← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 154

Sashe 63

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Ameena, wanda ke tsaye agefe, sosai jikinta yayi sanyi da rasuwan Adda Maryam ɗin, Da taimakon Ya Habu doctor ɗin ya ɗan yayyafawa Ya Ameenu dake sume ruwa akan fuskarsa, cikin abun da baiwuce minti ɗaya ba kuwa Ya Ameenu'n ya farfaɗo da wani irin gigitaccen kuka, dukansu kuka suke anrasa wanda zai rarrashi wani acikinsu, da ƙyar Baba Malam ya iya tsaida kukansa, ganin cewa magriba ta kawo kai, tasowa yayi inda ya ƙaraso har wajen da Ya Ameenu'n ke zaune, har yanzu kuka yake me tsuma zuciya, yayinda ya jingina kansa da jikin gadon da gawar Maryam ɗin take, dafa kafaɗansa Baba Malam yayi, cikin da shashshiyar muryarsa yace.
"Kayi haƙuri Ameenu, ayanzu Maryam bata buƙatar kukan mu, tafi buƙatar addu'ar mu fiye da komai."
kai Ya Ameenu ya shiga jijjigawa cikin matsanancin kuka, yace.
"Yazanyi na daina kuka Baba, bazan iya ba, bazan iya daina kuka ba, bazan iya jure rashin Maryam ba Baba, mutuwa ta ɗauki Maryam ta barni, mutuwa ta nisanta ni da Matata, mace mafi soyuwa agareni, tayaya zan iya jure rashin Maryam, wanda koda sau ɗaya ne bata taɓa ɗaga min murya, ko ƙin abun da nakeso ba, komai nakeso shi take so, idan nace kada tayi, har abada bata taɓa yi, idan na umurceta bata taɓa tsallakewa, farinciki na shine nata, ta amince da aure na batare da tana sona ba, hakan kuma baisa taƙi min biyayya ba, Dama mutuwa ta sani da ta barmin Maryam saboda ina da buƙatarta acikin rayuwata!."
sake rushewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya yayi, idanu Baba Malam ya lumshe take wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunsa, matuwar Maryam tayi matukar girgizasa ƙwarai, yanaji yana gani mutuwa ta ɗauki ƴarsa agaban idanunsa, mutuwa ta ɗauki ƴarsa mafi soyuwa agaresa, ina ma da ace mutuwa tana neman zaɓi, tabbas daya bata zaɓi ta ɗauke Zaleeha tabar masa Maryam, saboda Maryam takasance tamkar haske ne awajensa, takasance meyi masa biyayya, ita da Ahmad sun kasance suɗin daban suke acikin ƴaƴansa, masu tsananin biyayyya ne suɗin.

