← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 154

Sashe 65

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun afaɗan maganganunsa na farko, ta dainajin komai, duk wani abu najikinta tsayawa yayi, wayar hannunta ne ta sulale inda ta faɗi ƙasa, wani irin ƙara ta saki take kuma ta faɗi awajen sumammiya, cikin matsanancin tashin hankali, Aisha tayi kanta tana jijjigata, haɗi da ƙiran sunanta, ihunta da su Elizabet sukaji ne yasasu shigowa aguje, ganin Zaleehan asume yasa Elizabet dafe ƙirji cikin ɗaga murya tace.
"Innalillahi, a madadin tace Oh jesus meya ke faruwa?" Uncle solomon ne ya fita da gudu, bajimawa ya shigo hannunsa riƙe da kofin ruwa, ƙarasowa yayi inda ya ɗan yayyafawa Zaleehan ruwa afuskarta.

Azabure tatashi, cikin wani irin tashin hankali, damƙo Aisha tayi tana me jujjuya kanta, take kuma sai ta fashe da wani irin kuka mai matuƙar tada hankali, cikin kukan take ja da baya, tana me sake girgiza kanta, hankalinta amatuƙar tashe tace.
"Aisha Adda Maryam, Adda Maryam ɗina ta rasu, Adda Maryam tabar duniya batare da na sake sanyata a idanuna ba, wayyo Allah na wayyo ni, kaicon rayuwata, kaicona !!!" Wani irin azababben kuka ta saka kukane mai cushe zuciya da numfashi, lokaci ɗaya ta miƙe tsaye wayarta kawai ta ɗauka tare da buɗe jakanta, kuɗi ta ɗauko wanda batamasan ko nawa bane, takalmi ta zura aƙafafunta, ƙoƙarin fita daga cikin ɗakin take Elizabet ta riƙota cikin kulawa tace.
"Zaleeha ina zakije, dan Allah kitsaya ki nutsu tukun"

FaÉ—awa jikin Aishan tayi tana wani irin kuka, kanta ta girgiza cikin kuka tace.
"Adda Maryam É—ina Uncle Solomo Addana, Adda Maryam É—ina ta rasu"
Hawayen tausayin Zaleehan ne suka kwaranyo daga cikin idanun baki É—ayansu cikin sanyin murya Aisha tace.
"Muje to na rakaki ki hau mota, amma kafun nan ki kimtsa tukunna."
Kai Zaleeha ta girgiza cikin matsanancin kukan dake neman shiÉ—ar da ita ya tafi da rants.
Hannunta Aisha ta kama suka nufi ƙofar fita daga gidan Solo da martasa na biye dasu a baya.
Gaba É—aya Zaleeha bata cikin hayyacinta, hakanne yasa Aisha mannata da jikinta, domin kukan da Zaleehan keyi yasa bata ko iya ganin gabanta.
Suna kawo bakin titi kuwa sukai sa'a nan suka samu wata mota, wanda kaitsaye Gombe zata taho, da kwai ma mutane cike acikinta, Aisha ce tayi mata komai, tasata acikin motar, hannun Zaleehan dake kuka ta kamo, nan ta É—an É—aga mata hannu, itama hawayene ke zuba akan fuskarta, murya asanyaye tace.
"Allah yajiƙanta yasa al'janna tazamo makoma agareta, kiyi haƙuri kinji Zaleeha, dukkan me rai dama mamaci ne, kowa lokacinsa yake jira, dayazo kuma babu jinkiri."
Kai Zaleeha ta jinjina, tare da sakin sabon kuka, nandai Me motar yaja suka tafi, kowa dake cikin motar kallon yanda Zaleeha ke kuka suke, wasu kukan nata ya damesu, wasu kuwa matsanancin tausayinta ne ya kamasu, domin kukan da take irin kukan nanne me karÆ´ar da zuciya, kukan da take, kukane me fitar da irin tsananin tashin hankalin da take ciki, kukane da duk me imani dole zaiji tausayinta.

