Sashe 57
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Suna shiga ta yunƙura ta tashi zaune cikin sanyi tasa hannunta da yayi sanyi ƙalau tamkar ƙanƙara ta riƙo hannun mahaifinta.
Kai ta girgiza take kuma saiga hawaye sun silalo daga cikin idanunta, cikin muryarta dake fita da sanyi tace.
"Baba Malam ka yafe mi ninaji ajikina cewa bazan tashi ba Baba, dan Allah kayafemin in akwai laifin da nayi maka."
Da sauri Baba malam ya riƙe hannunta tare da cewa.
"Ni kam bakiyi komai ba Maryam, koda ko kinyi min na yafe miki duniya da lahira, bare ni baki min komai ba face biyayya, ubangiji ya yassare miki rayuwar duniya data lahira."
Hannu tasa ta share hawayenta murya na rawa tace.
"Nagode Babana."
Da ƙarfi zuciyar Baba Malam ta buga jin yadda ta kirashi, kama hannunta yayi da kyau jin tana cewa.
"Sannan kuma ina neman wata al'farma a wurinka Babana".
Zuciya a tsinke yace.
"Wacce al'farmace Maryam gaya min".
Lumshe idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka kwaranyo mota, cikin sanyin murya tace.
"Dan Allah ina son ka dawo da Mama dan Allah, ka kuma yafewa Æ´ar uwata Zaleeha, dan Allah Baba kayafe mana baki É—ayanmu Baba Malam ka yafewa Zaleeha dan kada rayuwa tayi mata muni bance kada kayi fushi ka nuna mata illar abinda tayiba, amman kada kuyi dogon fushi da ita, sannan in Mamana tazo kace mats na nemi yafiyarta, ta gafarta min".
Sai kuma ta fara kuka murya na rawa taci gaba da cewa.
"Baba malam Nasan duk inda Zaleeha take. Duk inda take a faɗin wannan duniyar in dai tana raye in taji rasuwata zata zo, dan Allah idan tazo kace mata na ajiye mata saƙo a cikin durowar gadona, kuma kada taje ita kaɗai in zata ɗauka taje ita da Mijinta Saifuddeen sannan kacewa. Ya Ahmad da Zakariyya kada suyi dogon fushi da Zaleeha su zame mata madadina."
taƙare maganar tana dhessheƙan kuka, kai Baba Malam ya jijjiga lokaci ɗaya hawaye suka cika idanunsa, hannunta ya kama ƙam cikin matsanancin ƙaunar ƴartasa yace.
"Insha Allah zaki tashi Maryam, za ayi miki aiki lafiya, kidaina faÉ—in irin waÆ´annan maganganun."
Murmushi tayi tare da kamo hannun Ya Ameenu wanda tuni hawaye sun wanke masa fuska, cikin matsanancin ƙaunar mijin nata tace.
"Inaji ajikina cewa zan barka Yayana, zantafi inda bazaka sake ganinka ba, kakulamin da Ayman É—inmu kaji, sannan kayafemin duk wani abu danayi maka."
Kuka Ya Ameenu ya fashe dashi tare da durƙushewa awajen, don bayajin zai iya cewa komai.
Mamy ma kuka take, nan ita da Ya Habu suka kama hannun Maryam É—in, murya asanyaye Mamy tace.
"Ki daina faÉ—in haka Maryam zaki tashi da yardan Allah."
Hannun Mamyn Maryam tasake riƙewa sosai, cikin muryan kuka tace.
"Ku yafemin Mamy, idan Zaleeha ta dawo kice mata nace tabi mijinta sauda ƙafa tayi masa biyayya, danni kam bazan samu daman faɗa mata hakan da bakina ba.
Ya Habu kaima kayafemin, sannan kada kuyi dogon fushi da Zaleeha."
Kukane ya ƙwace wa Mamy, da Ya Habu, Baba malam ma hawaye yake sosai.
Ganin haka yasa nurses ɗin suka tura keken sukayi ciki da Maryam ɗin, tana kallon Ya Ameenu shima yana kallonta haka aka shiga da ita ɗakin theatre'n, kuka sosai Ya Ameenu yasa kaman ƙaramin yaro, Baba Malam ne ya riƙesa yana rarrashinsa.
Ameena kuwa koda taje asibitin aje Adeel tayi awajen wata ƙawarta mesuna Umaima, nan ta nufi theatre room dan ansanar da ita cewa, babban Dr ɗinsu na nemanta acan ɗin.
Takusan kaiwa theatre room ɗinne tahango Baba Malam, Ya Ameenu, da kuma Ya Habu, sai Mamy suna tsaitsaye, cikin sauri taƙarasa garesu, ganin fuskokinsu ɗauke da matsanancin damuwa yasa jikinta yin sanyi asanyaye ta gaidasu, tare dayi musu tambayan halan ko wani suka kawo bashi da lafiya, dan taga idanunsu gaba ɗaya sunyi jajur.
Hankalim Mamy amatuƙar tashe yake faɗa mata cewa.
"Maryam ne suka kawota haihuwa, ankuma ce dole sai theatre za'ayi mata, yanzu haka ma anshiga da ita É—akin theatre'n."
Hankalin Ameena ne ya tashi sosai, take cikin sauri ta nufi É—akin theatre'n.
Littafina na ƙuɗine in kina buƙata turo katin mtn na ɗari uku ta wannan no ɗin 09097853257 ko kimin transfer ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.
     By
*GARKUWAN FULANI*
       Â
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: *(heart touching)*