Sashe 147
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fahimtar hakane yasa. Ummi miƙewa,
ta fita cikin jin daÉ—i, hakama Raliya ta bita a baya,
suka tafi cikin tsananin jin daÉ—i.
A ɗakin Saifuddeen ɗin kuwa cikin kula ya Adnan ya ɗaura mata wani ɗan leden ruwa ƙarami,
dasa mata alluran cin abinci,
daurewa iya daurewa Zaleeha tayi amman duk da haka saisa ta fidda hawaye da anasa mata allurar ruwan a hannunta,
Hamma Saif kuwa cikin kula da lallama yake in boddy language yake cewa.
"So sorry Sannu ko, da zafi ko? Ya Adnan ayimata a hankali".
Dariya Ya Adnan yayi kana ya tattara kayan aikinshi yace.
"Raki da raki sun haÉ—u, a kula da cin abin cinta, domin bawai cikinne ya sata amai da jirinba, rashin cin abinci ne yasa yunwa yayi ta murÉ—anta, yunwarce kuma tasa mata jiri da kasala da duhun da take gani, so dole a kula da ita da cin abinci."
cikin gamsuwa Hamma Saif in boddy language É—insa yace.
"In sha Allah zan kula ya Adnan, na lura kam tunda na dawo bata son cin abinci".
ƙarishe haɗa kayanshi yayi kana ya sallamesu ya tafi.
Yana fita Hamma Saif ya hau gadon da kyau, hannunshi yasa yana shafa gashin kanta,
ita kuwa Zaleeha tunda taji Ya Adnan ya ambaci kalmar ciki sai tayi shiru tana bin Hamma Saif É—inta da ido,
cikin tsananin jin daɗi yayi mata rubutu a wayarshi ya miƙa mata,
"Maman Baby, maman yara Ammin Adeel, my happiness my life my Everything. Ngd Ngd Ngd matuƙa,
Alhamdulillah Zaleeha Allah ya azurtamu da samar da abu É—aya, jinina da jininki sun kasance a sashi É—aya, burina da fatana sun cika kina da ciki har na tsawon wata biyu da sati uku".
Sai kuma ya sunkuyo yayi kissing goshinta,
ita kuwa Zaleeha lumshe ido tayi da sauri bayan ta karanta abinda ya rubuta mata,
hannunta tasa bisa lafeffen cikinta, wani irin daÉ—i farin ciki salama ne suka cika mata zuciya a baiyane tace.
"Alhamdulillah. Allah na gode maka da kyautar da kayi min, ya Allah ka al'barkacin abinda ke cikina,
ka bani shi mai kama da mahaifinsa".
Sai kuma ta É—an buÉ—e ido ta, Hamma Saif É—in nata, rubutun da yayine ta kuma karantawa.
"My dear meyasa!? Meyasa!!? Meyaaa!!!? Baki sanarmin kinada cikiba, meyasa kika ɓoye min abin farin cikinmu?".
A hankali ta kalleshi cikin sanyi tace.
"Hamma Saif nima bansan ina da cikiba".
Da sauri ya rubuta mata.
"Kamar yaya baki sani, tunda bakiga al'darkiba har wata biyu har na uku, ai yaci kisan kinada ciki".
A hankali tace.
"Hamma Saif ni ba ko wanne wata nake al'adaba, ina tsallake wata, wani lokacin har wata biyu nake tsallakewa sai ana uku sai ingani, shiyasa yanzunma da ban ganiba ban damuba dama duk zatona wata ƙil ƙarshen watannan zanyi dan ban taɓa tsallake wata ukuba a tunanina nanda kwana biyar zan gani".
Da sauri yasa hannu ya zare alluran ruwan dan ganin ruwan ya ƙare,
É—agota yayi ya ruggumeta a jikinshi tsam, yana kissing nata tako ina.
A cikin gida kuwa,
Dr Adnan na fita Ameena na shigowa.
A can falon Ummi kuwa cikin farin ciki Ummi tace.
"Ni dama na daɗe da zargin Zaleeha nada shigar ciki, dan har kamar zan gayawa Saifuddeen sai kuma nace bari dai in barsu inga zasu gane da kansune ko sai an ganar dasu, kuma da yake sabbin shigane duk basu ganeba, kai yarinta da daɗi ƙuruciya dangin hauka.