Littafina na kuɗine in kin gashi yana yawoma na satane, in kina buƙatan saya ga no ɗina 09097853276

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Sbpejg Acan gidan Baba Malam kuwa, kamar yadda Maryam ta buƙata kafun rasuwarta, Ya Ameenu da kuma Baba Malam ne sukayi mata wanka, wanda da ƙƴar suka iya daure zuciyarsu, nan ma Ya Ameenu saida ya durƙushe awajen yayi kuka sosai, har saida yaji numfashinsa na ƙoƙarin cushewa a ƙirjinsa, Baba Malam ma hawaye ne keta tsiyaya daga cikin idanunsa, haka dai suka kammala yi mata wanka, Ya Ameenu ne ya zura mata likkafani, sannan yayi mata duk wani abun daya dace, sosai jikinsa yake rawa, sakamakon kukan da yakeyi, ga wani irin jiri dake neman kadashi.
Bayan sun kimtsa ta ne suka koma gefe suka zauna, dan kuwa da sauran lokaci, ƙarfe goma ne za a sallaceta, yanzu kuwa ƙarfe 9 ne dai-dai.

Can ɓangaren Zaleeha kuwa, tunda ta shiga cikin motar, ta tura kanta tsakankanun cinyoyinta har zuwa yanzu bata ɗago ba, kuka take sosai harsaida numfashinta ya soma ƙoƙarin ɗaukewa, sosai motar tasu ke tsula gudu akan titi, hakanne yasa cikin abun dabai wuce awa uku ba suka iso cikin garin Gombe, nan cikin tashan gombe line aka sauƙe su, zuwa lokacin idanunta sun kunbura sunyi luhu-luhu dasu,
kaitsaye bakin titi ta nufa, wani mai adai-dai ta sahu wato keke napep ne, ya tsaya agabanta tare da ɗan leƙo kansa, cikin kulawa yace. "Ranki ya daɗe tafiya ne?".
Bata iya cewa dashi komai ba, kawai faÉ—awa cikin keke napep É—in tayi, nan ta jingina kanta da jikin keken, kana ta rumtse idanunta, wasu hawaye masu É—umi ne suka silalo daga cikin idanunta, dubanta me adai-dai-ta sahun yayi, cikin yanayi naÉ—an mamakin ganin hawaye akan fuskarta, yace.
"Hajiya ina zamu ne?".
Kasa amsa masa tayi domi , bakinta yayi mata nauyi sosai, batajin bayan kuka zata iya motsa laɓɓanta dan tace wani abu, wayarta dake hannunta ta kunna, cikin text message ta shiga, ataƙaice ta rubuta masa.
"New G.R.A, da kuma layin da zai sauƙe ta."
miƙa masa wayar tayi, amsa yayi ya karanta, yana gama karantawa ya miƙa mata wayar, cikin ransa yace.
"Masha Allah wannan gata kyakkyawa amma kuma da dukkan alama kurmace bata magana, amma dai Allah yayi baiwar kyau anan, ko me yasata kuka kuma oho?" Ganin zancen zucin bazai kaisa ko ina ba, ya sashi tuƙa keken nasa yaja sukai gaba.
Kamar yanda ta rubuta masa arubuce kai tsaye cikin G.R.A ɗin ya nufa da ita, har kuwa cikin layin da tayi masa kwatancen ya kawo ta, gaba ɗaya bata cikin hayyacinta saboda haka batasan da cewa sun iso ba, dawani idanu zata kalli ƴan gidansu? da wani bakin zata basu haƙuri? mezata ce dasu? da wani idanun zata kalli gawan Adda Maryam ɗinta? Da wanne ƙafar zata shiga gidansu da wanne ido zata kalli Baba malam me zata ce mishi?.
waÆ´annan tambayoyin sune abun da suka cika zuciyarta, juyowa me adai-dai-ta sahun yayi, cikin kulawa yace.
"Ranki ya daÉ—e mun iso fa."
