← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 154

Sashe 20

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren Zaleeha kuwa tana murzawa ƙofar key, da gudu ta haura kan gado tare da shigewa cikin blanket, ƙam haka ta kulle idanunta gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, sai alokacinne ma tatuna da irin shigar dake jikinta, take wani irin abu ya tokare maƙoshinta, tashi zaune tayi tare da duban kanta, ganin rabin ƙirjinta awaje, yasa ta cije baki, cikin takaici haɗi da kishin kanta tace.
"Sam baicancanci yaga surata ba, wayyo ni maiyasama nafita ne?."
Tsuka tayi tare da komawa ta kwanta, baccin tsorone ya É—auketa batare da ta shiryawa hakan ba.

Shikuwa Saifuddeen saida yasha artabu da jikinshi da zuciyarshi sosai kafun ya iya maida bacci.

Washe gari.
Kamar yanda takeyi tun da tazo gidan haka yauma tayi, tana gama idar da sallah tatafi ɓangaren Ummi inda tagaisheta.
Yau ɗinma Ummi cikin so da ƙauna ta amsa mata gaisuwarta,
a falo ta haÉ—u da Saifudddeen da Hayatuddeen bisa dukkan alamu daga masallaci suke,
cikin sakin fuska Hayatuddeen yace,
"Barka da safiya Aunty Zaleeha."
É—an tsayawa tayi fuska a sake tace.
"Barka dai autan Ummi."
murmushi yayi tare da cewa.
"Ya amarci da gajiyan biki."
hararansho taÆ´i cikin sanyi ta ratsa gefen Hamma Saifuddeen É—in harara ta cillamishi, sai kuma tayi wuf ta wuceshi kamar dai tsoro take kar ya cabketa
abinma dariya ya basu kana suka bita da ido.
daga ɓangaren na Ummi kaitsaye part dinsu ta  dawo, komawa tayi tanaɗe akan gado inda tacigaba da baccinta.

Acan gidan su Zaleeha kuwa sai jiya Mama tadawo daga tafiyanta da tayi, Baba Malam dai ko sannu baice da ita ba, koda ya lura cewa Zaheera bata gidan, tana can gidan Zaleeha, sosai ransa ya ɓaci, nanfa yasa Ya Ameenu Habu akan su kwashi kayayyakinta na aure da motocinta su kai maita kana su ɗauko Zahira sannan su ƙara yiwa Zaleehan nasiha inda yaje.
Hakan kuwa akayi, tuni Ya Ameenu da Habu sukatafi dan É—auko Zaheeran bayan duk sun lodo kayan aurenta a motocintan.
Koda sukaje gidan nasu Saifuddeen sai Ya Aminun ya bawa Habu kuÉ—i yacewa Habu ya hau keke napep ya koma ya É—auko motarshi su samu wacce zasu koma da ita tunda duk motoci biyun da suka zo dasu na Zaleehan ne É—aya na cikin kayan aurenta É—aya kuma wacce Ya Ahmad É—inta ya saya mata,
Ya Aminu na fitowa cikin motar ya nufi wurin maigaɗinsu akan yaje ya mishi sallama da masu gidan a nan suka haɗu da Ahmad, inda suka gaisa cikin girmamawa da mutum ta juna, Ahmad ne yayi masa jagora har cikin gidan, saida Ya Ameena yafara zuwa ɓangaren Ummi tukunna, cikin mutum tawa ya gaida ta, sannan yayi mata bayanin cewa yazo ɗaukar Zaheera ne,  sosai Ummi taji daɗin karramata da yayi, nan tasake aminta da tarbiyan gidan Baba Malam ɗin, Ahmad ne yayiwa Ya Ameenu jagora zuwa ɓangaren Zaleehan, don kuwa Saifuddeen bayanan, sun tafi meeting ɗin ƙungiyarsu na Jonapwd shida Ishaq.
Sosai Zaleeha taji daɗin ganin yayan nata, saidai kuma jin cewa Zaheera yazo ɗauka, yasanya taɗan ɓata fuska, saidai kuma bata isa cewa komai ba, sanin cewa Ya Ameenun nada zafi sosai, babu ruwansa yanzu saiya solleta soso da sabulu.
Haka Zaheera ma ranta baiso ba, don dai kawai Ya Ameenun ne yazo da kansa, amma da wanine bazata bisa ba, don ita ke gadin Zaleeha a cewarsu a yadda suka tsara kenan wai ai duk nacinsa bazai zo inda takeba in Zahira nan kuma da ita aketa plant É—in yadda Zaleeha zata gudu,