Hayatuddeen ne da Ahmad dake ta farin cikin labarin suka haÉ—a baki wurin cewa.
"Au Ummi itama Zaleeha bata san tana da cikinba".
Raliya ce tace.
"Ato da alama kam bata saniba, dan in ta sani ai Hamma Saif zai sani".
Dariya sukayi baki É—ayansu.
Dai-dai lokacin Ameena ta shigo.
bayan sun gaisa da sune ta kalli Hayatuddeen daketa cilla Adeel sama suna dariya tace.
"Autan Ummi yau farin ciki da sassafe babu baƙin halin tashi daga bacci mai ka samu haka?".
Cikin dariya yace.
"Yo Aunty Ameena ai dolena in girma tunda naga kun dage tuƙuru zaku cika mana gida da yara, Adeel zaiyi ƙani ai dole in daina yarinta kada ayi uban banza".
Cikin mmki da rashin fahimta ta kalli su Ummi dake dariyar mgnar Auta, a hankali tace.
" Ummi me muka samune".
Cikin kula Ummi tace.
"Ammin Adeel ne, ta kwana ba lfy, to shine da Yayanku yazo ya gwada yake cewa cikine gareta".
Wani irin sassanyan murmushi Ameena tayi cikin jin daÉ—i da kekyawan zuciya tace.
"A a Alhamdulillah. Adeel ya girma, ya zama babban yaya, Allah ya sauketa lfy".
Amin Amin suka amsa baki É—ayansu.
Sosai sukayi farin ciki,
Nan Ameena da Raliya suka shiga kitchin.
Ummi kuwa É—akinta ta koma,
a waya ta sanarwa Raihana dan tasan Adda Rahma kam mijinta zai gaya mata.
ta kuma sanarwa Goggo Dada da Aunty Mina ma sosai yan uwa da abokan arziki sukayi ta murnar cikin.
A can sashin Saifuddeen kuwa,
shi da kanshi ya taimaka mata, a tare sukayi wonka,
kana suka shirya,
rigar daya cire mata ta maida,
daga nan ta nufi É—akinta dan canza sakekkiyar riga.
Shi kuwa Saifuddeen tana fita ya fara kiran abokanshi yana sanar musu,
sosai sukayi ta farin ciki sunayiwa Zaleeha tsiya wai ai dolema ta gudu ta kuma dawo da kafarta, wai Adeel ne ya korata, cikin kuma shi ya dawo da ita.
Ishaq ne ƙarshen kira dan yasan angone kar ya takurashi da sanyin safiya.
Ishaq kuwa yana jin wayarshi na rigging amman bai samu damar É—agawa ba,
sabida yana lallaɓa amrya Rashida da yayi mata Dalla Dalla, sabida sam ya kasa ɗaga mata kafa, kun san riƙaƙƙun tuzurai ba sauƙi.
Yana tafe yana kuma gwada kiran Ishaq, yana shiga falonshi Ishaq na amsa kiran cikin tsokana yace.
"Ango kasha mai".
Dariya Ishaq yayi tare da cewa.
"Caɓa-caɓa ma kuwa mai kam harda lagwada, ai da nasan haka abin yake da ɗan karen daɗi da tuntini nayi aure".
Dariya sukayi baki É—ayansu,
Rashida dake manne jikin Ishaq É—inne ta É—an sune kanta a jikinshi.
shi kuwa Saifuddeen cikin happy yace.
"Al'bishirinka".
Da sauri Ishaq yace goro".
dariyarsa mai sanyi yayi cikin jin daÉ—i yace.
"Ka kusa samun ƙanin Adeel, jiya tunda muka dawo Baby keta amai ashe, cikine ni bamu saniba sai ɗazu ya Adnan ke sanar min."
Cikin tsananin jin daÉ—i Ishaq yace.
"Alhamdulillah, kai nayi farin ciki, kai mutumina ba sauƙi kai ko yaushe bugu ɗaya kake jefa ƙollo a raga".
Dariyar keta Saifuddeen yayi tare da cewa.
