sun ne ya yi bayanin dalilin dukan da sukay mata. Daga Zariya aka je har Abuja aka kamo Safeenah, wadda zuwa lokacin duk ta fige ta rame saboda zullumi da tsoro. Babu wanda bai yi mamakin jin Safeenah ce ta saka a sace su Afrah ba, kasancewar ta ƙanwar Mahaifiyarsu ta jini. Mamanta tay ta kuka tana Allah wadai da halin ta, duk da ba shiri suke da Ammi kishiyar ta ba, amma bata taɓa tsammanin ƴarta zata cutar da ahalinsu har haka ba. Ahmad ma ya sha mamaki ba kaɗan ba, duk da ya san Safeenah tana sonsa amma bai taɓa tunanin son zuciyarta har ya kai haka ba, dan shi a gurinsa wannan hauka ne da jahilci ba so ba, dan duk mutumin da yake k'aunarka to zai so ƴaƴanka. Safeenah ta yi nadama mara amfani ita da ƙawarta Saudat, dan har ita Alk'ali ya tisa prison bayan an gabatar da su a gaban kotu bisa laifin bayar da kwangilar kisan kai, duk da bata gama warkewa daga jinyar dukan da yaran Gaye sukay mata, sai dai an cigaba da ɗora ta akan magani a gidan kason.

Yau ta kama ranar Alhamis, misalin ƙarfe huɗu da mintuna na yamm Neehal ta dawo gida daga school. A falo ta ajiye handbag ɗinta da sauran tarkacen school, kitchen ta nufa saboda hango Mama da ta yi a ciki. "Mama sannu da aiki, I'm back." Ta faɗi haka bayan ta shiga kitchen ɗin. Mama ta ce "Sannunki da zuwa, shine zaki shigo mun babu sallama." Ta ƙarasa ta rungume Mama ta baya a shagwab'e ta ce "Na yi sallama fa ba ki ji ba ne. Mama duk na gaji yau ɗin nan." Mama ta shafi kuncinta ta ce "Ki je ki yi wanka ki sakko ki abinci, idan kin huta akwai maganar da za mu yi." Ta bar jikin Maman tare da faɗin "Tom Mamana, Yaya ya kawo miki saqo ki bani?" Mama ta ce "Ya kawo tun safe, ki duba kan mudubi zaki gani." Ta ce "Me ya kawo mun?" Mama ta ce "Ban duba ba, ki je ki gani, zaki gan shi a cikin leda." Ta juya cikin murna ta fice daga kitchen ɗin. Ɗakinta ta fara shiga ta yi wanka, bayan ta shirya ta je ɗakin Mama ta ɗauki ledar da Ameen ya kawo mata ta buɗe. Kwalin sabuwar waya ta gani kamfanin iPhone, ta shiga buɗe kwalin da sauri ta zaro sabuwar wayar ta shiga jujjuya ta a hannunta cikin tsananin murna, da sauri ta tashi ta sauka ƙasa ta shiga kwad'awa Mama kira. Mama ta fito falo da sauri jin kiran tana faɗin, "Ke lafiya kike mun wannan kiran?" Ta rungume Mama tana murmushin farinciki ta ce "Mama Yaya ya siyo mun sabuwar phone." Mama ta yi murmushi tare da zare ta daga jikinta ta karɓi wayar tana kallo ta ce "Congratulation Dear, Ameen ya hutar da ni, na huta da mitar kullum Mama anyo sabuwar waya kaza ki siya mun ko ki sa Dad ya siya mun." Neehal ta yi dariya ta ce "Mama tun sanda result ɗinmu na last semester ya fito na nuna masa, da ya gani shine ya ce na yi ƙoƙari sosai me nake son na siya mun? Na ce masa kome ne ma ina so. Ni har na manta mun yi haka da shi, ashe shi bai manta ba yana sane. Jiya da ya zo da daddare shine ya ce mun zai kawo mun sak'ona  yau na alƙawarin da yay mun." Mama ta ce "Ya kyauta sosai, sai kira shi ki yi masa godiya." Ta ce "Toh Mama bari na saka wayar a chaji." Mama ta bata wayar ta koma sama. Bayan ta saka chajin ta sauko ƙasa ta ɗebo abinci ta ci.
Chapter 105 · 0% Book details