Sanin cewa kuka bazai bawa Maryam É—in komai ba, yasa can cikin zuciyarsa ya soma ambaton sunan Allah, yana meyi mata addu'a, cikin ransa kuwa, yanajin cewa Insha Allah, Maryam É—in zata dace da rahamar Allah.
Duban Mamy dake kuka sosai yayi, kana ya kalli Ya Habu wanda shima kukan yake kaman ƙaramin yaro, dai-dai nan Dr Adnan ya shigo cikin ɗakin, gaba ɗaya jikinsa amace yake, dan kuwa labarin rasuwar Maryam ɗin yaje kunnensa, ganin yanda Ya Ameenu dasu Ya Habu ke kuka, yasa yaji idanunsa sun cika da ƙwalla, haƙiƙa mutuwa wata abace dake ruguza duk wani farincikin iyali, sannan kuma bata barin wani dan wani yaji daɗi.
Cikin matsanancin tausayawa Dr Adnan yayiwa Baba Malam ɗin ta'aziyyan rasuwar, Ya Habu ne ya miƙe ya fita daga cikin ɗakin, nan cikin kuka ya laluɓo wayarsa daga aljihun rigarsa, number'n Yaa Ahmad ya fara dannawa ƙira.
Ya Ahmad dake zaune afalo shida Aunty Lubna, hakanan yana ganin ƙiran Ya Habu'n yaji zuciyarsa ta tsinke, gabansa ya faɗi, Yana ɗaga wayan kuwa zuciyarsa ta soma bugawa da ƙarfi, sakamakon yanda yaji Ya Habu'n na kuka wiwi.
Cikin matsanancin tashin hankali Ya Ahmad yamiƙe tsaye akiɗime yace.
"Habu lafiya meke faruwa ina Baba Malam?". cikin muryan kuka Ya Habu yace.
"Ya Ahmad, Allah yayiwa Maryam rasuwa!."
Ɗaɓas haka Ya Ahmad ya sulale ya zauna aƙasa, cikin matsanancin tashin hankali da kuma mugun kaɗuwa, take jikinsa ya soma ɓari, inda yaji kunnensa sunyi masa wani irin luuuuuu, sake wayar tasa yayi lokaci guda kuma sai ya fashe da wani irin kuka me sauti, wanda har Ya Habu da bai katse ƙiran ba yana jiyo sautin kukan.
Cikin matsanancin tashin hankali Aunty Lubna tace.
"Lafiya kuwa wani abune ya faru agida? dan Allah meke faruwa?".
Tayi masa tambayar aruÉ—e.
Cikin matsanancin kukan da yakeyi, ya É—ago kansa, ya dubeta, yana kuka sosai yace.
" Lubna Allah yayiwa Maryam rasuwa."
Wani irin hajijiyane taji naneman ɗaukanta, domin maganar tazo mata abazata, durƙushewa tayi kan ƙafafunta, take wasu irin hawaye suka silalo daga cikin idanunta, sai kawai itama ta fashe da kuka, Ya Habu kuwa yana katse ƙiran, Goggo Maryama yaƙira inda ya sanar mata maganan rasuwan, amatuƙar rikice Goggo Maryama tasa masa kuka, jin tana kuka itama yasashi katse wayan, Nan ya dannawa lambar Malam Adam ƙira, bugu biyu kuwa ya ɗauka, jin abun da Ya Habun ke faɗi, yasa Malam Adam, sanya salati, hankalinsa amatuƙar tashe, yace zaizo nan asibitin ya samesu.
Lambar Hajja Inna ya kuma laluɓa, saida wayar ta kusa tsinkewa kafun ta ɗaga, tana shirin masifance sa kan cewa ya dameta da ƙira, jinsa yana kuka yasa cikin matsanancin tashin hankali tace.
"Kai Habu lafiyanka kuwa? me yake faruwa naji kana kuka?"
Cikin matsanancin kuka yace.
"Maryam ne."
Cikin sauri Hajja Inna da ƙirjinta ke bugu tace. "Maryam ne me? Meya sameta."
Zakariyya da Ziyada dake zaune nan falon, tun da Hajja Inna ta fara wayan suka tsura mata ido.
Cikin kukan da yaci ƙarfinsa yace.
"Allah yayi mata rasuwa."
Sa ke wayan Hajja Inna tayi, tare da sulalewa ƙasa.
Cikin sauri Zakariyya ya É—auki wayar ya kara akan kunnensa, jin muryan Ya Habu na kuka, yasa aruÉ—e yace.
"Ya Habu, meya samu Adda Maryam É—in."
Jin muryan Zakariyya yasa, Yaya Habu cewa.
"Maryam ta rasu Zakariyya, Allah ya karɓi rayuwarta." azabure Zakariyya yasoma girgiza kai, lokaci guda kuma wani irin kuka ya ƙwace masa, nan ya durƙushe gaban Hajja Inna dake kuka, shima kukan yasa me tsuma zuciya, fahimtar abun daya faru yasa Ziyada faɗawa jikin Zakariyyan ta rungumesa tana kuka. Hajja Inna, Zakariyya, Ziyada, duka kuka suke, an rasa mai rarrashin wani acikinsu.
Ya Habu kuwa haka ya dinga ƙiran ƴan uwa yana sanar musu da rasuwan, kowa yaji saiya girgiza, saboda Maryam macece abun soyuwa ga kowa, bata banbance kowa natane.

