Sashe 35
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru falon ba kowa dan haka kai tsaye ya wuce bedroom É—inta,
kan sallaya ya sameta bisa dukkan alamu tayi walahane,
shiru yayi yana kallon yadda ta ɗaga hannayenta sama tana kwaranyo musu addu'o'i shida ƙannenshi, wanda mafi yawan addu'ar a kanshi ne a hankali take cewa.
"Ya Allah ga bawanka Saifuddeen cikin matsalolin rayuwar daka jarabceshi, ya Allah ina mai roƙa masa sassauci da salama da sauƙi a rayuwarshi ta duniya da lahira.
Ya Allah ka yaye mishi duk wani cuta dake jikinshi ka bashi lfy ka ƙaddara mishi sake miƙewa saye da sawunshi da sake mgna da ji,
Ya ubangijin talikai ka yassare masa ƙofofin samunshi gabas da yamma kudu da arewa, ya Allah ka al'barkaci kasuwancinsa ka tsare minshi daga sharrin mahassada damasharranta tsakanin mutun da al'jan, ya Allah ka tsare min imaninshi ka bashi ikon cinye jaraboɓunshi."
Sai ta kuma ƙara ɗaga hannu cikin kushu'i da ƙanƙan da kai take cewa.
"Ya Allah kayi mishi zaɓi mafi al'khairi tsakaninshi da matarsa Zaleeha in ita al'khairinsace Allah ka bashi haƙuri da juriyar duk wani abinda zai faru daga gareta, in kuma ita ba al'khairinshi bace, ya Allah ka musanya musu da abinda yake al'khairi a garesu baki ɗaya. Ya Allah ka karemin surkata a duk inda take."
sosai Saifuddeen yake wani irin lallausan murmushi yayinda shima ya É—aga hannayenshi sama yana mai amsa cikin ransa da .
"Amin Amin. Ameen ya rabbil izzati ya Ummi."
sosai ya tsura mata ido likacin da take cewa.
"Ya Allahna ga ɗana Hayatuddeen cikin ganiyar ƙuriciya da tashen balaga ya Allah ka shirya minshi ka tsare minshi, da tarbiyarsa ka kare min imaninshi ka sa mishi nitsuwa da kamala kwatan-kwacin na ɗan uwanshi, ya Allah ka yaye mishi wannan rawan kan da gigin ƙuruciya".
Sosai yake Murmushi Allah sarki Ummi wato rawan kan Hayatuddeen na tsoritata.
numfashi ya sauƙe a hankali ganin tana cewa.
"Ya Allah ka al'barkaci ahlina ka shirya minsu dama dukkan al'ummar musulmai ka azurta É—iyata Raliya da samun haihu da Æ´aÆ´a na gari ka basu zaman lfy da mazajensu."
Haka dai tayi ta musu addu'a yana mai amsawa da amin.
A tare suka shafa addu'an,
kana ta juyo ta fuskanceshi da kyau cikin sakin fuska tace.
"Dama kana gidane!."
Kai ya jinjina mata tare da mata bayanin zuwan bappa Ali da Baba Malam,
ya ƙara da cewa Bappa Ali yace sun tasoma dan haka zai jirasu kawai.
kai ta gyaɗa tare da miƙewa ta cire hijabin jikinta tana mai ninkewa take cewa.
"Eh lallai Faroq ya É—auki wayar yana game to inaga ya gama da cajinta ne ,
dan naga yazo ya sata a cajin.
jin haka ya É—an juyo ya jawo wayar dake haÉ—e a caji nan kuwa ya samu a kashen take.
juyawa yayi ya fito falon Ummi na biye dashi a baya tana gyara mayafin jikinta.
Suna zama ba jimawa kuwa su Bappa Ali suka iso.
suna cikin gaggaisawa ne Baba Malam da Malam Adam da Dirankadi suka iso bisa jagorancin Ahmad wanda yanzu ya dawo gida dan kiran bappa Ali daya samu.
Falon shiru bayan duk sun gama gaggaisawa,
A hankali Ummi ta miƙe da niyar basu wuri a matsayinsu na maza kuma manya su tattauna komai tsakaninsu,
sai kuma ta koma ta zauna jin Baba Malam yana cewa.
"Uhummm Ummin Saifuddeen zauna, akwai mgna mai mahimmancin da nake son muyi ne."
shiru tayi cikin jin tausayin mutumin wato wannan shine É—an kuka mai jawa uwarsa jifa."
