← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 118

Sashe 57

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Zaune a kan darduma Mama ta tarar da Neehal ta jingina jikinta a jikin gado, Sallamar Mama yasa ta ɗago da kanta tare da amsa mata. Mama ta zauna a bakin gado tana dubanta. Neehal ta ce "Ina kwana Mama." Mama ta ce "Lafiya k'alau, me ya samu idanki?" Neehal ta girgiza mata kai, Mama ta ce "kuka kika yi ko? kuka dai ba ya maganin duk wata damuwa, addu'a ita ce kawai mafita." Neehal ta gyaɗa mata kai. Mama ta kalli su Afrah dake bacci ta ce "ƴan rigimart taki ba su tashi ba kenan?" Neehal ta ce "Ehh ni Mama dama ina son na faɗa miki me zai hana a saka su a makaranta kafin Allah ya bayyana iyayensu, kin ga idan na tafi school ko aiki kema in kin tafi asibiti sai su kaɗai fa a gidan, su Aunty Dijee ma kin ga suna zuwa islamiyya da yamma." Mama ta ce "Hakane kin kawo shawara mai kyau, ranar Asabar in Allah ya kai mu sai a kai su tahfiz, ranar Monday kuma sai na kai su school." Neehal ta ce "Allah ya kai mu." Mama ta ce Ameen, ga saqo in ji Dad ɗinki."  Neehal ta miƙa hannu dan karɓar abun da Mama take miƙo mata tana faɗin "Saqon mene?" Kafin Maman ta bata amsa ta gani da idonta, waro ido ta yi waje tana murmushi ta ce "Mama kar dai ki ce mun wannan nawa ne Dad ya siya mun Mota?" Ita ma Mama tana murmushin ta ce "Ban ce ba to, amma ni dai saqo aka bani kuma na isar." Neehal ta rungume Mama da sauri cikin farin ciki ta ce "Alhamdulillah, amma fa Dad ya iya surprise." Mama ta ce "D'aga mun jiki ni, sai a kula da titi sosai tare da kasancewa cikin addu'a a kodayaushe." Neehal ta ce "Insha Allah Mamana." A take Neehal ta tafi part ɗin Daddy ta masa godiya sosai, Mama ce ta yi musu breakfast yau dan ta san murna ba zata bar Neehal ta yi musu cikin nutsuwa ba. Ƙarfe tara da ƴan mintuna Neehal ce zaune a gaban mudubi tana ɗaura d'ankwalin atamfar dake jikinta, ɗinkin riga da skirt ne ya mata das a jikinta. Bayan ta gama ɗaura d'ankwalin ta saka ɗan kunne fashion mai kyau kalar one colour na jikin atamfar, sannan ta ɗaura agogo a left hand d'inta, ta zira abun hannu a right. Masha Allah ta yi kyau sosai small pink lips ɗinta sun sha white lipstick sai k'yalli suke. Su Afrah dake zaune a kan carpet ɗin bakin gado suna breakfast, ganin ta miƙe ta ɗauki mayafinta dake kan gado suka miƙe su ma da sauri suna haɗa baki gurin faɗin "Zan biki Aunty." Neehal ta kalle su ta yi murmushi sannan ta kama hannuwansu ta ce "Bana faɗa muku school zani ba, ku bari idan na dawo da yamma za mu je unguwa Insha Allah." Suka gyaɗa mata kai ba dan ransu ya so ba. Neehal ta yi picking goshinsu sannan ta ce su tafi ɗakin Mama ta musu wanka idan sun gama break ɗin. Ta yafa mayafinta wanda ya kasance babba ne amma ba me kauri sosai ba, sannan ta ƙara fesa perfumes ɗinta ta zira plate shoe d'inta ta ɗauki jakarta da car key ɗinta ta fice daga ɗakin tana yi wa su Afrah bye_bye. A falo ta tarar da Mama ta ce mata "Mama zan tafi sai na dawo." Mama ta ce "Allah ya kiyaye ina yaran fa?" Ta ce "Suna ɗaki suna break in sun gama na ce su zo ki musu wanka." Mama ta ce "To Allah ya bada sa'a, ki kula da titi fa kuma kar ki manta da addu'a." Neehal tana fita daga falon ta ce "Insha Allah Mamana, bye." A parking space kamar yadda Daddy ya ce mata Motar ta tana can, a nan ta ganta. Ta sa key ɗinta ta buɗe murfin Motar da bismillah sannan ta yi addu'a ta shiga zuciyarta cike da farin ciki, gaba-d'aya damuwar data kwanta da ita daren jiya a ranta ta ji duk ta gushe, Daddy ya faranta mata ba kaɗan ba, a rayuwarta tana son ta ga tana driving, tun da Daddy ya so siya mata Motar amma Mama ta hana. A hankali take driving ɗin cikin nutsuwa da kula, sai dai ba ta yi nisa da tafiya ba ta ga wata Motor kamar tana binta a baya, ba ta kawo tunanin komai a ranta ba, tafi zaton may be hanya ce ta haɗa su ɗaya da mai motar, sai dai yanda take driving ɗin a hankali ya ci a ce mai Motar ya zo ya wuce ta kamar yadda wasu motocin ke yi. Cikin ikon Allah ta ƙarasa har cikin Bayero lafiya, kuma har ta zo bakin gate ɗin makarantar Motar na biye da ita a baya. Ƙarfe biyu suka gama last lecture ɗinsu, ko Sallah bata tsaya yi ba ta yi wa Freinds ɗinta sallama ta yo gida, saboda tana son ta je gidansu Haneefah ta nuna mata sabuwar Motarta. Tana fita daga get ɗin makarantar ta hau kan titi kenan ta mudubi ta ga kamar motar d'azu ce ke kuma binta, ita tama manta da batun wata motar d'azu, dan ta yi tunanin mai Motar shima Bayeron zai je a d'azun. Gabanta ya yanke ya faɗi tsoro ya fara ziyartar zuciyarta, hakan yasa ta shiga karanto Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, da hasbinallahu'wani'imal'wakil. Har ta ɗan samu nutsuwa a ranta ta cigaba da driving ɗinta. Wata zuciyar na faɗa mata ƙila ma ba Motar d'azun ba ce irinta ce kawai. Sai dai kuma kamar ɗazun duk inda ta yi nan Motar itama take bi, har tafiya ta fara yi a slow wai dan ta ga ko Motar zata zo ta wuce ta amma still dai motar tana bayan tata..........✍️

Don samun complete document
09047871750
#500
[7/21, 9:03 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*3️⃣5️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
Chapter 57 · 0% Book details