← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 154

Sashe 97

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda tazo falon Ummi dai-dai lokacin su Zaleeha ma suka dawo,
su Ummi duk sunata farin cikin musulunta dasu Solomo sukayi wanda Zaleeha ne ta gaya musu,
tana shiga Hayatuddeen ya kalleta tare da cewa.
"Wow Anty Ameena kinyi kyau wannan gayu haka".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ngd".
Sai kuma ta kalli Zaleeha dake juyo kan Adeel tana cewa.
"Papy kalli Momy, oyoyo Momy! oyoyo Momy!!".
ai kuwa Adeel na ganinta ya fara kaÉ—a hannu alamun oyoyo, kana Zaleeha na tayashi,
shi kuwa yaro sai dariya yake yana miƙa hannu alamun ta ƙarɓeshi yakeso,
hannu ta miƙo mishi tana kallon yadda Zaleeha ta biye mishi,
tana karɓanshi ya fara wawure-wawure so yake a bashi nono.
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"ÆŠan nema mai yawan ciye-ciye kalli yadda yake kokuwan a bashi nono kamar ya shekara bai shaba".
Dariya sukayi baki É—aya dan duk hankalinsu ya dawo kan Adeel da Momynshi.
Zaleeha ce ta É—anyi murmushi tace.
"Allah ko Ummi Autanki ne ya ɓata min papy na da yawanci, shi ya gado".
Tura baki Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"To wai waye baya cine da kuka tasoni gaba mijinku ma cine dashi kamar gara, amman da yake shi nakune bakwa faÉ—a".
Dariya Zaleeha tayi tare da cewa.
"A a kam Hamma Saif baida irin cinka, ko Ummi?".
Ta ƙarishe mgnar tana murmushi, wani irin daɗi ne ya rufe Ummi ikon Allah yau Zaleeha ke suffanta Saifuddeen da mijinta har tana kareshi,
Shima Saifuddeen ido ya É—an zuba mata a fakaice.
Shi kuwa Adeel zuƙan nono yake harda kamo ƙafarshi ɗaya, har wata zufa yake haɗawa,
shafa kanshi Saifuddeen yayi cikin son yaron da ganin darajar da kumar Uwarshi,
ya juya zai fita kenan Ummi tace.
"Saifuddeen zo muci abinci tukun".
Kanshi ya É—an jujjuya tare da mata alamar.
"Ummi kuci na ƙoshi".
Murmushi Zaleeya tayi tare da cewa.
"Autan Ummi ka gani ko".
Tura baki Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Waya san me kuka ciyo a woje".
Dai-dai lokacin Raliya tace.
"Dan Allah kuzo muje muci abinci ni yunwa nakeji".
Miƙewa Zaleeha tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah wlh a ƙoshe nake, yau a gajiye ma nake zan konta da wuri".
Cikin wani irin yanayin tuhuma da zato da zargi Ameena ta bita da lallo tana fita.

A ranta tace.
"Okay duk sun ƙoshi bazasu ciba, to me suka ciyo? Ina sukaje? Me suka wuni yi da tace a gajiye take?".
Take shaidan ya fara haÉ—a mata zato da zargi ya kuma zauna ras dan komai da hujja yake bata.

Abincin da itama bata iya ci ba kenan dan sai ruwa tayi tasha koda Ummi ta matsamata kan taci sai tace a ƙoshe take ƙawarta Samira ce ta kai musu awara shi sukaci shine sai ruwa suke tasha.
Koda suka gama ta saɓa ɗanta a kafaɗa ta nufi side ɗin.

Zaleeha kuwa dama kai tsaye É—akinta ta wuce, rege kayan jikinta tayi kana ta shiga wonka,
tana fita tayi shirin baccinta sannan ta konta.

Shi kuwa Saifuddeen aiki ya ɗanyi a system ɗinshi, inda ya ƙara samun damar bin diddigin Dalla dan ya dawo da niyar, rarake yan mata huɗu da yayi al'ƙawarin dan dama ya tafine dan badda sawu,
wannan dalilin yasa Saifuddeen bai bari direba ya kai Zaleeha ita É—aya ba ko É—aukota.

Koda ya gama aikinshi wonka mai rai da lafiya yayi dan Allah ya sani yana begen cingam ɗinshi, ya rigada ta saba mishi ko yaushe tana liƙe dashi kuma hakan na mishi daɗi yanzu tunda ya rigada ya saba.
Bayan ya gama kimtsa wa ne sai zuba ƙamshi yake,
ya nufi side É—in Zaleeha ganin tayi bacci sui ne yasa bai tada itaba rigarta ya ja ya É—an gyara mata a hankali ya fice ya tafi.

Ita kuwa Ameena da bata da niyar neman shi so take ya mata laifi kaɗan ta samu na ƙorafi,
haka yasa ta konta tasa É—anta a gaba.