Nan take labarin rasuwar ya kewaya gaba ɗaya cikin danginsu yan uwa da maƙoto, lokaci ɗaya kuwa iyalan familyn suka ruɗe da koke koke.
Saida Ya Habu yagama sanarwa kowa, kafun yake dannawa number'n Mama ƙira, wayar bata wani jima tana ringing ba Mama ta ɗaga, Kukan da taji Habun nayi ne yasa hankalin ta matuƙar tashi, cikin ruɗewa tace.
"Tun safe nakejin gabana na faÉ—uwa, Habu faÉ—amin wani abune ya samu Zaleeha ko?".
Jin abun da ta faɗa yasa Ya Habu sake fashewa da kuka, cikin matsanancin kuka yace. "Mama Maryam ne, Maryam tatafi ta barmu, Maryam tayi nesa damu ta yanda har abada bazamu sake ganinta ba, Mama Allah ya karɓi rayuwar Maryam ɗazun nan, shikenan Mama Maryam tatafi inda bazamu sake ganinta ba...."
Tunda Mama taji yace Maryam ta rasu, shikenan ta daina fahimtan sauran maganganun da yake faɗi, har wayar hannunta ta faɗi kasa batare da ta sani ba, akiɗime ta shiga jujjuya kanta, maganan rasuwan ƴarta ta Maryam ne ke yawo acikin kunnuwanta, ƙafafunta ne sukai mata nauyi, hannu ta ɗaura aka ta saki wani irin fitinannen kuka, wanda yasa Zahira fitowa daga cikin ɗaki da sauri, ganin Maman zaune daɓas aƙasa tana kuka, yasa Zahiran ƙarasowa cikin tashin hankali tace.
"Mama meya faru?." Cikin kuka Mama tace.
"Tarasu Zahira, Maryam ta rasu, tabar mana duniyar."
Wani irin ƙara Zahira tayi take kuma ta faɗi awajen tana kuka.

Can cikin asibiti kuwa Dr. Adnan ne ya nemo ambulance inda aka sanya gawar Maryam aciki.
Da ƙyar Baba Malam ya iya rarrashin Ya Ameenu, sai-dai kuma har yanzu bai-daina kuka ba,
Cikin minti kaÉ—an saiga Malam Adam yazo, zuwan Malam Adam É—in shiya taimaka wajen rarrashin Baba Malam da kuma su Ya Habu da Mamy, suka bar kuka, amma Ya Ameenu kam hawaye sun kasa daina zuba, daga cikin idanunsa.
Malam Adam ne yayi duk wani abun da ya dace, shine ma yasanya Ya Ameenu amota, sannan dukansu suka nufo gida.

Nan gidan nasu kuwa tunkan isowan su tuni ya cika da ƴan uwansu na kusa, nan fa kuka ya dawo sabo, kaitsaye falon Baba Malam aka wuce da gawan, nan kan tiles ɗin falon aka kwantar da ita kudu da arewa tana fuskantar gabas Ya Ameenu ne ya zauna inda yasa gawan agaba ya fashe da wani irin kuka, wanda saida yasa kowa kuka awajen, ganin kukan yayi yawane yasa, Malam Adam ya tara gaba ɗaya jama'an gidan, nan ya bawa kowa alƙur'ani, yace sufara karatu, sannan ayanzu Maryam addu'a take buƙata, bawai kuka ba, nan aka fara karanta mata al'ƙur'ani, Baba Malam ne yasa gawan agaba, yana mata karatun al'ƙur'ani hawaye na tsiyaya daga idanunsa, Ya Ameenu kuwa muryarsa kwata kwata ta daina fita saboda tsabar kuka.

Ɓangaren Ameena kuwa, koda taga tafiyan su Baba Malam gida tare da gawan Adda Maryam ɗin, excuse ta ɗauka, dan batajin zata iya zama, mutuwar Adda Maryam ɗin yasa gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, koda ta fito daga asibitin, adai-dai-ta sahu ta hau, dan bawani iya mota tayi ba, shiyasa bata fitowa da motar da Saifuddeen ɗin ya saya mata wajen aiki, sannan kuma tasani sarai, duk wani abu na ƙarfe ba karɓanta yake yi ba, da ta fara amfani dashi zai lalace, shiyasa ma kawai ta ajiye motar, gudun kada Motar ta mutu da wuri.
Chapter 63 · 0% Book details