← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 118

Sashe 111

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washegari kamar yadda Dad ya ce, Sadik ya zo gidan da yamma. Har part ɗin Daddy'n akai masa iso ya je ya same shi. Daddy yay masa ƴan tambayoyi, sannan ya ce ya bashi auran Neehal ya turo magabatansa. Ai Sadik ji ya yi kamar ya rungume Daddy dan tsananin farin ciki, yay ta zuba masa godiya. Ranar Neehal ta sha kalamai da soyayya a gurin shi kala_kala, ita kuwa tay ta masa dariya tana tunanin ranar da aka ɗaura musu aure kuma sai ya kusa mutuwa dan farinciki. Bayan sati ɗaya mahaifinsa da abokinsa da Yayan Maamah suka zo nema masa auren Neehal, tare da kuɗin na gani ina so. Daddy da Kawu Musa da Uncle Mahmud, da mijin Aunty A'isha, su suka karb'i kuɗin, aka saka ranar biki bayan ƙaramar Sallah da yardar Allah, lokacin Neehal sun yi graduation ba jimawa. Su Sadik baki ya ƙi rufuwa, saboda farincikin nan da watanni biyar zuwa shida zai angonce da masoyiyarsa. A ɓangaren Ahmad kuwa a washegarin ranar da ya zo ya koma Abuja, yana zuwa ya sanar da su Ummi abun da yake faruwa. Sun ji ba daɗi sosai har Abban su Ahmad, amma suka ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Ahmad ya bawa zuciyarsa haquri, bai bari damuwa ta masa illa ba, duk da ko d'igo babu abun da ya ragu na son Neehal a cikin zuciyarsa. Daga ya ji abun zai dame sa sai ya dinga maimaita kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un da hasbunallahu'wani'imal'wakil, ga zuciyarsa kullum cikin ƙarfafa masa gwiwar Neehal tasa ce take, kar ya fidda rai da samun ta. Kuma babu abun da ya canza wa Neehal daga yanda suke before, idan ya kira wa su Afrah ita a waya, ta ce su ba shi wayar yana karɓa su yi magana har da ƴar tsokana wani lokacin, sai dai ba ya mata zancen soyayya ko kaɗan, zumunci kawai suke yi. Itama Neehal ɗin ta yi ƙoƙari ta cire damuwar rabuwa da shi daga ranta. Ta yarda cewa Allah ya yi Sadik ne mijinta tun fil azal, ba Jameel, Anwar da Ahmad ba, tunda su sun rasu, Ahmad kuma shi yasa Allah ya raba su tun a farko, dan da a ce ba su rabu da shi ba a lokacin da take gidan Aunty Fauziyya, da ko soyayya ba za ta yi da Jameel da Anwar ba, tunda ga shi kuma tun lokacin yake son ta. Ta kwantar da hankalinta suna shan soyayyar su da Sadik. Sai dai tunda aka tsayar da lokacin bikin su take jin wani irin feeling a cikin zuciyarta, feeling ɗin da ta kasa tantance ko na mene ne, sai dai yana mata yanayin kamar tsoro ko fargaba, amma kuma tsoron da fargabar na mene? Sai kuma wani abu guda ɗaya, ɗan sakin fuskar da ta fara samu daga gurin Ameen da kulawa ya daina yi mata yanzu, sai ta gaishe shi ma ya ƙi amsawa, ita kuma hakan na damun ta matuƙa, ba ta son ta ga yana yi mata irin wannan shariyar, sai ta ji duk ranta babu daɗi........✍️
[8/7, 9:21 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*5️⃣9️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*

Haka rayuwa tay ta tafiya, bikin Neehal na ƙara kusantowa. Ɓangarorin biyu na amarya dana ango suna ta shirye-shiryen bikin, duk da dangin Angon ba kowa ke son auren ba. Sai dai kamar yadda Uncle Mahmud ya roƙi alfarma tun ranar da aka kawo kuɗin Auren, akan a ɓoye batun auren sai abun ya matso daf sannan a bayyana saboda tsaro, a cewar sa idan ma wani ne yake kashe samarin da Neehal zata aura kamar yadda ake hasashe, to lokacin da zancen bikin zai fito kafin ya gama duk wani shirinsa an yi bikin an gama Insha Allah. Hakan ce ta kasance kuwa domin ba kowa ya san da maganar bikin ba, sai na jiki_jiki wanda ya zama dole. Ita Mama kam ta ce babu wani shagali da za'ai da bikin, ɗaurin Aure kawai za'ayi a kai amarya gidan ta. Sai dai fa shi Ango Sadik da bai san da shirin Mama ba yana ta shirye-shiryen haɗa gagarumar dinner shi da abokanansa. Haneefah ma ta ce baza su yi biki lami ba, sai sun cashe ko da na rana ɗaya ne, tana nan tana ta yiwa Mama naci da magiya akan ta amince. Ita kam Neehal tsarin Maman ya mata dai-dai, dan ita ba gwanar son harkar taro ba ce dama. A wannan azumin na bana Neehal suka ziyarci ƙasa mai tsarki ita da Mama, Mama ta cika alƙawarin data ɗaukar mata tun last year. Sun je sun yi Umrah, satin su biyu a can suka dawo. Bayan Sallah da sati ɗaya suka fara final exam ɗinsu. Neehal ta maida hankalinta sosai akan karatu, ta watsar da duk wani feeling da take ji a cikin ranta ta duk'ufa ga karatu, domin tana son yanda ta fara karatun ta successfully ta gama successfully. A gefe guda kuma zuciyarta cike take da murnar kammala karatunta da zata yi this year.
Chapter 111 · 0% Book details