Haka dole ta haɗo kayanta, Gyara zama ya Ameenu yayi, cikin kulawa haɗi da kwantar da murya, yashigayiwa Zaleehan nasiha, dayi mata nuni akan tabi mijinta, idan ya umarceta da yinnabu matuƙar bai saɓawa shariya ba yace tayi to koda bataso tayi, domin hakan shine dai-dai domin al'jannarta na ƙarƙashin diga-diginsa .
Itadai Zaleeha jinsa kawai take, amma bata ɗauƙa, koda yazo tafiya har compound ɗin gidan ta rakosu,
nan kuma yasa Hayatuddeen da Imran dasu Zakariyya kwashe kayayyakinta kab suka shigar mata,
sannan ya bata car keys ɗinta duka biyu a hannunta, godiya tayi tare da cewa ya gaishe mata da Ƴar uwarta Maryam.
Haka Ya Ameenu yatasa Zaheera suka bar cikin gidan, shikansa ya yaba da tsarin gidan, musamman ma part ɗin Zaleeha wanda yayi matuƙar kyau, shida kansa ya ƙyasa, ya kuma yabawa Saifuddeen sosai, don bakowani namiji bane zai iya ɓarnatar da dukiyarsa wajen ƙawata gida mai kyau kamar haka ba.

Tafiyan Zaheera yasa Zaleeha duk taji gidan bayayi mata daɗi, hakanan taji komai ya tsaya mata, batasan dacewa motsin Zaheeran na ɗebe mata kewa ba, sai ayanzu da Zaheeran tatafi, haka ta koma ɗaki ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.
Tananan ƙule aɗaki har akayi sallan isha,
Nanfa wani irin tsoro yashiga diro mata, take fargaba ta cika zuciyarta, sam batajin zata iya kwana itakaɗai aɗakin batare da wani nata ba, sosai tsoron sa yashiga zuciyarta, tabbas ayanda taga cikin idanunsa jiya to idan tayi wasa komai zai iya aikata mata, abanza saiya rabata da virginty ɗinta, shikenan kuma daganan yagama cutanta, dan tasa aranta cewa bamakawa daga ranan daya yayi disvirgin ɗinta tofa shikenan itakam ta sallama rai da rayuwa, don baƙinciki ne zaiyi ajalinta tabbas.
Tashi tayi daga kan sallayan tare da kai dubanta jikin ƙofar ɗakin, ganin babu key ajikin ƙofar yasa gaba ɗaya hankalinta ya ƙara tashi,  atsorace tashiga neman key ɗin amma bata gani ba.
Ƙirjintane yatsananta bugu alokacin da taji motsin mutum a falonta.

Shikuwa Saifuddeen lokacin dawowansa kenan daga masallaci, kaitsaye É—akinsa ya wuce, dan yanaso yaÉ—an watsa ruwa, kafun ya ya É—a ci abinci.
Jin motsin buɗe kofar falonsa, dakuma rufewa yasanya taɗanji zuciyarta tayi sanyi, cikin hanzari ta ɗauki blanket da pillow, saikuma phone ɗinta, saɗab-saɗab tafito daga cikin ɗakin, ahanzarce tayi hanyar fita daga cikin falon, tana samun kanta aɗan compound ɗin shashin nata kuwa ta saki ajiyar zuciya,  kaitsaye garden ɗin dake cikin part ɗin nata ta nufa wanda yake cike da sanyi da sauraye, kan wata kujera dake ɗan cikin garden din ta kwanta, tare da jawo blanket ta rufa jikinta, ɗaura kanta tayi akan pillow tare da sauƙe ajiyar zuciya, ta dai gwammace kwana awajen da dai ta tsaya aciki ya illata mata rayuwa, zata jure komai amma bazata iya jure abinda zai iya mata ba, hakanan bata tsaya wani mugu yayi disvirgin ɗinta ba tunda ta duba ɗaya ɗakinma babu key sai tayi zaton shine ya zaresu dan karta rufe ƙofa ya samu damar shigowa ya mata fyaɗe injita da faɗi.

