Sashe 17
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafin azhar su Neehal sun je gidan Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta tare su da fara'a sosai, bayan sun gaisa ta kawo musu drinks su na zaune a falo Aunty Sadiya ta dubi Neehal ta ce "Ni kuwa Daughter Ina son in miki wata tambaya." Neehal ta maida hankalin ta duka a kan Aunty Sadiya ta ce "Ina jin ki Aunty." Aunty Sadiya ta ce "Ki na da saurayi bayan Anwar ne?" Neehal ta ce "A'a, dan gaskiya ba na kula duk masu nuna suna so na, tun daga lokacin da a ka yi Engagement É—inmu." Aunty Sadiya ta ce "Babu wani wanda yake son ki tun da dad'ewa kafin haÉ—uwar ki da Jameel, kuma har yanzu ya na nuna ya na sonki?" Neehal ta ce "Ban gane ba Aunty?" Aunty Sadiya ta ce "Ina nufin kamar shekaru Biyar da suka wuce, ba ki yi wani saurayi da ya nuna ya na sonki ba, kuma har yanzu bai daina son ki ba.?" Neehal ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Gaskiya ba na jin akwai, idanma da akwai na manta." Aunty Sadiya ta gyad'a kai sannan ta maida dubanta ga Haneefah da take saurararsu ta ce "Ke fa Haneefah ko kin sani?" Haneefah ta ce "Gaskiya samarin Neehal na baya duk sun hak'ura da ita, wasu ma sun yi Aurensu." Aunty Sadiya ta ce "Alright." Neehal ta ce "Amma me yasa ki ka mun wannan tambayar Aunty?" Aunty Sadiya ta ce "Kawai." Daga haka suka shiga wata hirar. Sai bayan la'asar suka bar gidan Aunty Sadiya, wadda cikin hikima take yi wa su Neehal tambayoyi domin samun wani information d'in da zai taimake ta gurin binkicen da take. Kamar yadda Mama ta ce gidan Aunty A'isha suka wuce, nanma sun sha hira da Aunty A'isha sai bayan sallar Magriba suka yi haramar tafiya, shima sai da Mama ta kira su ta ce "Ko kwana za su yi a nan É—in ne?" .Neehal ta na É—aukar hand bag d'inta ta ce "Toh Aunty mun tafi sai gani na biyu." Aunty A'isha ta ce "Yanzu ba za ku jira driver'n ya dawo ya kai ku ba tafiya za ku yi?" Neehal ta ce "Gwara mu tafi Aunty, tunda ba mu sani ba ko ba zai dawo da wuri ba, gashi kin kira wayar shi ta Æ™i shiga balle mu ji in ya na kusa mu jira shi." Aunty A'isha ta ce "Toh Shikenan, ku gaida gida, ku gaida su Hajiya da Yaya Fatimah." Neehal ta ce "Za su ji Insha Allah." Haneefah ta yi wa Aunty A'isha sallama, Aunty A'isha ta ce ta gaida Mamanta sannan suka tafi. Suna fitowa daga gidan Haneefah ta dubi Neehal ta ce "Wai me ya sa ba za ki kira driver'nki ya É—auke mu ba?" Neehal ta ce "Kawai yau Napep nake so mu hau." Haneefah ta ce "Kin shiga uku da tsurfa, ko mai ciki haka ta ganki ta k'yale." Neehal ta ce "Na ji É—in." Suna tafiya suna hirarsu, sun zo dai_dai Æ™arshen layinsu Aunty A'isha za su fita titi wata had'ad'd'iyar Mota ta shigo layin, kamar ance Neehal ta kalli Motar suka haÉ—a ido da ma mallakin motar wanda ya kasance saurayi, kuma a ka yi sa'a ya zuge glass d'in Motar, wata irin fad'uwar gaba Neehal ta ji dalilin haÉ—a ido da suka yi da shi, da sauri ta É—auke kallonta daga gurin Motar bugun zuciyarta na sauyawa...........âœï¸
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇ðŸ½
*500MB* 200
*1GB* 300
*2GB* 600
*3GB* 900
*6GB* 1800
(CHECKING BALANCE * 461*4# )
VALIDITY : 1 MONTH
For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*
Ƙoƙarin b'oye baƙon yanayin da ya riske ta lokaci ɗaya ta yi dan kar Haneefah ta fuskanta. Yanda take ta sauke numfashi a kai_a kai ya sa Haneefah dubanta da mamaki ta ce "Ya dai?" Neehal ta girgiza mata kai. Haneefah ta ce "Mu tsaya a nan mu samu Napep ɗin, tunda kin samu tafiyar ƙasa, gashinan ba'aje ko ina ba kin gaji." Neehal ta ce "Ni na ce miki na gaji?" Haneefah ta ce "Ba ki faɗa ba, amma na ga alama, sai sassauke numfashi ki ke kamar wadda ta yi tseren gudu raguwa kawai." Neehal ta harareta ba ta ce komai ba, suka tsaya domin duba abun hawa. A hankali yake yo baya da Motar tasa cikin tsananin zak'uwa da son ƙara ganin fuskar Neehal, tabbas idan har idanunsa ba gizo suke masa ba, matashiyar 'yar jaridar nan ya gani wadda take matuƙar burge shi tare da abokiyar aikinta. Duk yadda ya so ya wuce ba tare da ya musu magana ba amma ya kasa, duk da tarin gajiyar dake addabar gaɓɓan jikinsa, hakan ya sashi bin shawarar zuciyarsa na bin su domin ya musu magana. