← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 118

Sashe 24

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan ta shirya suka sauko ƙasa inda suka tarar da Mama,Hajiya,Ammi,Aunty Sadiya da Aunty A'isha sun baje kayan lefen a falon suna kalla, Ammin su Ameerah sai yaba kayan take ta na faɗin "Masha Allah kaya sun yi sosai". Neehal ta ƙarasa ta rungume Hajiya cikin murnar ganinta ta ce "Hajiyata Oyoyo na yi missing ɗinki." Hajiya ta ce "Kamar da gaske, ina ja'irar k'awarki.?" Neehal ta ce "Daɗina dake ba'a miki gwaninta sai ki gwale mutum." Hajiya ta ce "Na ji ɗin." Neehal ta sake ta, ta ƙarasa kusa da Amminsu Ameerah ta rungume ta tare da gaishe ta, Ammi ta amsa mata cikin fara'a da kulawa. Gaishe da su Mama da Aunties ɗinta ta yi. Mama ta dube ta, ta ce "Ki je ki haɗa breakfast ki kaiwa Yayanki, kema ki haɗa ki ci." Neehal ta ce "Mama bari na ga kayan nan sai na kai masa." Hajiya ta tari numfashinta da faɗin "Kayan da sun kusa sati a gidan nan, mak'ota da ƴan'uwa duk sun zo sun gani amma ke ki na kwana a gidan baki gani ba." Mama ta bata amsa da faɗin "Ba ta wani gani sosai ba saboda ta na exam, kin san Neehal idan ta na exam ba ta da nutsuwa." Aunty Sadiya ta ce "Yanzu dai an gama, sai a bita da addu'a Allah ya ba da sa'a." Suka amsa gabad'aya da "Amin." Bayan ta gama ganin kayan ta mik'e ta shiga kitchen ta haɗawa Ameen breakfast kamar yadda Mama ta bata umarni, tunda Ameen ɗin a gida ya kwana yau. Ta ɗauki kayan ta na duban Ameerah da ta taya ta haɗa kayan ta ce "Mu je ki raka ni na kaiwa Yayan." Ameerah ta riƙe hab'a tare fito da idanunta waje ta ce "Wa? ki je ke kaɗai dai, kin san halin kayanki fa." Neehal ta ce "Kar ki je ɗin, kuma sai na faɗa masa in ce kin ce masa masifaffe." Ameerah ta ce "Allah ya na gani dai." Ammi ta bi Neehal da kallo bayan sun fito harta fice daga falon, Ammi ta sauke Numfashi ta ce "Neehal har yanzu ba ta maida jikinta ba tun ramar da tayi lokacin rasuwar Anwar." Mama ta ce "To bata son cin abinci, ba dole tai ta rama ba."  Ammi ta ce "Duk da rashin cin abincin ma, amma mutuwar na damunta a rai har yanzu." "Ai dole ne ta damu Aunty Bilki, Samari har biyu sai an kusa bikinku duk su mutu."  Cewar Aunty Sadiya cikin jimantawa. Mama ta ce "Wlh nima abun na damuna ina tsoron kar ace sanadin Neehal ake kisan nan." Cikin tarar numfashi Hajiya ta ce "Ashsha, faɗima ba na hanaki wannan zancen ba, yanzu idan wani ya ji ba sai ya samu abun ɗorarwa ba, tunda kema uwarta ki na faɗa, kun san mutane ba sa rasa abun fad'i, yanzu sai a gogawa yarinya baƙin fenti aita jifanta da sharruka kala_kala." Mama ta sauke numfashi ta ce "Shikenan Hajiya In sha Allahu na dena faɗar haka, shima Dad ranar da na faɗa masa haka sai ya hauni da faɗa wai a kan me zance haka, Neehal ɗin me taiwa wani da zai dinga bibiyarta ya na kashe mata samarinta?" Aunty A'isha da ba ta ce komai ba tunda suka fara maganar sai yanzu ta ce. "To mu dai muna ga Allah, kuma shi zai warware mana gaskiyar al'amari, duk ma mai nufin wani da sharri Allah ya mayar masa kansa." Suka amsa gabad'aya da "Amin."