Raliya kuwa wacce tazo rufe window'n ɗakinta dake abu ɗe ne taga kaman wulgawan mutum ya shiga cikin garden, kanta tasake zurowa ta cikin window'n, nan idanunta suka gane mata Zaleeha dake ƙoƙarin kwanciya akan wata kujeran ƙarfe.
Mamakine yakusan  kasheta awajen, sosai abun ya ɗaure mata kai, komawa cikin ɗakin nata tayi ta zauna tare dayin jigum, me hakan yake nufi kenan? tsanar da Zaleeha tayiwa ɗan uwanta har yakai wanda zataƙi haɗa shumfuɗa dashi? har ta gwammaci kwana acikin sauro da ciyawi da sanyi a kan kujerar ƙarfe akan ta kwana dashi.
Kanta ta jinjina tare da rumtse idanunta wanda suka ciko da ƙwalla, sam bahaka ta ke wa ɗan uwannata fata ba, babban burinta shine yasamu ingantaccen kulawa daga wajen matar tasa amma meyasa Zaleeha ke gudunsa?
kwaffa tayi tare da cewa.
"Ko ya zakiyi wlh in sha Allah sai dai ya raɓi jikinki in Allah ya yarda duk iskancinki kin shiga hannu kenan mutu ka raba, ato sai yaci sadakinshi."
Tana faɗin haka sai kuma ta miƙe da sauri ta nufi.....!

Littafina na kune in kin ganshi a wojema na satane, turo É—ari 300 ta wannan no 09097853276 ko ka/kiyi min transfer'n 300 ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

Wanda ya karanta na sata Yaseeeen doguwa.

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Cikin bedroom É—in ta da nufin zataje ta sanarwa Ahmad,
ko meye ta tuna kuma, oho sai ta koma ta zauna tana nazari.
Sosai abun yayiwa Raliya ciwo, koda Ahmad ya fito ganin meya tsareta,  kamar zata faɗa masa saikuma tayi shiru, shi kuwa da bai san meke faruwaba sai janta yayi suka koma bedroom ɗinta dan yana tare da begenta.

Ɓangaren Saifuddeen kuwa kwata-kwata ma bai nemi Zaleehan ba, yana fitowa daga wanka kwanciya kawai yayi,  sam bayaso yaje gareta, harma yaga abun da zai rabasa da nutsuwarsa, dan shikaɗai yasan irin azaban dayasha jiya, saboda haka baya sake fatan shan wani azaban kalan wannan, kasancewar agajiye yake hakan yasa yana kwanciya bacci ya ɗaukesa.
Zaleeha kuwa gaba ɗaya tatakura akan kujeran da take kwance, sam kujeran bata da daɗin kwanciya bare daɗin bacci, cikin mintuna ƙalilan har jikinta yasomayi mata ciwo, gawani irin masifaffen sanyi dake busawa acikin garden ɗin, mutsutstsuka jikinta kawai takeyi, sosai takejin wuyanta ya ƙage amma kuma bata da wani zaɓi, wanda ya wuce yin haƙurin kwana awajen.
Atakure haka bacci ɓarawo yasamu nasarar ɗaukarta.

Ƙiran sallan asuban fari da akeyine ya ratsa jikinshi ya bashi lokacin salla yayi, ahankali ya buɗe idanunsa,  ɗan miƙa yayi tare da haɗawa da salati a zuciyarsa, nan yatashi zaune, kekensa ya jawo tare da hawa kanta, cikin nutsuwa da ɗan sauran kasalan bacci yakai kansa banɗaki, wanka yayi tare da ɗauro alwala, kaitsaye yafice daga ɓangaren nasa.
Har yaƙarasa jikin ƙofar na Zaleehan saikuma wani tunani yazo masa, take yafasa shiga tada'ita da yayi niyya, sai ya ƙonƙasa mata ƙofar, kana ya juya ya tafi,
kai tsaye yawuce masallaci.
Chapter 20 · 0% Book details