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya hango su tsaye a bakin titin, da alamun abun hawa suke jira. Neehal da har lokacin zuciyarta ba ta daina bugawa ba ta ga Mota kamar daga sama ta yi parking a gabansu. Kallon juna suka yi ita da Haneefah da sauri da alamun mamaki. Ba su gama mamakinsu ba suka ji wata daddadar murya mai sanyi daga cikin Motar ta na faɗin "Assalamu alaikum." Haneefah ce ta yi ƙarfin halin amsa wa, Neehal kuwa ƙasa ta yi da kanta gabanta na ci gaba da fad'uwa. "Ina yininku?" Ya gaishe su idanunshi a kan Neehal. Haneefah ta yi ɗan murmushi haka kawai ta ji Matashin ya burgeta, "Lafiya k'alau, amma na ji kunyar amsawa, saboda mu yakamata mu gaishe ka, tunda ka na gaba da mu." Cikin jin daɗin kalaman Haneefah ya ce "Haba k'anwata kar ki ji komai, ai durk'usawa wada ba gajiyayawa ba ne." Haneefah ta ce "Hakane." "Ita k'awar taki ba ta magana ne?" Ya yi maganar idanunsa a kan Neehal. Haneefah ta ce "Hmmm, gajiya ta yi ne daga ɗan......." "Ke! ki zo mu tafi, ki na sane Mama ta ce kar mu yi dare, a hakan ma kin san sai ta yi faɗa." Neehal ta katse Haneefah a ɗan zafafe. Murmushi ya yi har yanzu ya kasa ɗauke idonsa daga kanta, cikin wani irin salo mai narkar da zuciya ya ce "Gaskiya ba na so Mama ta yi muku faɗa, idan babu damuwa ku shigo in kai ku gidan mana." Neehal ta yi sauri ta ce "A'a mun gode." Ta ƙarashe maganar ta na turo baki gaba ganin yanda ya tsareta da ido, duk ya bi ya wani dabaibaye ta." "Please and please, ba danni ba, 'yar k'anwata." Ya fadi maganar cikin marairaicewa. Haneefah ta ce "Ka yi hak'uri, idan ka kai mu gida za'a yi mana faɗa." Ya ce "Waye zai muku faɗan?" Haneefah ta ce "Mama, za ta ce me yasa ba mu kira an ɗauko mu ba." Ya ce "Sai in shiga in mata bayani, In ce sabon ɗa ta yi shi ne ya kawo k'annensa gida." Haneefah za ta kuma magana ya katse ta da faɗin "Kar mu tsaya ja_in_ja daku, ku shigo kawai mu tafi, kunga kun ce za'ai muku faɗa idan ku kai dare, ni kuma bazan barku ba sai na kai ku gida." Haneefah ta yi murmushi ta ce "To Mun gode." Neehal ta ɓalla mata wata uwar harara, Haneefah ta mata gwalo ta wuce ta zagaya ta buɗe murfin Motar ta shiga, ita ma Neehal ba ta da zaɓi wanda ya wuce ta shiga Motar tunda Haneefah ta riga da ta shiga. Karon farko a rayuwarta da ta shiga Motar wani wanda ba ta sanshi ba, amma fa ta ɓata rai sosai alamun ba ta so. *Sadik* ya yi murmushin jin dad'i, wani irin nishad'i yake ji a ransa, gajiyar da take damunsa tuni ya neme ta ya rasa. Neehal ta lumshe idanunta ta na sauke numfashi saboda k'amshin da ta shak'a da ta shiga Motar, wanda ya haɗe da sanyi Ac. K'amshin ya mata daɗi sosai domin har shige ta ji ya mata da na Yayanta. Sadik ya tambayi Haneefah unguwar su ta faɗa masa, kunna Motar ya yi suka hau titi suka fara tafiya. Su na tafiya su na hira da Haneefah wadda ta saki jiki sosai da shi kamar sun dad'e da sanin juna, Neehal kuwa sai harara take bankawa bayan Haneefah, ita ko ba ta ma san ta na yi ba. Har layinsu Neehal ya kai su, daidai k'ofar wawakeken gate d'in gidan Haneefah ta ce ya tsaya, bayan ya yi parking Haneefah ta ce "To new Bro, mun gode sosai fa." Sadik ya na murmushin da ya ƙi bacewa daga fuskarsa ya ce "Haba sai kace wani abun, ai nine da godiya da har kuka yarda kuka shigo 'yar akwalar Mota ta, kuna Manyan 'yan jarida." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kai Yayana akwai ka da zoyala." Neehal ta tab'e baki, kamar ba ta son magana ta ce "Mun gode, Allah ya saka da Alkhairi." Ba ta jira amsar sa ba ta buɗe Motar ta fice ta fara tafiya. Sadik ya bita da kallo wani abu na yawo a cikin zuciyarsa game da ita, Haneefah ma fita ta yi tare da yi masa sallama. Mai da dubansa ya yi gareta ya ce "Sai yaushe kuma?" Haneefah ta ce "Sai ransa Allah ya kuma haɗa mu." Complimentary card ɗinsa ya mik'a mata, Haneefah ta karb'a ta ce "Bye bye, Insha Allahu zan kiraka."