Ameen ya na cikin bedroom ɗinsa ya na shiryawa ya ji a na knocking k'ofar falo, sai da ya ƙarasa shirinsa a tsanake sannan ya fito dan zuwa ya buɗe, zuwa lokacin Neehal ta gaji da tsaiwa ga kaya a hannunta. Ya buɗe k'ofar tare da yin baya dan ba ta damar shigowa, Neehal ta yi sallama sannan ta shiga. "Yaya a ina zan ajiye maka?" Ta tambaye shi bayan ya amsa mata sallamar. Kan carpet d'in dake tsakiyar falon ya nuna mata, ajiyewa ta yi ta na sauke numfashi. Juyowa ta yi Ameen dake kallonta yay saurin ɗauke kansa tare da zama a kan kujera 2 seater. Neehal ta zauna a kusa da shi ta na kallonsa a ranta ta na gulmarsa ganin kamar ƙara kyau yake ya yi wani fresh abinsa, Neehal a ranta  ta ce "Tun kafin a yi auren, wannan ina ga anyi auren." 
"Ina kwana Yaya" ta faɗa cikin nutsuwarta. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Lafiya, Ya exams.?" Neehal ta ce "Mun gama jiya." Ameen ya jinjina kai ya na dubanta ya ce "Allah ya ba da sa'a." ta ce "Ameen." Daga haka suka yi shiru, Neehal ta na son ta tambaye shi abu amma ta kasa saboda sanin halin halinsa, wannan ƴar sakewar da ta samu ya mata yanzu sai ta nemeta ta rasa. Wayarta dake cikin aljihun rigarta ce ta fara vibrate, hannu ta zira ta ɗauko a tunanin Mama ta ce amma sai ta ga Sadik ne. D'agawa ta yi ta na murmushi ta kara a kunnenta. "Wa'alaikassalam Yaya Sadik ɗina." Ta fad'i haka cikin murmushi mai sauti alamun ta na cikin nishad'in kiran da a ka mata. Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Lafiya k'alau and you?" Ameen dake kallonta ya tab'e ɗan ƙaramin bakinsa tare da ɗauke kansa daga kallon nata, da sauri kuma ya juyo amma cikin basarwarshi yanda ba za a gane saurin nashi ba jin ta na magana cikin shagwab'a "Dan Allah da gaske kake Ya Sadik? Kar fa kasa na fito kuma ba ka zo ba." Sosai Ameen yake kallonta, Ƴar dariya ta yi sannan ta mik'e ta na faɗin "Gani nan to." Kallon Ameen ta yi ta ce "Yaya ina zuwa, bari in je in dawo." Ba ta jira amsarshi ba ta fara tafiya. Bin ta da kallo kawai ya yi cikin ransa ya na ƙissima abubuwa da dama, har ta kai bakin k'ofa ya tsayar da ita ta hanyar faɗin...........✍️
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *⚡NEEHAL⚡*

_By_
_Zeey Kumurya_

1️⃣6️⃣

INAYI MUKU ALBISHIR 💃💃💃💃DA SABON LITTAFINA NA KUD'I MAI SUNA(sarauniya SADDIK'A) PAID BOOK NE GA MASU SO SUYI MIN MAGANA NAN DA NEX WEEK 16 October, 2021 Ranar Asabar IDAN ALLAH YAKAIMU 😍😍😍😍😍😍

GAMAI BUKATAR KARANTA LITTAFIN SARAUNIYA SADDIKA
YAMIN MAGANA TA PC GA NUMBER (07089540330 Asmeety) Sai najiku kadda kubari abaku labari 😍😍😍💕💕💕💕💕

(Hot Sexy 🍌, Love❤️,and💞 Romantic 👄 than Funny 🤣)💞

All in this Book (SARAUNIYA💞 SADDIKA)💞

KADDA KUBARI ABAKU LABARI💞 😍 LOVE YOU FAN'S GOOD LUCK💞

BY ASMEETY💞

"Ke!" Neehal ta juyo da sauri jin yanayin da ya yi maganar kamar a zafafe. Ganin yanda ya haɗe fuska tamau ya sa ta shiga cikin nutsuwarta, cikin raunin murya ta ce "Na'am." Ɗauke kansa ya yi kamar ba shi ya kira ta ba, dawowa cikin falon tay ta tsaya a gabansa tare da faɗin "Gani Yaya." Abincin da ta kawo ya nuna mata da hannunsa, cikin rashin fahimtar abun da yake nufi ta ce "Ɗaukewa zan yi na kai dinning?." Wani kallo ya watsa mata, ƙasa tay da kanta da sauri idanunta suka cicciko da k'walla, ta na ƙoƙarin mai da k'wallar ta ji ya ce "Da kike ƙoƙarin fita ki na rawar jiki saboda za ki gurin wani, Ni zan zuba wa kaina abincin.?" Neehal ta ce "Ka yi hak'uri ban san yanzu za ka ci ba." Ta ƙarashe zancen hawaye na zubawa a kan kuncinta, a rayuwar Neehal kwata_kwata ba ta san a mata faɗa ko tsawa, shi kuma Yayan nata ta fuskanci ya na k'aunar hakan. Ta na share hawayen fuskarta ta tsugunna ta haɗa masa tea a ƙaramin cup d'in da ta haɗo da shi, miƙa masa tay ya karb'a tare da faɗin "Thanks." Sauran kayan soye_soyen ta zuba masa a cikin v ta ajiye masa a gefensa ganin ya sakko ƙasa ya fara shan tea d'in. Harta mik'e ya dawo da ita, ya na kallonta fuskarsa a ɗan sake ya ce "Kukan me ki ke.?" Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Hannunsa ya zira a aljihun wandonsa ya ɗakko handkerchief ɗinsa dake tashin daddad'an k'amshinsa ya mik'a mata, ba ta yi musu ba ta karb'a ta share hawayennata. Cikin sanyin murya kamar ba shi ya gama mata magana cikin faɗa yanzu ba, ya ce "Rigimammiya kawai, tashi ki tafi." Neehal ta mik'e zumbur ta na ƙara turo baki gaba, ya bi ta da kallo har ta fice.
Chapter 24 · 0% Book details