Sashe 3
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya ta buɗe ido a hankali tana salati, tashi zaune ta yi tana mutsitstsike ido, duban Haneefah da take dariya ƙasa_ƙasa ta yi ta ce "Ai dama nasan sai ke, dan Neehal dai ba za ta yi mun wannan muguntar ba, To ke da Allah, ina cikin baccina mai daɗi kin katsemun ko uban me zan miki idanna tashin Oho?" Haneefah ta tsuke fuska ta ce "Hajiya dan na tashe ki ki ci abinci ki yi Sallah, shine za ki ce mugunta, gani na yi ke bakya wasa da Sallah kuma lokacinta ya kusa" Hajiya ta ce "To yi haƙuri ai ban sa ni ba, yaushe ki ka zo gidan? ya kuma Maryam ɗin?" Haneefah ta ce ɗazu na zo ai, na tarar ki na ta sharar baccinki, Mommy kuma tananan Lafiya k'lu" sakkowar Mama ƙasa ya katse musu maganar da suke, Haneefah ta mik'e ta je ta yi hugging Mama. Mama na murmushi ta ce "Welcome, yaushe ki ka zo?" Haneefah ta ce "Na ɗan jima" Mama ta ce " sannunki, Ya Barrister ɗin?" Haneefah ta ce "Tananan klu" Mama ta kalli kofar kitchen ta ce "Neehal ba ta gama girkin ba ne, ta yi ta fito ku shirya ku tafi kar ku yi late" kafin haneefah ta ce wani abu Neehal ta fito daga kitchen d'in, Mama ta bita da kallo fuskarta ɗauke da mamakin ganin ta a shirye, Neehal ta ƙaraso kusa da su ta ce "Mama na gama abincin" Mama ta mata wani kallo ta ce "To sannu" Sannan ta juya ta kalli Haneefah ta ce "Kin taya ta girki ko?" Haneefah ta sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, Mama ta ce "Ba magana nake miki ba Haneefah?" Haneefah ta ce "Mama ƙarasa mata miya kawai na yi, na ce ta je ta shirya dan mu yi sauri mu tafi" Mama ta ce "Ba na ce ko sauke abu ki dena taya ta da shi ba, ki barta ta dinga yin komai da kanta" Haneefah ta gyad'awa Mama kai. Neehal ta ɗan turo baki gaba ta wuce za ta ɗauki jakarta, Mama ta ce "Kun ci abincinne?" Haneefah ta ce "Na k'oshi Mama, ina gama cin abinci na fito, sai dai idan mun dawo" Mama ta dubi Neehal ta ce "Ke fa?" Neehal ta ce "Ni ma haka" Mama ta ce tunda kin cika cikinki da kayan zak'i ba, ki wuce kitchen ki d'ebo abinci ki ci kar na ɓata miki rai" Neehal ta ɓata fuska, amma ba ta da zaɓi sai bin umarnin Maman, kitchen d'in ta koma ta d'ebo abinci kaɗan a plate ta dawo falon ta zauna a ƙasa ta fara ci kamar ba ta so, ta na ci ta na yamutsa fuska, kaɗan ta ci Mama ta ce ta tashi su tafi, tun da ɓata musu lokaci kawai take ba cin abincin za tay ba. Neehal na duban Mama da Hajiya ta ce "Sai mun dawo" "Mama ta ce ƙarfe nawa za ku dawo?" Neehal ta ce "8" Mama ta ce "8 ina Hospital" Neehal ta ce "Mama yau fa Saturday me za ki yi a Hospital kuma?" Mama ta ce "Akwai patients d'in da zan duba ne" Neehal ta ce "Toh, idan mun tashi zan biya Zoo road na siyo popcorn a a'one" Mama ta ce "In ma a 10 ne ba damuwata ba ce, kin san Yayanki na gida ai, 8: 15 in ba ki dawo ba, ke da shi ne" Neehal ta ɓata fuska ta yi gaba, Haneefah ta yi wa su Mama sallama, Mama ta musu addu'a suka tafi, Hajiya na faɗin "Wai yaushe zaku kai ni gidan talabijin d'innan naku ne nima a hasko Ni a ciki?" Suna jin ta suka mata shiru. Parking space suka nufa suka shiga Mota Driver'n Neehal ya ja su zuwa *ASTV* fitaccen gidan TV'n da ya shahara a nan ƙasarmu Nigeria dama nahiyar Africa baki ɗaya.
