← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 118

Sashe 46

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Uncle please zan sha ruwa." Kallonta ya yi fuska a sake ya ce "Oh sorry Dear take it." Neehal ta karb'i ruwan da yake miƙa mata tare da faɗin "Thank you." Murmushinsa Mai kyau ya mata, Neehal ta buɗe robar ruwan da sauri har tana yar da kuɗin kayan miyan bata sani ba, kai robar ta yi bakinta zata sha ruwan ya katse ta da sauri ta hanyar faɗin. "No, go there ki zauna sai ki sha." Ya ƙarashe maganar tare da nuna mata wani dakali dake kofar gidansu. Da sauri Neehal ta ƙarasa ta zauna ta fara quqqutar ruwan, sai da ta shanye tass sannan ta yarda robar. Matashin yana tsaye yana kallonta, haka kawai ya ji ya kasa tafiya, Neehal ta dafe cikinta saboda k'ullewar da ya fara mata saboda yunwar da take ji. Cike da tausayawa Matashin ya sunkuya ya ɗauki kuɗin da ta yar a ƙasa ya ƙarasa inda take, cikin tausayinta da ya d'arsar masa a zuciya lokaci ɗaya ya ce "Are you Ok?" Neehal ta girgiza masa kai ta ce "I'm felling hungry." Ya ce "Okay, sorry, ki jira ni anan, zan dawo yanzu." Neehal ta gyaɗa masa kai tana ƙara dafe cikinta. Cikin 5 minutes ya shiga gidansu ya fito hannunsa ɗauke da Cake wanda aka yi rapping ɗinsa, sai kuma lemon jarka guda ɗaya. Miƙa mata ya yi ta karb'a da sauri tare da kallonsa, a hankali ta ce "Thank you so much." Sannan ta fara cin Cake ɗin, ƙura mata ido ya yi ganin yanda take cin cake ɗin cikin nutsuwa tana lumshe ido, ita kuwa Neehal daɗi Cake ɗin ya mata ba kaɗan ba. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta ɗauki leman ta sha fiye da rabin jakar, ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce "Alhamdulillah." Sai kuma ta miƙe zumbur kamar wadda aka tsikara ta fara ƙoƙarin tafiya, katse ta ya yi ta hanyar faɗin "Zo ki ɗauki sauran mana." Neehal ta ce "Na k'oshi ne." Ya ce "Are you sure?" Ta gyaɗa masa kai, ya ce "To ki tafi da shi gida anjima sai ki ci." Neehal ta waro ido waje ta ce "Aunty zata dake ni idan na je da shi gida." Miƙa mata kuɗin data yar ya yi ya ce "Kin manta." Neehal ta karb'a da sauri ta wuce. Cake ɗin data bari da lemo ya ɗauka ya shige Motarsa, yana fita titi ya hango ta a gurin mai kayan miya, an yi sa'a ita ma ta juyo suka haɗa ido, d'aga mata hannu ya yi yana murmushi itama ta mayar masa da murmushin tare da d'aga masa hannun, a gurin ya samu almajiri ya bashi ragowar Cake ɗin da lemon. Cikin sauri Neehal ta siyi kayan miyan ta koma gida, zuciyarta cike da tsoron Aunty Fauziyya, wani ɓangaren na zuciyarta ta kuwa farinciki take yau ta ci Cake ta sha lemo. Da masifa Aunty Fauziyya ta tare ta, ita dai tay shiru kawai tana kallonta tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Aunty Fauziyya cikin bala'inta ta ce "Shegiyar yarinya mai kama da aljanu, ana miki magana ki tsare mutum da wasu idanunki kamar na mage." Ta kamo kunnen Neehal ta murd'e da ƙarfi tana faɗin, "Gobe ma in ƙara aiken ki ki kuma zuwa ki zauna." Neehal ta saka kuka saboda zafin da ta ji a kunnenta, Aunty Fauziyya ta dungurar da ita a wurin tare da daka mata tsawar ta rufe mata baki. Kayan miyan ta wanke ta bata ta kai markad'e, ko tunanin bata abinci bata yi ba gashi har la'asar ta yi. Cikin mintuna ƙalilan Neehal ta dawo daga kai markad'en da yake anan mak'otansu ake babu nisa. Sai a sannan Aunty Fauziyya ta bata abinci a wani ɗan kwano, jallop ɗin shinkafa ce da cavage ce akai. Neehal ta kai abincin ɗaki ta ajiye a bayan kayanta, dan a koshe take. Aunty Fauziyya bata barta ta huta ba, sai da ta bata wankin uniform ɗin su Aiman, Neehal ta jijjik'a ta shanya dan ba wani iya wanki ta yi ba, sai dai tai ta goggoga sabulu ajikin kaya in ta ga ya yi kumfa sai ta d'auraye ta shanya. Bayan isha'i tana zaune a ɗaki tana yi wa su Aiman Homework, dan Yaran babu abun da suka iya sai dambe da zagi, ashar kala_kala sun iya narkawa kamar ƴaƴan maguzawa. Tun da Neehal ta zo gidan ita take musu Homework da Assignment ɗin islamiyya. Jin Uncle Umar ya shigo ta miƙe ta shiga falon ta gaishe shi, Allah ya so Aunty Fauziyya tana ɗakinta da sai ta k'ulla mata wani sharrin a gurinsa. Bayan ya amsa ta ce "Uncle Ina son na koma School da Islamiyya." Uncle Umar ya ɗan bata rai ya ce "To je ki sai na duba." Neehal ta tashi ta koma ɗaki ta cigaba da abun da take. Aunty Fauziyya ta fito daga ɗakinta tana yamutsa fuska ta ce "Me na ji yarinyar can tana ce maka ne?" Uncle Umar ya ce "Wai Makaranta take so ta koma." Aunty Fauziyya ta haɗe sosai ta ce "Kai kuma saka ta a makarantar zaka yi?" Ya ce "To ya zan yi, tunda Allah ya ɗora mun." "Ka dai ɗora wa kanka." Aunty Fauziyya ta faɗa tana keɓe fuska. Uncle Umar ya ce "Hmmm, tunanin ma makarantar da zan kaita nake, amma ina ga makarantar su Aiman zan kai ta." "Me? Makarantar su Aiman fa ka ce, dubu ashirin da biyar ɗin zaka biya mata? Tab'! To wallahi ka nemarwa kanka sauƙi, ka nemi Government School ka kaita." Uncle Umar ya ce "Ai na ga babu Government School a kusa ne shi ya sa." Aunty Fauziyya ta ce "Ga ta nan ana ginawa, ka bari idan an gama ginin sai ka kai ta mana." Daga haka suke rufe wannan chapter, suka kama wata. Washegari bayan Neehal ta gama shan akinta kamar kullum aka aike ta siyan kayan miya, yau ma ba ta ci abinci ba ta tafi, gashi abun da bata ci ma Aunty Fauziyya ta yi wato tuwo, tuwon ma miyar kuka.

