Sashe 74
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Da sauri ta d'ago ta kalle shi gabanta na fad'uwa ta ce "Doctor! wa...." Ya katse ta da faÉ—in "Kin yi mamaki ba, na san yanzu kina tambayar kanki ina na samo waÉ—annan hotunan, kuma yaushe aka yi su?" Ya É—an ja numfashi ya ce "Neehal! Na yi mamaki sosai da kika kasa gane ni a lokacin da kika ganni, duk da nasan shekarun da yawa kuma lokacin da muka haÉ—u kina yarinya Æ™arama, amma na san yanzu waÉ—annan pictures É—in sun tuna miki da ni a rayuwarki." Kallon fuskarsa ta shiga yi ko kiftawa ba ta yi, lokacin É—aya idanunta suka ciko da k'walla, ta yi minti uku a tana kallonsa kallo irin na k'urilla sannan ta ce. "Uncle Ahmad! Are you the one please?" Ta faÉ—a cikin raunin murya da tsantsar mamaki. Ya yi murmushi cikin jin daÉ—in yanda ta iya tuno shi da wuri haka ya ce "Yes, kin manta ni a rayuwarki ko? kin karya alÆ™awarin da kika mun." Ta girgiza masa kai cikin Æ™oÆ™arin mai da k'wallar data tarar mata ta ce "Ban manta ka ba a cikin raina, domin a duk lokacin da zan tuno da rayuwata ta gidan Uncle Umar sai na tuna da kai da irin taimakon da ka ba ni." Ya ce "Amma me yasa da kika ganni kika kasa gane ni." Ta ce "I don't know, amma kasan shekarun da yawa, kuma ranar dana ganka na ga kamar na san fuskarsa, amma na rasa a ina na santa." Ahmad ya juyo ya fuskance sosai ya ce "Neehal, duk tsawon shekarun nan da suke wuce dai_dai da rana É—aya ban taÉ“a mantaki ba a cikin raina, kodayaushe ina tunanin ki tare da fatan na sake haÉ—uwa dake a rayuwata, ashe ta sanadin twins Ubangiji zai Æ™ara haÉ—u mu, haÉ—uwar da bana fatan mu rabu har abada." Neehal ta sauke numfashi ta ce "Ina Mamy?" Cikin mamaki ya ce "Baki manta Mamy ba?" Ta ce "Eh mana, kamar yadda ban manta ka ba itama ban manta ta ba, amma na san idan na ganta a yanzu ba zan gane ta ba, har yanzu tana unguwar su Uncle Umar?" Ya ce "A'a sun tashi daga unguwar, amma suna Kanon dai. Sai dai ita tafi shekara bata Æ™asar nan, ta je Turkey, shekaran jiya ta dawo, yanzu ma daga gidanta nake." Ya É—an É“ata fuska sannan ya cigaba da magana "Ni fa ban ga kina murnar gani ba, ko ba ki yi farinciki da sake haÉ—a mu da Allah ya yi ba?" Neehal ta yi murmushi ta ce "Hmm, wlh Uncle farincikin da yake cikin Zuciyata a yanzu na haÉ—uwa da kai a karo biyu a rayuwata ba zai misaltu ba, kawai tsananin mamaki ne ya hana murnar tawa bayyana, gani nake ma kamar mafarki nake, Uncle Ahmad, mutumin kirki, mai taimakon bayin Allah ba tare da ya san su ba, shine mahaifin Twins É—ina? Abun kamar almala Uncle." Ahmad ya yi murmushi yana jin zuciyarsa ta masa wasai ya ce "Ikon Allah ya fi Æ™arfin komai Princess." Ta yi shiru kawai tana kallon sa, ta kasa É—auke idanunta daga kansa. Ya d'age mata gira É—aya ya ce "Wannan kallon fa?" Da sauri ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi, wani irin farinciki take ji a cikin ranta, kamar ta tashi tai ta tik'ar rawa haka take ji. Ya yi Æ™asa da murya ya ce "Ya zaki rufe mun maganin ciwon idona? Please ki buÉ—en wannan kyakkyawar fuskar da idanuna ba sa gajiya da kallon ta" Ta buÉ—e fuskar amma sai ta yi Æ™asa da kanta, wata irin kunyarsa take ji ba kaÉ—an ba. Ahmad da yake jin kamar ya rungume ta saboda wutar k'aunarta da take Æ™ara ruruwa a ransa ya ce "Now tell me, me ya faru bayan rabuwar mu." Ba tare data d'ago ba ta ce "Ka fara faÉ—a mun naka, da yanda har ka yi aure ka....." Sai kuma ta yi shiru. Ya ce "Uhm, Æ™arasa faÉ—ar abun da zaki ce mana." Ta É—an turo baki ta ce "Babu." Ya gyara zama tare da faÉ—in. "Ranar da muka haÉ—u dake last, bayan na koma gida na kasa aiwatar da komai saboda tunanin ki, na farko ina tunanin kar a miki wani abu a gida saboda Uncle