← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 118

Sashe 49

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Misalin ƙarfe 2/:30mp Aunty Fauziyya ta aiki Neehal siyan kayan miyan gado, dan shi kaɗai ne aikenta tunda komai na abinci Uncle Umar ya siyo ya dire, sai kuma markad'e idan babu wutar Nepa. Babu musu ta karb'a kamar kodayaushe ta tafi. Yau ma kallon gidansu Ahmad ta yi ta wuce duk kuwa da yanda zuciyarta take azalzalarta akan ta shiga, amma tsoron abun da Uncle Umar zai mata idan Aunty Fauziyya ta faɗa masa yasa take ƙin shiga. Tana shan kwana Motar Ahmad na shigowa layin, cikin tsananin murnar ganinta Ahmad ya taka burki wanda har yasa ta tsorata ta yi baya. Da sauri ya buɗe murfin Motar ya fito, da mamaki ya ce "Princess." Neehal ta washe baki ta ce "Uncle ɗina ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau Princess, me yasa kwana biyu ba kya zuwa." Neehal ta ce "Uncle ne ya hana ni, ya mun faɗa sosai, He said in aka ƙara aike na na daɗe sai zane ni." cikin rashin jin daɗi Ahmad ya ce "Ayya I missed you alot dear." Neehal ta ce "Me too Uncle." Ahmad ya ce "Mu je gida in baki cake da sweet ɗinki." Da murnarta ta ce "Toh." Yanayin garin damuna ta fara shigowa dan shekaran jiya ma an yi ruwa, yau ma garin ya yi luf kamar hadari_hadari. Gashashshiyar kaza Ahmad ya bata da yoghurt, Neehal ta zauna ta ci ta k'oshi tay hamdala. Mantawa ta yi da wani tsoron Uncle Umar ta zauna ta shiga yi wa Ahmad hira, shi kuma yana ta aikin murmushi cikin jin daɗi da nishad'i, sai yanzu da ya ganta ma ya ƙara tabbatar da ya yi kewar ta sosai. Kiran sallar la'asar ne ya tashe su, Ahmad ya yi alwala suka fita tare ya rakata ta siyi kayan miyan sannan ya wuce masallaci ita kuma ta nufi gida. Zuwa lokacin hadari ya ƙara haɗuwa sosai har an fara Iska, sauri Neehal tay ta yi kar ruwa ya sauko tana waje, aiko ana idar da Sallah aka fara yayyafi, da gudu ta ƙarasa gidan dan har ta fara jik'ewa, kitchen ta nufa zata ajiye kayan miyan amma sai ta tarar da shi a kulle da mukulli, ga ruwan ya fara ƙarfi. Ƙofar falon ta dawo ta fara bugawa da ƙarfi tana faɗin, "Aunty! Aunty, na dawo ki buɗen ƙofa!" Amma Fauziyya tana ji ta ƙi buɗe ƙofar, gashi kaf tsakar gidan babu gurin fakewa, dan ko toilet babu duka suna cikin ɗaki, kitchen ne kawai kuma ta kulle. Gashi irin gidan nan ne da kana buɗe gate ɗinsa sai tsakar gida babu soro. Haka Neehal ta takure jikinta cikin ruwan dan bata da  yanda zata yi, cikin ikon Allah kuma ruwan ya tsuge kamar da bakin kwarya, Neehal ta runtse ido tana jin saukar ruwan ajikinta. A hankali kuma ya fara ɗaukewa, sai da ya ɗauke dif sannan Aunty Fauziyya ta buɗe ƙofar falon ta fito, Neehal na tsugunne a bakin ƙofar sai rawar ɗari take saboda sanyi ta ci kuka ta gode Allah. Aunty Fauziyya ta ɗauke kayan miyanta tare da faɗin "Kar ki shigar mun ɗaki kina yarari, ki jik'a mun ɗaki." Neehal ta miƙe ta cire komai na jikinta ta shanya a igiya, pant kawai ta bari sannan ta shige falon da sauri. Aunty Fauziyya tay dariyar mugunta ta ce "Gobe ma kya ƙara tafiya gantali Shegiyar yarinya kawai." Ita kam tana shiga ɗaki ta yi toilet ta cire pant ɗin jikinta ta rarumi towel ta ɗaura a jikinta sannan ta tsugunna ta yi fitsarin daya matse ta. Tana fitowa ta hau kan katifa ta ja bargonsu Aiman ta lullub'a. Kafin dare mura ta mata mugun kamu, ranar da tari ta kwana. Washegari duk masifar Aunty Fauziyya ba ta saka ta aiki ba, dan jikin nata ya yi zafi ba kaɗan ba, ta san ma ko ta saka ta ba iyawa zata yi ba shi yasa. Amma ta sha zagi da masifa, a cewarta cutar ma ta ƙarya ce da shegen rakin tsiya. Kwana huɗu ta yi a kwance, a ran na biyar ne ta fara samun sauƙi, shi ma sai da Uncle Umar ya ga ciwon ya ƙi ƙarewa sannan ya kaita chemist aka bata magani, aiko suna tafe yana mitar ta ja masa asarar kuɗin da ya siya mata magani, maganin da ko 1K bai kashe ba, alhalin kuma dukiyarta da duk wata kadararta tana hannunsa. Bayan ta warware aka cigaba da aikenta, kullum sai sun haɗu da Ahmad amma ta daina shiga gidansu sai dai su haɗu a ƙofar gida, yasan lokacin da ake aikenta, dan haka time ɗin yana yi zai fito ƙofar gida ya zauna zaman jiranta, saboda ta bashi labarin dukan da ruwa ya mata har ya sata zazzaɓi akan ta daɗe ranar, shi kuma saboda tsananin  tausayinta shi yasa ya daina tsayar da ita, dan kar a ƙara yi mata wata muguntar. Amma duk da haka bai daina bata abubuwan da yake bata abaya ba, idan ta je gurin mai kayan miyan akwai benci wanda dan customers aka tanade sa, anan take zama ta yi sauri ta cinye abun da ya batan sannan ta koma gida. Haka rayuwa tay ta tafiya da Neehal a gidan Uncle Umar cikin wahala da azaba kala_kala a gurin Aunty Fauziyya, gurin Ahmad kawai take jin daɗi, gashi ta yi magiyar a saka ta a makaranta an ƙi, har ta gaji ma ta dai na, sai ɗan lesson ɗin da Ahmad yake mata atsaitsaye.
Chapter 49 · 0% Book details