← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 118

Sashe 112

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau Friday wadda ta kama sati uku da fara exam ɗinsu, kuma yau ne za su yi final exam. Exam ɗin safe gare su, hakan yasa tun asuba ta fara shirinta. Ta shirya cikin Black skirt ɗin da suka yi anko na ƴan class ɗinsu da farar t_shirt wadda aka yi rubutu a gaban rigar, aka rubuta sunan department ɗinsu da year da suka gama school. Ta zauna ta tsara ɗaurin ɗan_kwali a kanta da wani plan yadi Black. Ta saka ɗan kunne white colour. Ta ɗaura tsadadden agogon hannu mai kyau Black a left hand ɗinta, sannan right kuma ta saka white abun hannu da k'aton zobe mai stone a ɗanyatsanta na tsakiya. Ta kalli kanta a mirror tare da yin murmushi, kallo ɗaya zakai mata kasan tana cikin farinciki a yau. Ta tashi ta ɗauko sabon Black shoe ta zira kyakyawan ƙafuwanta dake sanye cikin socks a ciki. Bayan ta feshe jikinta da sanyayan turarukanta masu daɗin k'amshi ta ɗauko madaidaicin mayafi white colour ta yafa a jikinta, sannan ta ɗauki ƙaramar handbag mai ɗauke da exam card ɗinta da pen da kuɗi da phone's ɗinta a ciki.Ta riƙe jakar a hannun damanta, hannun hagunta kuma leda ta riƙe mai ɗauke da rigar graduation ɗinta a ciki. Ta fito ta nufi part ɗin Daddy domin Mama tana can. A falo ta tarar da su a zaune akan carpet Daddy yana breakfast. Ta ajiye kayan hannunta ta tafi da gudu ta rungume Mama tana murmushi. Mama tana murmushin itama ta shafi gefen fuskarta ta ce. "Congratulatios my Daughter, Allah ya albarkaci karatunki da rayuwarki baki ɗaya." Tana murmushi ta ce "Amin, Thank you so Much Mum." Sannan ta tashi ta koma kusa da Daddy ta zauna ta ce. "Good Morning Dad." Yana murmushi cike da kulawa ya ce. "Morning Daughter, how was your preparation of been a graduate?" Ta ce "Alhamdulillah." Daddy ya ce, "To Masha Allah Daughter, Allah ya bayar da sakamako mai kyau, ya nuna mun ranar da zaki zama professor." Ta ce "Amin My Dad, thank you so much." Ya ce "You are always welcome Dear." Mama ta dube ta, ta ce, "Dafatan kin yi breakfast, ba saurin tafiya school ba." Ta girgiza kai ta ce. I'm full." Daddy ya ce, "A'a Daughter, ba'a yi celebration ciki babu abinci ba, zauna mu ci a nan tare." Ta ce "Toh Daddy na." Ta haɗa tea ta sha tare da bread. Ƙarfe bakwai da mintuna tay wa su Mama sallama ta tafi, su kuma suka bi ta da addu'a tare da fatan samun nasara. Bayan ta ƙarasa school ta tarar da classmates ɗinta cikin irin shigar jikinta, mata da skirt maza da wando. Cikin farinciki Freind's ɗinta suka tarb'e ta, kowacce tana yaba kyawun da ƴar'uwarta ta yi. Ƙarfe takwas da mintuna suka shiga ɗakin jarrabawa, Alhamdulillah exam ɗin ta yi mata sauƙi dan jiya kusan raba dare ta yi tana karatu. After 1 hour waɗan da suka gama suka fara submit na exam sheet, itama submitted ta je ta yi dan already ta gama. Tana fitowa suka rungume juna ita da wasu classmates ɗinta da suka riga ta fita, suna taya juna murna. Ta ɗauko wayarta ta shiga WhatsApp ta yi story da *Alhamdulillah.