É—inki ya ganmu tare. Na biyu kuma wanda shi ya fi sani cikin damuwa komawa Abuja da zan yi in yi nesa dake. Tun kafin ranar nake wannan tunanin, da farko na É—auka tausayin ki ne yasa nake wannan tunanin, amma daga baya na gane na shak'u dake shak'uwa mai tsanani. A ranar ko baccin kirki ban iya yi ba saboda tunani. Da safe bayan na gama shiryawa kafin na fita sai da na je wajen gidanku ko Allah zai sa in ganki, amma ko me kama dake ban gani ba. Gashi ni ban san gidanku ba tunda bana Æ™arasawa a hanya muke rabuwa. Haka na dawo gida jiki a sanyaye, gashi washegarin ranar ne tafiyata Abuja. Tun da na je Masallaci na yi sallar Azhar har aka kira la'asar ban koma gida ba, ina Æ™ofar gida ina jiran ki, ki zo wucewa, ranar ko abincin kirki ban iya ci ba. Bayan na yi Sallar la'asar na je gurin mai kayan miyan da kike siya a gurinsa na masa kwatancenki na tambaye shi ko kin zo siyan kayan miyan ranar ya ce mun A'a baki zo ba. Hankalina fa ya tashi matuÆ™a na Æ™ara komawa layinku ko zan gan ki, na tambayi wasu yara ko sun san gidanku suka ce mun bama su san ki ba. Ranar dai haka na kwana cikin tsananin damuwa. Washegari tun safe na wuce Abuja zuciyata babu daÉ—i ko kaÉ—an. Wata na uku da komawa Abuja na tafi India na yi wani course na shekara É—aya, bayan na dawo da some weeks na fara aiki. A'isha Æ´ar gidan wani abokin Daddy ce, na santa sosai suna zuwa gidanmu tun kafin mu fara soyayya da Ita. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa, shine abun ma da ya ja hankalina a game da Ita. Mun kai 3 years muna soyayya kafin mu yi aure, dan sai da na jira ta Æ™arasa karatunta na degree. Na ji daÉ—in zaman aure da A'isha sosai, saboda macece mai haquri da biyayya ga ilimin addini, ta bani kulawa da kowanne É—a Namiji yake fatan samu a gurin Matarsa ta sunna. A'isha ta san labarinki tass a gurina, saboda yawan zancen ki da nake mata, a duk lokacin da na mata zancenki sai ta ce mun ita dai tana son ta ga Neehal É—in nan, Allah ya nuna mata ke kafin ta mutu. Ashe baza ku taÉ“a haÉ—uwa domin a haihuwar twins Allah ya mata rasuwa. Mutuwar A'isha ta dake ni ba kaÉ—an ba, sanadiyyar mutuwar ta hawan jini ya kama ni saboda damuwar da na saka a raina da yawan tunani. Idan na kalli twins ne kawai nake jin sanyi a raina. Afrah suna biyu ta ci a gurina, da sunan Ummi da sunanki, Amrah kuma A'isha na yiwa takwara. A hankali radadin mutuwar A'isha ya fara raguwa a zuciyata, sai dai up to now ban Æ™ara kallon wata mace da sunan soyayya ba balle na yi tunanin Æ™ara aure, shekara biyar kenan da rasuwar A'isha. Yarana sune farincikina, su suke É—ebe mun kewar Mahaifiyarsu, kuma tun suna jarirai ni na riÆ™e su, Ummi ta so É—aukar su ita da Ammi na ce bazan iya yin nesa da Æ´aÆ´ana ba su yi haquri zan riÆ™e su a gurina. Aka samo mun wata dattijuwa (Baaba Talatu) ita take taya ni kula da su, tun suna jarirai har time É—in da aka sace su." Ya sauke numfashi tare da kallon Neehal cikin ido ya ce "Duk waÉ—annan abubuwan da suka faru, kamanninki da tunaninki suna manne a zuciyar *Ahmad Aliyu Bulama*. Lokaci zuwa lokaci ina kallon pics É—inki wanda na adana su a Email É—ina. Ni ba ma'abocin kallon TV ba ne, dan tun ina Æ™arami na kallo ba ya gabana, shi yasa ban san ki ba. Na yi mamaki sosai da Aunty Mardiyya da Zahra suka ce mun shahararriyar Æ´ar jarida ce ke domin ban taÉ“a sani ba. Dan da nasani kafin yanzu da tuni na binciko inda kike na zo mun haÉ—u. Tun Ranar da na bar Kano ban Æ™ara zuwan ta ba sai last zuwan da mukai dalilin su Afrah. Ina sauka a cikin garin Kano ke kika fara faÉ—o mun a cikin raina, amma ko kaÉ—an ban yi tunanin ganinki a nan kusa ba, duk tunani ma zuwa yanzu kin yi aure. Lokacin da na yi 2 eyes dake yanayin