Duk shiru sukayi suna sauraranshi.
Shi kuwa gyara zama yayi cikin nitsuwa da cikar kima yayi gyaran murya tare da cewa.
"Da forko dai zan fara da baku haƙuri akan rashin ɗa'a da Zaleeha tayi mana baki ɗayanmu,
wanda nake zargin kaina da cewa duk nine sila, tunda ku dai kun so'a janye batun auren tun kafin ayi auren, ni na kafe nace ayi sabida zatona itama irin Maryam ce in anyi auren zatayi biyayya ta zauna É—akinta, amman sai gashi ta samu asarar lokaci da dukiya da mutuncina ta gudu ta watsar da auren."
shiru yayi sabida yadda Bappa Ali ya fuskanceshi tare da cewa.
"Dan Allah na roƙeka Malam Bashiru ka daina bamu haƙuri da ɗaurawa kanka wannan laifin,
Wannan aurefa nufine na Allah, Allah ne ya É—aura aurennan kafin mu muka É—aurashi, kuma har gobe muna kyautata zaton zata dawo É—akinta ta zauna."
Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa.
"To mun isa muja da ikon Allah ne, babu laifin kowa a cikinmu, da Allah malam Bashiru ka daina tada hankalinka kam zancen yarannan."
ita dai Ummi shiru kawai tayi,
Saifuddeen da Ahmad shirun sukayi.
Sai kuma Dirankadi da Malam Adam ne suka ƙara kwantarwa Baba Malam hankali kan dan Allah kada ya sake zuwa da batun badu haƙuri.
Cikin jin sanyi a ranshi ya kallesu baki É—aya kana ya fuskanci Saifuddeen da kyau cikin sanyi yace.
"Dan Allah Saifuddeen ina neman wata al'farma a wurinka."
da sauri Saifuddeen ya nuna kanshi da Æ´ar yatsarshi alamun.
"Ni kuma al'farma kuma?."
Kanshi gyaÉ—a mishi alamun eh kai É—in dai.
sai ya kuma gyara murya da zama kana ya kalli Ummi, Bappa Ali da kuma Malam Ashiru yace.
"Ina neman al'farma a wurin É—anku É—alibani kuma surkina a wani sashin kuma É—ana.
Dan Allah Saifuddeen kayi haƙuri akan duk wani abun da Zaleeha tayi maka daka riƙe igiyar aurenka da ita naroƙi al'farma a wurinka da iyayenka duk rintsi kada ka saki Zaleeha, lallai kam nasan saki halalne duk da ubagiji baya son shi, ina roƙonka da Allah da manzonsa kada kayiwa Zaleeha abinda take buru da son kayi mata ka riƙe igiyar aurenku duk rintsi, domin inada yaƙinnin wata rana zata dawo gareka."
ya ƙarishe mgnar cikin rauni da alamun neman al'farma.
Su kuwa gaba É—aya idanu suka zubawa Saifuddeen daya fara musu bayani da yarensu na kurame wanda gaba É—ayansu suna gane hakan,
A hankali ya matso gaban Baba Malam cikin tanƙwashe ƙafafu yace.
"Baba Malam umarni zaka bani ba neman al'farma ba, in sha Allah bazan saki Zaleeha ba,
ka daina tada hankalinka."
shafa kanshi Baba Malam yayi tare da cewa.
"Ngd ngd Saifuddeen Allah yayi maka al'barka ya azirtaka da yara masu biyayya."
Amin Amin suka amsa baki É—ayansu,
Ummi kuwa sosai taji daÉ—in addu'arshi ga Saifuddeen É—inta,
Shi kuwa Baba Malam kallonsu yayi baki É—aya kana ya fuskanci Saifuddeen da kyau cikin muryar bada umarni yace.
"Maganata ta gaba ba al'farma nake nema a gareka Saifuddeen umarnune nake baka a matsayina na Malaminka kuma surkinga, ina mai baka umarni da fito da wata matar auren zan aura maka ita ko ƴar wayece ni ne nan zan auro maka ita, Saifuddeen aure za ƙarayi, a cikin watannan!."
Wani irin zabura da zare ido Saifuddeen yayi cikin tsananin mmki da kaÉ—uwa ya fara nuna kanshi da alamun tambaya.