Jin motsinshi ne yasa ta rufe ida nunta,
kunna hasken wayarsa yayi gane ba bacci takeyi bane ya sashi ɗauke Adeel cak ya medashi kan gadonshi kana ya dawo a hankali ya sauƙa kan kekenshi ya hau kan gadon ya konta inda ya ɗauke Adeel ya meye gurbin shi kenan,
ya zama suna fuskantar juna.
a hankali yasa hannu ya jawota jikinshi,
da sauri taja baya tare da juyawa ta bashi baya.
Hannunsa yasanya ya rungumota ta baya, fusge jikinta tayi, ranta amatuƙar ɓace, ta matsa daga kusa dashi, idanunta wanda suka kaɗa sukai jajur ta watsa masa, cikin fushi da ƙunan zuciya tace. "Kada ka taɓani, dan bani da buƙatar hakan, bani kaɗai bace matarka ai, kana da wanda kake ɗauka kutafi resturant da garden ai, ni dama menene amfani na awajenka, tunda na riga dana haifi ɗa, sannan kuma bankaita kyau ba, hakanne yasa kake ƙoƙarin fifi tata akaina, saboda kun fita yawon shaƙatawa, kunje kun more rayuwarku, dole ai kace bazaka ci abinci ba, tunda kana da ƴar gold kunje kun wuni liƙe da juna harda wani cewanta a gajiye take,ai ba sai ta faɗa min haka zan gane ta wuni a kanka kuna aurataiya ba."
Taƙare maganan cikin matsanancin ɓacin rai, da kuma tafasar zuciya, Allah yasani kishin Saifuddeen yaci ƙarfinta, saboda hakane ma take yarda da duk wani abun da zuciyarta ta raya mata.
Shiru yayi tare da tsura mata tsumammun idanunsa, ƙwarai yanda idanunta suka rufe, take faɗan duk wani abu da yazo bakinta, shine abun dake matuƙar basa mamaki, dan gaba ɗaya lokaci guda ta sauya, ta tashi daga Ameenan da yasani ada, ta dawo wata irin mace me yawan ƙorafi, da kuma yarda da zargi bata da wani mugun abu tare da ita illa kishi dake son fin ƙarfinta, wato dama duk ilimin mace dole kishi na tsaburarta sai dai wasu na iya dannewa, wasu basa iya, a zahiri dai babu matar da bata da kishi,kuma yaji ya sani ya yarda zazzafan son da take mishine yasa take tsananin kishinsa.
Kansa ya girgiza tare da sa hannu ya kamo hannayenta, tabbas dole zaiyi mata uzuri saboda yasan zafin kishi ne ke É—awainiya da ita, a wayarshi ya rubuta mata.
"Zargi bashi da kyau, kin sani ko a addinance, meyasa Ameena? meyasa ako yaushe kike yarda da abun da zuciyarki ke faɗa miki, meyasa ba zakina ƙaryata zuciyarki ba? kada ki cigaba da bari shaiɗan yayi tasiri acikin zuciyarki, tayaya kike tunanin aranan girkinki zan ɗau Zaleeha mu tafi garden ko resturant duk dan kawai na baƙanta miki, sam ba haka nake ba, ya kamata ace ke dakanki ki zama shaida, dan bana iya tauyewa kowa haƙƙinsa, sannan da kiketa ihun cewa munje resturant, ayaushe ne mukaje resturant ɗin? ya kamata ace kina kyautata mana zato, domin kuwa ba resturant mukaje ba, gidan Baba Malam mukaje, saboda yau akayi sadakan bakwai ɗin rasuwar Adda Maryam, zargi bashi da kyau, yana lalata aure, saboda haka ya kamata kina iya controlling zuciya, kishi, da kuma fushinki sabida bana so ki lalata mana zamanmu." Hannunta dake cikin nasa ta janye, kwata-kwata maganganun da ya faɗa basuyi tasiri acikin kunnuwanta ba duk da wani sashi na zuciyarta ya yarda da batunshi, sai dai zafin kishi da takeji ya danne komai hasalima jinsa kawai take, dan ayanzu kam gaba ɗaya idanunta sun rufe, wutar kishi ne kawai kecin zuciyarta, hakan yasa ba zata gane gaskiya ko akasinta ba, ganin yanda take ta sakin huci tana fitar da numfashi cikin fushi, ya sashi girgiza kansa kawai, tabbas tana ƙoƙarin ɓarar da damar da ta samu,
gyara kwanciyarsa yayi tare da kwanciya ya juya mata baya, saboda aduniya baya tunanin akwai wata mace da ta isa, yi masa fushi babu dalili, ya kuma rarrasheta taƙi ji, shiba sakarai bane, saboda haka bazai taɓa zama wawa akan mace ba, ko Zaleeha da ta kasance zaɓinsa ne takeyi masa haka, to tabbas bazai tsaya sauraranta ba, domin yariga dayasan ko awajen Allah bashi da wani laifi, tunda dai bai aikata ba dai-dai ba. Blanket ya ja ya rufa ajikinsa, tare da lumshe idanunsa. Ameena kuwa ganin yanda yayi kwanciyarsa ba tare da ya kara ce mata komai ba, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ƙara ɓaci, can nesa dashi ta matsa tare da jawo Adeel jikinta.

Saifuddeen kuwa dama baji yake ba, kuma gashi ya bata baya, hakan yasa baimasan tanayi ba, dan baccin gajiya ne ma keneman É—aukarsa.
Saida tayi kuka sosai kafun take maida ajiyar zuciya, jitake inama da ace Zaleeha bata dawo gidan ba, inama da ace Saifuddeen baikasance mijin Zaleeha ba, da duk hakan baifaru akanta ba, dan tanajin zata iya jure kishi da kowacce mace amma banda Zaleeha, ta jima sosai tana sheshsheƙan
Chapter 97 · 0% Book details