dana tsinci kaina a ciki na shock É—in ganin ki ba zai misaltu ba, na kasa banbance tsakanin bayyanar su Afrah da ganin ki da nayi a bazata wanne ya fi sakani farinciki, sai dai rashin gane ni da baki yi ba shi ya kashe mun gwiwa, kuma a ranar ba mu da ishashshen time É—in zan miki bayanin da zaki iya tunawa da ni. Tunda muka koma gida tunanin ki ya hanani sakat, so nake kawai na Æ™ara saka ki a cikin idona, amma saboda yanda mutane suke zuwa mun murnar ganin su Afrah ya sa ban samu dama na zo ganin ki ba sai yau." Ya yi shiru yana sauke numfashi. Neehal ta d'ago da kanta wanda yake Æ™asa tunda ya fara bata labarin, cikin sanyin jiki ta ce "Allah ya ji k'an Aunty A'isha ya gafarta mata." Ahmad ya ce "Amin ya Allah." Suka yi shiru na wasu mintuna kowa da tunanin da yake a cikin ransa. Ahmad ne ya katse shirun da faÉ—in "A zak'e nake in ji labarin abun da ya faru da ke bayan rabuwar mu, gashi kuma na ga magriba ta gabato." Neehal ta ce "Next time idan muka haÉ—u sai na baka labarin, dan yana da tsayi." Ya ce "Gobe zan wuce Abuja, amma kafin na tafi zan biyo ta nan In sha Allah." Neehal ta ce "Allah ya kai mu." Ya ce "Amin." Ta ce "Bari na zuba maka abinci, tun d'azu muna ta hira baka ci ba." Ya ce "No, kar ki zuba a Æ™oshe nake." Ta shagwab'e fuska tare da turo baki gaba. Ya yi murmushi ya ce "Kin san me?" Ta girgiza masa kai ita a dole fushi take da shi, tun da ba zai ci abinci ba. Ya ce "Kin Æ™ara kyau sosai da zaÆ™in murya, sai dai shagwab'arki mai kyau tun ta yarinta tana nan har yanzu, tun last zuwan da muka yi na lura da hakan, sai nake tuno da, idan na zaunar dake a gidan Mamy, sai ki shagwab'e mun ki ce, Uncle please zan tafi gida, idan na daÉ—e Aunty zata dake ni." Ta rufe fuska tana murmushin da ya kufce mata ba tare da ta shirya masa ba saboda yanda ya yi maganar yana kwaikwayon muryarta. Shima Æ´ar dariya ya yi wadda ta Æ™ara fito da zallar kyawunsa. Wani irin nishad'i yake ji yau a cikin zuciyarsa, wanda rabon da ya ji irinsa tun kafin rasuwar A'isha. Neehal ita ce first love É—insa a duniya, a kanta ya fara sanin menene so. Wayarta dake gefenta ce ta shiga vibrate, ta duba ta ga Sadik ne yake kirancta. Ta É—an saci kallon Ahmad ta ga ita yake kallo, sai ta ji baza ta iya d'aga wayar a gaban sa, ta Æ™i yin picking. Tana katsewa wani kiran ya Æ™ara shigowa, shima har ya katse bata d'aga ba. Ahmad ya ce "Ba kiran ki ake ba, ki d'aga mana." Zata yi magana ta ji shigowar sak'o cikin wayar, É—auka ta yi ta cire key ta duba, ganin Sadik ne ta shiga karantawa a zuciyarta. _Where Are you sweetheart inata kiran ki baki É—auka ba, gani kuma a cikin gida na zo na ganki._ 'Ya Sadik kuma da sakaliyar yammar nan?' ta faÉ—i haka a cikin ranta. Reply ta masa da faÉ—in _Ina abu ne, na zo zan yi picking kafin na É—auka ta katse, Okay ka Æ™araso ciki mana._ Ta ajiye wayar tare da d'agowa ta kalli Ahmad wanda ya Æ™ura mata ido. Ta shagwab'e fuska ta ce "Ni fa kallon nan naka yana sa in ji wani abu a jikina, Please ka daina." Ya ce "Idan kina kusa da ni ba zan taÉ“a iya daina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki ba Princess." Ta yi Æ™asa da kanta ba ta ce komai ba. Ya É—auki wayarsa dake kan cinyarta ya shiga Camera ya fara É—aukarta a hoto ba tare data sani ba. Ta d'ago zata yi magana ya katse ta sauri da faÉ—in, "Please Princess ko É—aya ne." Ta yi murmushi saboda yanda ya wani marairaice fuska. Ya ce "Yawwa, Wow da murmushin ya fi kyau." Ya Æ™arashe maganar tare da É—aukarta hoton tana murmushin. Dai_dai nan Ameen ya buÉ—o Æ™ofar falon ya shigo...........âœï¸
[7/21, 9:31 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
[7/21, 9:31 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*