"Aure kuma? Ni kuma inyi wani auren kuma, to ita Zaleehanfa, in mata kishiya."
Dirankadine yayi murmushi tare da dafa kafaÉ—un Saifuddeen É—in.
Jin an dafashi ne ya sashi juyowa ya kalli wanda ya dafashin kai ya runƙa jujjuyawa jin Dirankadi na cewa.
"Haba Saifuddeen aurefa akace kayi ba yaƙiba, me na wannan firgitan da ɗimaucewa,
to kai a zatonka barinka zamuyi ka zauna ba matane?."
Kainshi ya jujjuya tare da zaro wayarshi ya fara rubutu dan yanaga kamar dai basa fahimtarsa ne.
"Baba aure kuma, ko wata É—aya banyi da yin aureba, yaza'ayi kuma inyi wani auren,
ina da mata ai zata dawo, dan Allah baba ka bawa Baba Malam haƙuri, bazan fa iya zama da mata biyu ba."
Murmushi Dirankadi yayi tare da cewa.
"Me zai hana Saifuddeen tsab zaka iya zama da mata biyu."
Wayyo Ahmad kam ji yake tamkar ya tashi ya rinƙa taka rawa dan daɗin wannan umarni na Dottijon arziƙi Baba Malam, a ranshi yake cewa.
"Hegiya ifiritiya kin jazawa kanki kishiya,
Aure nai dai in sha Allah za'ayishi."
Ummi kam ita kanta taji daÉ—in wannan abu,
Yes tunda É—anta nada lfy har yanada muradin aure ainyi kuma ta gudu asheko dole a nemo mishi wata matar.
Murmushi tayi lokacin da Saifuddeen ya juyo yake mata mgna da yarensa.
"Wai Ummi kema naga murmushi kikeyi, nifa mijin mace ɗaya ne, ta yaya zan ƙara wani auren?."
Cikin dariya tace.
"A a to ni kuma ina ruwana, ka dai ji umarni ne yace ya baka ba neman al'farmaba."
Tirƙashi wannan shine ana wata sai ga wata,
kawai shi kam Saifuddeen ido ya zuba musu ganin da gaskefa sukeyi kuma Bappa Alima yayi na'am da hakan har cewa yake.
"Ahmad kuyi ƙoƙari ku fito da matar aure dan cika umarnin surkinku, kunji dai yace nanda mako biyu yakeso ayi auren,."
Wani mugun harara Saifuddeen ya dannawa Ahmad ganin yadda yaketa dariyar jin daÉ—i harda cewa.
"In sha Allah kuwa, Kawu Ali zumu fito da matar, ayi komai kamar yadda malam yake so."
Shi kuwa Baba Malam cikin son kontarda hankalin Saifuddeen yace.
"Ka nemo matar da take sonka,
Ni zanyi maka komai na auren ko sisinka bana buƙata."
Shifa yanzu ganinsu yake kamar al'mara,
su kuwa nan suka gama tattauna komai.
Ganin azahar tayine yasa suka yi addu'a suka tashi a taron kana suka sallami Ummi suka fita baki É—ayansu su.
Anan matsallacin jikin gidan nasu sukayi salla kana su Baba Malam da Dirankadi da Malam Adam suka tafi.
Su bappa Ali kuwa suka dawo cikin gida sukaci abinci sannan suka ƙara jaddawa Saifuddeen batun auren sannan suka tafi.
Su Babba Ali na fita Ahmad ya kwashe da dariya harda dukan cinya cikin jin daÉ—i ya kalli Saifuddeen daya haÉ—e fuska girarshi É—aya ya É—aga mishi tare da cewa.
"Ya akayi ne angon mata biyu a wata É—aya, kai Alhamdulillah lallai wannan dattijon ya cika adali mutun, kaga nanda mako biyu kana tare da sabuwar amaryarka dal a leda."
Wani irin bugu ya ya kaiwa Ahmad,
da sauri ya kauce tare da cewa.
"Sai fa an maka auren na."
Dariya Ummi tayi ganin yadda Saifuddeen É—in ya haÉ—e fuska cikin dariyar tace.
"To wai duk wannan haÉ—...!
Littafina na kuÉ—ine turo katin mtn na 300 ta wannan numbers 09097853276 ko ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.
Masu iya magana dai sunce kyauta da kayan wani mugunta dan haka masu fitarmin da littafi ku bari,