← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 118

Sashe 53

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ganin ta yi bacci Uncle Usman ya lalubo Numbern Aunty A'isha ya kira ta, sai da ta kusa katsewa sannan ta d'aga bakinta ɗauke da Sallama. Uncle Usman ya amsa ya ƙara da faɗin "Ina kwana Aunty dafatan kin tashi lafiya, ya su Hajiya?" Aunty A'isha ta ce "Lafiya k'alau Uncle Usman, su Hajiya suna nan k'alau, ya kwana biyu da bayan saduwa? inata kiran wayarka data Uncle Umar duk bana samun ku dafatan dai lafiya?" Uncle Usman ya ce "Lafiya k'alau, ai yanzu na koma Niger da kasuwancina ne, to idan ina can sai na sauke wannan layin, ina ta son na kira ki amma sabgogi sun sha mun kai, jiya_jiya ma na shigo garin." Aunty A'isha ta ce "Allah sarki, Allah ya taimaka ya ba da sa'a, wancan satin ai na fita daga takaba." Uncle Usman ya ce "Ikon Allah, lokaci ba wahala har kin fita, Allah ya ji k'an su Yaya." Aunty A'isha ta ce "Ameen ya Allah, a satin nan ma nake son shigowa Kano zamu zo siyayya bikin Sadiya ya kusa, ya labarin Neehal kuwa? kana zuwa kana ganin ta? Kullum da ita nake kwana nake tashi a raina, kwanaki ma na so zuwa na ganta Hajiya ce ta hana ni ta ce in bari na fita daga takaba tukunna." Cikin ɗacin rai Uncle Usman ya ce "Hmm, bari kawai Aunty wallahi Neehal wahala kawai take sha a gidan Ya Umar gurin Matarsa, yanzu ma muna asibiti bata da lafiya saboda dukan da suka yi mata jiya." A ruɗe Aunty A'isha ta ce "Subahanallahi, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, asibiti kuma? Wannan wanne irin duka ne haka? ashe shi yasa jiya na wuni da tunaninta a cikin zuciyata, har na kasa daurewa sai da na yi  zancenta a gida, Hajiya ta ce na kwantar da hankalina ai na kusa zuwa na ganta, ya jikin nata yanzu?" Uncle Usman ya ce "Da sauƙi Alhamdulillah, yanzu ma bacci take yi, Nima shekaran jiya na kira Ummi mun yi waya ne ta ce dan Allah in daure in je in dubo mata Neehal, ta tura ƴaƴanta sun ce ba su san gidan ya Umar ɗin ba, ita kuma tana fama da ciwon ƙafa baza ta iya zuwa ba, shine na zo na tarar da wannan abun takaicin. Wallahi Aunty A'isha baki ga ni ba, abun tausayi gaba-d'aya Neehal ta lalace ta yi baƙi ta rame duk ta fita hayyacinta." Aunty Aisha tana hawaye ta ce "Shi yasa naso tafiya da ita amma Uncle Umar ya hana ashe rabon wahala ne yake kiranta." Uncle Usman ya ce "Kar ki damu Aunty daga nan Gombe zamu zo na kawo miki Neehal da zarar ta ji sauƙi, ai kuma ta gama zama a gidan Ya Umar." Aunty A'isha ta ce "Kana ganin Uncle Umar ɗin zai yadda Neehal ta dawo gurina da zama?" Uncle Usman ya ce "Kar ki damu da wannan na san me zance masa kuma dole ya bari. Amma dan Allah Aunty  kar ki tada hankalinki fa komai ya zo ƙarshe ai dan zuwa gobe ma za'a iya ba mu sallama tunda ta ji sauƙi sosai." Aunty A'isha ta ce "Shikenan Usman na gode sosai, idan ta tashi daga baccin ka kira ni dan Allah." Uncle Usman ya ce "insha Allah zan kira ki, a gaishe da su Hajiya da Amarya, ace ina mata fatan Alkhairi kafin na zo." Aunty A'isha ta ce "Duk za su ji, sai anjima." Daga haka ya katse wayar. Ummi ya kira ya sanar mata halin da ake ciki, amma ya ɓoye mata wasu abubuwan dan kar hankalinta ya tashi sosai tunda ba ishashshiyar lafiya gare ta ba. Itama ta jajanta abun sosai ta kuma yi Allah wadai da halin Umar da Fauziyya, har ma da Ƴan'uwansu na cikin Kano wanda ko waiwayar Neehal ɗin ba sa yi alhalin suna gari ɗaya. Ta kuma yi na'am da mayar da riqon Neehal hannun Aunty A'isha da Usman ya ce mata zai yi, amma kafin su tafi Gomben ta ce ya kai mata Neehal ɗin ta gan ta..........✍️
[7/21, 9:03 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*3️⃣3️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
Chapter 53 · 0% Book details