Ta zo dai_dai layin da suka haɗu da mutumin jiya wanda ta rad'a masa suna *Uncle mai kirki* , har ta wuce gidan ta dawo ta tsaya a ƙofar gidan tana kallon gidan, a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar ta fara knocking, 2 minutes tana tsaye sannan aka buɗe ƙofar. Faɗaɗa fara'a ta yi sosai kamar yadda shi ma yake fara'ar cike da mamakin ganin ta, yana sanye cikin ƙananan kaya wanda suka masa kyau sosai, sai tashin daddad'an k'amshinsa yake. Neehal ta ce "Ina yini." Yana murmushi ya ce "Lafiya k'alau." Juya wa ya yi ya ce "Come in." Neehal ta tsaya ba tare data bishi ba, ya juyo ya ce "Ya kika tsaya? Ki shigo mana." Neehal ta girgiza masa kai alamun a'a, ya ce "Why?" Ta ce "Ina jin tsoro." Da ƙyar ya lallaɓa ta ta shiga gidan, a BQ yake har ciki ta shiga ta zauna a falo a d'arare, haɗadd'iyar pride rice ya kawo mata a plate da bottle water da juice, da murna Neehal ta karb'a ta fara ci. Zama ya yi yana kallonta cikin tausayinta. Sai da ta ci ta yi ƙat sannan ta ce "Uncle ina Mamanka?" Ya ce "Tana cikin gida." Ta ce "Nan part ɗinka ne?" Ya ce "Ehh." Shiru ta yi tana ƙarewa falon kallo, cikin kulawa ya ce "What is your name?" Neehal ta ce "Neehal." Ya ce "Wow Nice name, real name ɗinki fa?" Ta ce "Fateemah." Ya ce "Wow! My mother's name." Neehal ta ce "And you?" Ya yi murmushi ya ce "Ahmad." gyaɗa kai ta yi tare da tashi da sauri ta ce "Zan tafi Uncle, zan siyo wa Aunty kayan miya, idan na daɗe zata zane Ni." Ya ce "To Princess, gobe ma zaki zo ko?" Neehal ta yi shiru can kuma ta ce "Ehh." Har bakin titi ya raka ta sannan ya dawo gida. Yau ma data koma gida sai da ta sha bala'in Aunty Fauziyya. Tun daga wannan ranar kullum sai aka aike ta sai ta biya gidansu AHMAD, ya bata lafiyayyen abinci ta ci da drinks, wataran kuma ice cream da snacks yake bata, choculate da sweet kam kullum sai tasha su ta more, idan ta koma gida kuma Aunty Fauziyya tay ta mata masifa, wataran har da duka akan dad'ewar da take, amma ko sau ɗaya bata taɓa tambayarta inda take zuwa ba. Idan ta bawa Neehal abinci sai ta k'ulle a leda ta faki idon Aunty Fauziyya ta fita ta bawa almajiri, tunda yanzu kullum a k'oshe take wuni, abincin dare ma kullum sai ta rage kaɗan take ci. Breakfast kawai take yi full a gidan. A hankali shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Ahmad, kullum ta zo yana mata tambayoyi a game da rayuwarta, a haka ya gane marainiya ce kuma bata haɗu da uwar riƙo ta gari ba, hakan ya ƙara masa tausayinta a zuciyarsa sosai, kullum yana mata ƙarin haddarta na Alqur'ani tunda Uncle Umar ya ƙi saka ta a Islamiyya da School, haka karatun boko kullum yana mata lesson, sai ta yi fiye da awa biyu a gidansu, ta koma gida kuma ta ci duka, amma duk da haka gobe sai ta kara zuwa.
Chapter 46 · 0% Book details