* Dai-dai nan sak'on text message ya shigo wayarta daga Ameen. Ta buɗe da sauri ta karanta. Murnar graduation yay mata tare da tarin addu'oin nasara a rayuwarta. Ta yi murmushi cikin jin daɗi, a ranta ta ce. "One like no other, My Yaya." Tay masa reply da thank you. Daga nan suka shiga ɗaukar pictures ita da classmates ɗinta, har time ɗin gama exam ɗin ya yi, kowa ya fito daga exam hall, suka sassaka rigunan su na graduation mai ɗauke da sunayen kowa a jikin tasa. Rigar white and black colour ce, sai ta dace da dress ɗin jikinsu. Sun sha hotuna yau kamar ba gobe, Haneefah ta zo mata har yamma suna tare a school, whites t_shirt ɗin jikinsu gaba-ɗaya ta ɓaci da sign out, dan ma ita Neehal bata bari an mata ba sosai ba, k'awayenta mata ne kawai su kay mata. Sai kusan Magriba ta koma gida, ta tarar Mama ta haɗa delicious for Dinner na taya ta murnar graduation. Sai bayan ne Magriba ta kunna datar wayarta dan tun safe da tay posting pics ɗinta bata kuma kunnawa ba, ta tarar da tarin messages daga mutane ana mata congratulations, ciki har da Sadik da Ahmad, sai kuma waɗanda suka ɗora ta a status da pics ɗin da ta yi posted. Ta yiyyi screenshot ta ɗora a story tare da godiya. Sosai take cikin farinciki yau, yau wata rana ce mai girma a rayuwarta, da ba za ta taɓa mantawa da ita ba. Bayan ta yi wanka ta canza kaya tana zaune a falon ƙasa kan dinning table tana cin delicious ɗin da Mama ta haɗa mata Ameen ya shigo falon. Kasancewar tana dinning area hakan yasa bata ga shigowar shi ba. Ya zauna suka gaisa da Mama. Sai da ta miƙe domin ɗauko juice dake ɗan nesa da ita akan table ɗin, sannan ta hango shi. Ta ɗauko juice ta tsiyaya ta sha idanunta na kansa, sannan ta ajiye cup ɗin ta nufo inda suke. A kusa da shi ta zauna duk zuciyarta cike take da tsoron kar ya share ta, amma sai ta ga saɓanin abun da ta yi tsammani. Ya juyo yana kallon ta fuskarsa ɗauke da murmushin da ta manta rabon da yay mata, kafin ta yi magana ya riga ta da faɗin. "Congratulations sis." Ta yi murmushi cikin daɗi ta ce. "Thank you Yayana." Ya gyaɗa mata kai sannan ya ɗauke kansa daga gare ta. Ta gaishe shi ya amsa mata cikin kulawa, sannan ta tashi ta ɗauki wayarta ta tafi upstairs dan amsa kiran da Sadik yake ta zuba mata. Tana shiga ɗakinta wani kiran nasa yana ƙara shigowa. Ta d'aga tare yin sallama. Ya amsa mata tare da faɗin. "Graduate." Ta yi fari da ido tana murmushi ta ce. "Yes Barrister." Ya yi murmushi ya ce. "Congratulation once again Dear." Ta ce "Thank you, Husband to be." Ya ce, "Wow kina fasa mun kai fa, idan kika ce Husband to be ɗin nan." Ta yi ƴar dariyar dake bayyanar da farincikinta ta ce. "To na daina faɗa maka." Ya kwaikwayi muryarta ya ce, "Ai bakinki ne ya iyar faɗar Husband, ina son ki kira ni da sunan." Ta murmusa ta ce, "To Husby, Ya Maamah da Abba?" Ya ce "Suna nan k'alau, suna taya surukar su murnar kammala makarantar ta." Ta ce "To ina godiya sosai." Ya ce "Darling ya kamata mu haɗa wani ɗan special party fa, na taya ki murna." Ta ce, "Hmm Daddy ya so haɗa mun amma Mama ta hana, ta ce ita bata son wannan bidi'a_bidi'an, ka san halin Mama sai ita. Sadik ya yi dariya ya ce. "Mama tamu, Allah ya bar mana ita." Ta ce. "Amin." Suka ci-gaba da hirar su, suna cikin wayar kira ya shigo wayarta, ta duba ta ga Ahmad ne yake kiran ta. Ta cewa Sadik zata ɗan d'aga waya mintuna kaɗan, ya ce babu damuwa. Ta d'aga kiran cikin sauri ganin yana ƙoƙarin katsewa.
Chapter 112 · 0% Book details