"Sune zalamammu daga na basu sai su ƙarɓa, kuma dama Zaleeha kam addu'ar da nayi tayi kenan, har a kaba na roƙi Allah ya azirtamin samun haihuwa da ita akai-akai kafinma ta ankara, gidana ya zame mata farin cikin duniyar ta, ta haifo min yara dozin-dozin".
Dariya sosai Ishaq yayi kana yace.
"Mugu, to Allah ya sanya al'khairi ya sauƙeta lfy".
Amin Amin yace kana sukayi sallama".
Daga nan ya shiga falon Zaleeha a falon suka haɗu cikin kula ya miƙo mata hannu, kana suka nufi falon Ummi.
Suna shiga, duk suka gaggaisa, hannu Zaleeha tasa ta karɓi Adeel dake hannun Hayatuddeen,
cikin kula sukayi mata sannu da jiki.
Ameena da Rayila ne da suka gama shirya breakfast a dinning table suka iso falon cikin sakin fuska Ameena ta kalli Saifuddeen fuska a sake tace.
"Congrats Abban Adeel, Allah ya sauƙeta lfy".
Amin Amin sukace baki É—ayansu,
Ita kuwa Zaleeha sunkuyar da kanta tayi ƙasa cikin tsananin jin kunya.
Shi kuwa Saifuddeen wani irin fitinenne kallo yakewa Ameena kallo mai cike da mutun taka, ji yake tamkar ya kamota ya ruggumeta, amman ba dama, ita kuwa ganin kallon da yake matane yasa ta meda kanta kan Zaleeha sabida taga Saifuddeen kallon farin cikin tayashi murnar da tayi yake mata ta hango wani baiyanenne farin ciki a fuskarshi cikin kula tace.
"Ammin Adeel ya jikin?".
A hankali tace.
"Na worke fa Ummu Adeel".
Dariya Raliya tayi tare da cewa.
"In kinci abinci ne zamu yarda kin worke".
Da sauri Saifuddeen ya jinjina mata kai alamar da kyau.
Ahmad kuwa dariyar ƙeta yayi tare da cewa.
"Allah ya fito mana da _Sodangi_ mu lfy, dan dai shine ya somu yasa aka gudu aka kuma dawo,
Jingudo haka sunan yake ko macece ko na mijine".
Dariya sukayi dukansu, Ameena kuwa shiru tayi.
Kalmar Jingudo da Ahmad ya kira ta amsa mata tarin tambayoyin dake ranta na cewa ina Zaleeha taje
Dan duk cikekken bafulatani in yaji an kira yaro da Jingudo ko Sodangi to yasan auren dole akawa mace, ta haifeshi a gidan wanda aka aura mata dolen, to shi ake cewa Jingudo."
A ranta ta tuno kalmar Adda Rahma inda take cewa mata.
"Kan Abu ɗaya ya taɓa nuna ƙulafashinsa a duniya a kanta ne kaɗai,
Sai ta kuma nazarci kalmar Ahmad na cewa Allah ya fito mana da Sodanginmu lfy don dai shine ya somu an gujemu an dawo".
Kai ta rausayar jin Ummi na cewa suje suci abinci.
kan dinnin table É—in suka nufa, tana mai magar zuciya.
"Uhumm Ahmad kenan da kenan ka sani yanzu son Abban Adeel da nake hangowa cikin idonta ya wuce zaton mai zato, Allah sarki wato auren dole akayi mata, da alama kuma guduwa tayi lokacin da Adda Maryam ta rasune ta dawo ikon Allah to meyasa Zaleeha zataƙi Abba Adeel duk da tarin kyanshi da dukuyarshi basu ruɗeta ba."
Jin Saifuddeen ya murza hannunta alamun taci abinci ne yasa tasa hannu ta fara ci.
Zaleeha kuwa sanadin alluran da akayi mata to ta samu taci abinci sosai,
shiyasa duk jiri da murÉ—a da duhun suka tafi sai É—an kasalar da ba'a rasaba.
Ranar dai Saifuddeen wuni yayi yana jinya,
shida kanshi kuwa ya kira Ya Ameenu da ya Ahmad ya sanar musu batun cikin Zaleeha,
sosai Ya Ahmad yai tawa Zaleeha wasa wai ashe yanzu kam girma yazo zata bar guje-guje.