Ƙarfe 8 kamar yadda Neehal ta ce suka tashi daga gurin aiki, bayan sun gama gudanar da shirin *'Yancin mata* wanda suke yinsa duk Ranar Asabar da misalin Æ™arfe 7 na dare zuwa 8. Su na gamawa suka yi sallama da ma'aikatan gidan TV suka nufo gida, Neehal ta yi_ta yi Haneefah ta bita ta gidansu kamar yadda take yi wani lokacin amma ta ce ita gida za ta wuce, sai da suka biya suka fara sauke ta sannan suka wuce, da yake duk ba su da nisa, gabad'aya a cikin Nasarawa G.R.A suke har ASTV'n. Driver na parking Neehal ta fito, ganin Motar Dad a gurin alamun ya dawo ta ji daÉ—i a ranta, dama yau gabad'aya ta yi missing É—insa. Part d'in Mama ta nufa, ta shiga falon bakinta É—auke da sallama, gabantane ya faÉ—i ganin Ameen zaune shi kaÉ—ai a falon ya na latsa waya..........âœï¸
[7/21, 8:59 AM] Zee data: *⚡NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*0ï¸âƒ£3ï¸âƒ£*
.Lumshe idanunta ta yi tana shaƙar daddaɗan kamshinsa da ya mamaye falon, numfashi ta sauke ta buɗe idanunta a hankali cikin ƙoƙarin daidaita nutsuwarta ta cigaba da tafiya kanta a ƙasa, sallama ta yi masa cikin siririyar muryarta tana kyab'e fuska ita a dole fushi take da shi, ba tare da ya d'ago ba ya amsa mata sallamar a can ƙasan mak'oshi, har ta ɗan wuce shi za ta haura saman steps ya kirata ta hanyar faɗin "Miemah!" Tsayawa ta yi tare da juyowa amma ba ta ƙaraso inda yake ba, kamar ba shi ya kira ta ba ya wani waske abunsa yana ta aikin latsa wayarsa, sanin halinsa ya sa ta ƙaraso inda yake ta zauna a ƙasan kujerar da yake ta ce "Ga ni Yayah" Be kulata ba, kusan 2 minutes kamar ya manta da ita a gurin, sai kuma ya d'ago ya mata wani kallo, cikin daddaɗar muryarsa mai daɗin sauraro ya ce "Sau nawa zan hanaki bulbula turare a jikinki idan zaki fita?" Turo baki ta yi gaba ta ce "Kaɗan fa na saka" ya ce "Ƙarya na yi miki kenan?" Girgiza kanta ta yi alamar a'a, maida hankalinsa ya yi kan wayarsa, Neehal na son wucewa sama amma ta na tsoro tun da bai bata umarni ba, shikuma ya cigaba da al'amuransa kamar ya manta da ita a gurin, kuma ya na sane umarninsa take jira, ɗayar wayarsa da ke ajiye a kusa da shi ce ta yi ƙara alamun shigowar kira, dubawa ya yi, ganin sunan Dad na yawo akan wayar ya sa shi d'agawa da sauri. Dad ya ce "Muhammad ka dawo daga masallacin ne?" Ameen ya ce "Eh" Dad ya ce "Daughter din ta dawo ne" ya ce "Eh" Dad ya ce "Ok, ina son ganinka yanzu a part ɗina" Ameen ya ce "Ganinan zuwa yanzu" ya katse wayar tare da miƙewa ya nufi part d'in Daddy wanda akwai ƙofar da za ta sadaka da part d'in Daddy'n ta cikin falon Mama. Neehal ta mik'e da sauri kamar wadda ke zaune a kan ƙaya ta haye sama. Ɗakin da Hajiya take ta lek'a, Hajiya dake zaune kan darduma ta na lazimi ta dubi Neehal ta ce "A'a kin dawo ne?" Neehal ta ce "Ba gashi kin ganni ba" Hajiya ta ce "To sannunki da dawowa, ina ja'irar ƙawar taki?" Neehal ta ce "Ta wuce gida, Mama ba ta dawo ba?" Hajiya ta ce "Sai bayan magriba fa ta tafi, na yi_na yi ta haƙura da zuwa asibitinnan ta huta itama amma ta ƙi, kamar wadda aka yi wa wahayi haka ta tafi a darennan, dan ma aikin Allah za ta yi, tun da duba marasa lafiya ne" Neehal ba ta ce Komai ba ta juya ta fice ta nufi ɗakinta. Tana ajiye jakarta ta fito ta nufi kitchen, cake ta ɗauko da meatpie saboda wata irin yunwa ta take ji, ɗakinta ta koma bayan ta ɗau drink a falo, sai da ta ci ta yi k'at, sannan ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala dan yin sallar isha'i.
Tun da Ameen ya shigo Dad yake binsa da kallo cikin mamakin irin ramar da ya yi, duk da Mama ta masa bayani a waya amma bai yi zaton abun ya kai haka ba, Ameen ya zauna a ƙasan kujerar da Abba yake tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Dad ya nisa ya ce "Muhammad cuta ka yi a can barrak ɗinne ba mu sani ba?" Ameen ya ce "A'a Daddy" Dad ya ce "To wannan ramar fa ta menene?" Shafa lallausar sumar kansa ya yi tare da lasar lips d'insa na ƙasa, cikin girmamawa ya ce "Dad yanayin aiki ne kawai" Dad yay shiru ya na kallonsa ba tare da yarda da abin da ya ce ɗin ba, sanin halinsa koda zai kwana yana tambayarsa ba faɗa masa abin da ke damunsa zai yi sai ya kyale shi kawai, amma tabbas ya san akwai abin da ke damun ɗan nasa. Sauke numfashi Dad ya yi ya ce "Shikenan Captain, Allah ya taimaka ya ba da sa'a" Ameen ya amsa da "Amin" Dad ya gyara zama ya ce "Ɗazu kafin na fita mun yi magana da Doctor akan shirye_shiryen bikin Daughter, tunda bikin ya matso, ya kamata mu san abin yi mu fara shiri" Ameen ya ce "Hakane, Allah ya kai mu Lokacin da rai da lafiya, ya kuma sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya" Dad ya ce "Amin ya Allah, ta mun Magana kuma a kanka kaima, ya kamata a ce zuwa yanzun kaima ka fitar da matar Aure, dan mu da son samu ne ma a haɗa bikinka da na Daughter" Ameen ya d'ago kansa da sauri ya na duban mahaifinnasa amma bai ce komai ba, Dad ya ce "Kayi shiru Captain" Ameen ya sauke Numfashi ya ce "Dad a dan ƙara mini time, zuwa bayan bikinnata insha Allahu zan fitar da mata nima" Dad ya ce "To shikenan, Allah ya kai mu da rai da lafiya, ya kuma haɗa ku da abokan zama na gari, Allah ya muku Albarka" Ameen ya ce "Amin ya Allah" Wata hirar suka shiga daban akan aikinsu na sojoji.
Neehal tun tana sallah take jin wayarta na ringing, sai da ta idar ta yi shafa'i da wutri sannan ta É—akko wayoyin nata dake cikin jakarta.