Sai alokacin ta buɗe idanunta da suke alumshe, gaba ɗaya kuɗin dake hannunta ta damƙa masa, wanda ita kanta bata masan ko dubu nawa bane, idanunsa ya waro waje, cike da mamaki, dai-dai lokacin ita kuma tafice daga cikin napep ɗin, ƙofar gidan nasu cike yake da jama'a wanda suka fara taruwa danyin sallan jana'iza, tsaye tayi tana kallon tankamemen gidan nasu, lokaci guda kuma wasu hawaye masu tsananin zafi suka fito daga cikin idanunta, da ƙyar take iya jan ƙafanta haka ta nufi cikin gidan, bataji bakuma ta ganin kowa agabanta, hakan yasa tafiya kawai take, sai faman cin tuntuɓe take tayi, amma bata ko kulawa, da wani dutse ta buge har saida babban ƴar yatsar ƙafarta ta fashe, amma koda kaɗanne bata ji zafi ajikinta ba, domin kuwa zafin dake cikin zuciyarta, ya zarce na wannan ciwon, wannanne yasa wasu daga cikin mutanen da suka zo jana'izan suka tsura mata idanu, saboda yanayinta ya gama nuna cewa bata cikin hayyacinta.
Tana jefa ƙafanta acikin gidan taji wani irin abu ya daki zuciyarta, kaitsaye sashin Baba Malam ta nufa, sai faman gauraya hanya take, tana zuwa dai-dai bakin ƙofar shiga falon Zakariyya yazo zai fito sukayi karo da juna, amatuƙar mamakance Zakariyya yasoma ja da baya yana komawa cikin falon, dai-dai lokacin kuwa nan cikin falon Baba Malam ne zaune yana kuka mai tsananin taɓa zuciya, kuka yake sosai wanda hakan yasa gaba ɗaya mutanen falon suma suka fara zubda ƙwalla, cikin kuka murya na rawa Baba Malam ke cewa.
"Ya Allah ka jiƙan Maryam kayi mata rahama,ya Allah ka ƙara mana haƙurin rashinta.
Tabbas mutuwa ta yanke mana ƙauna, mutuwa ta nesantani da ƴata me tsananin biyayya agareni."
Sai ya kuma saki shessheƙan kuka mai cike da ciwo a zuciya murya a disashe yace.
"Inama ina ma da ace mutuwa tana bada zaɓi.
To wallahi dana bata zaɓi ta ɗauki min Zaleeha a doron duniya tabarmin Maryam, dana bata zaɓi ta nesantamin Zaleeha daga wannan duniyar ta barmin Maryam! Da ta ɗauke Zaleeha dana huta da baƙin cikin da take ƙunsamin."
Ya ƙare maganar yana kuka sosai.
WaÉ—annan maganganun sune suka dira acikin kunnuwan Zaleeha, Zakariyya kuwa bakinsa na rawa, cikin É—an É—aga murya yace.
"Adda Zaleeha!." Ƙiran sunan Zaleehan da yayi, shiya sanya gaba ɗaya mutanen falon suka kai dubansu ga ƙofan shigowa, ae kuwa tabbas suka ga Zaleehan ce tsaye, hawaye na shatata akan fuskarta kaman an buɗe famfo, dai-dai lokacin kuwa aka fito da gawar Adda Maryam daga ɗakin Baba Malam, angama kimtsata tsaf saura ai mata sallah kawai akaita makwancinta na gaskiya.
Cikin wani irin gigita Zaleeha ta ɗaga ƙafanta da niyar ƙarasowa cikin falon, Baba Malam ne ya ɗaga mata hannu, alaman dakatarwa, kanta ta shiga jujjuyawa tana kallon gawar Adda Maryam ɗin, take ta saki wani irin firgitaccen kuka mai tsananin ƙarfi, tare da sulalewa anan jikin ƙofan falon, tana wani irin kuka mai tada hankali.
Chapter 65 · 0% Book details