← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 154

Sashe 29

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abu kamar wasa tun ana ƙarfe ɗaya, biyu, uku, har zuwa ƙarfe huɗun yamma babu Zaleeha babu alamarta, sannan daga gidansu ba'a ƙira ance tana can ba, abun da yayi mugun ɗaga hankalin Ummi kenan, nan tatura akayi mata ƙiran Saifuddeen, zuwa yanzu yasake wanka cikin wasu tsadaddun riga da wandon jeans masu kalar navy blue, sosai sukayi masa kyau.
Dubansa Ummi tayi cikin nuna damuwarta afili tace.
"Gabana faÉ—uwa yake Saifuddeen, har yanzu fa Zaleeha bata dawo ba, kuma kace bata sanar dakai fitan ta ba."
Kansa ya jinjinawa Ummin tare da kamo hannunta, cikin kulawa yayi mata alama da body language É—insa, kan cewar.
"Kada ta damu Zaleehan zata dawo ne, wata ƙila tayi nisan zango ne."
Girgiza kai Ummi tayi cikin kulawa tace.
"Bari dai naƙira gidan nasu naji, ace mutum ya fita tun gari bai gama haske ba, kuma ace har yanzu kusan ƙarfe 5 ake nema amma baidawo ba."
Nan Ummi ta ɗauki wayarta, inda ta danna wa number'n Mamy ƙira, don duk gidan number'n mamy kaɗai take dashi.
Bugu biyu aka ɗauki ƙiran, amutunce suka gaisa da Mamyn, cikin nutsuwa Ummi tace.
"Dama cewa zanyi ko Zaleeha na gidan naku ne, tun safe ta fita kuma shine har yanzu munji shiru bata dawo ba."
Gaban Mamy ne ya faɗi, cikin  yanayin mamaki tace.
"Tun safe kuma,  to ina take kenan don dai kam batazo gidan nan ba yau."
Zuciyar Ummi ne ya tsinke cikin muryar damuwa tace.
"Nima fargaba ne ya isheni shiyasa nace kawai bara naƙira na tambaya, indai ko bata gida to ina taje kenan, tunfa gari baigama haske ba ta fice."
Cikin mamaki haÉ—i da fargaba Mamy tace.
"Bakomai ku kwantar da hankalin ku, bari na shiga can ɓangaren mahaifiyarta ta saina tambaya kota zo, sannan zan faɗawa Baban nata ma, duk yanda ake ciki zaku jini."
Nan Ummi tayi mata godiya, daga haka ta aje wayar,  kallon fuskar Ummi kaɗai Saifuddeen yayi, ya fuskanci cewa akwai damuwa.

Mamy kuwa ko aje wayar batayi ba ta nufi ɓangaren Mama, da sallama ɗauke abakinta ta kutsa cikin falon Mama'n, Zaheera dake kwance tana kallo ne ta amsawa Mamy'n, dubanta Mamy tayi tare da cewa.
"Zaheera ina maman taku."
Zaheera bata kai ga cewa komai ba, saiga Mama tafito daga cikin kitchine, duban Mama Mamy tayi cikin nutsuwa tace.
"Halima yanzun mahaifiyar Saifuddeen taƙirani, wai tun safe Zaleeha tabar gida kuma har yanzu bata koma ba, shine take tambaya ko nan tazo, nace da ita a'a, saidai kuma bansani ba ko tazo yau ɗin, naji ma kamar hankalinsu atashe yake, kuma gashi naga bata nan ɗin ma, ina Zaleeha tashiga kenan?."
Mamy ta tambaya cikin yanayin damuwa.

Tsuka Mama tayi tare da turo É—an kwalinta gaba, cikin halin ko inkula tace.
"Wani daga cikin ku yabani ajiyar Zaleeha ne da zakizo kina tambaya ta, ko kuwa idan tazo nan ɗin goyata zanyi abayana na kaita ɗaki na ɓoyeta, kwaje can kunemeta nikam banganta ba!." Mama taƙare maganar tana me yatsuna fuska.
Shiru Mamy tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, ahankali tace.
"Allah ya huci zuciyarki."
Bata jirayi me maman zata ce ba, ta juya tabar falon.
Ƙwafa Mama tayi tare da jijjiga kanta, cikin yanayin mugunta tace.
"Gaba É—ayanku zaku sani ne, kuma ku sani, wallahi Æ´ata tagama zama da nakasashshe ehe."

Daga ɓangaren na Mama kai tsaye Mamy wajen Baba Malam ta nufa, tana shiga kuwa ta iskesa zaune shida Habu da kuma Ameenu, cikin nutsuwa Mamyn ta sanarwa Baba Malam abun dake faruwa, nan take Baba Malam yaji zuciyarsa tayi wani irin bugawa, gyara zamansa yayi tare da fuskantar Mamy'n cikin, nuna damuwa yace.
"Zaleeha bata gidan mijinta kuma, to ina tashiga?."
Rumtse idanunsa yayi, tare da ambatan sunan ALLAH Acikin ransa, haƙiƙa Zaleeha kyautace daga wajen Allah, amma sosai lamuranta ke caza masa ƙwaƙwalwa, sam batajin magana ko kaɗan ta bambanta da Maryam.

Ya Ameenu kuwa wani irin baƙin cikin Zaleehan ne ya turnuƙesa, shikam tun ba yauba ya gane cewa iskanci Zaleehan keji dashi, yayi rantsuwa kuma saiya sauƙe mata, guguwar dake kanta, burinta kullum shine tajawo musu abun faɗa, so take ta ɓata musu suna, ta kuma ɓatawa Baba Malam halin dattakon sa.
Ya Habu ne yace.
"To yanzun ina taje?."
"Sai Allah!." Mamy ta faÉ—a asanyaye.
Nan take Ya Habu ya ɗauki wayarsa, inda yasoma ƙiran ƴan uwansu na kusa ko Zaleehan taje, amma babu wanda yace tazo.
Ya Ameenu ne ya ƙira Maryam awaya inda ya tambayeta ko Zaleehan tazo bayan fitowan sa daga gida, cikin tsananin tashin hankali Maryam tace masa bata zoba.
Baba Malam da kansa ya ɗauki wayarsa inda ya dannawa ƙanwarsa, wato Goggo Maryama ƙira, nan ma cewa tayi sam Zaleehan bata zoba, haka Ya Habu da Ya Ameenu suka dinga ƙiran layukan ƴan uwa da kuma abokai na kusa, waƴanda suke  tsammanin cewa Zaleehan zata iya zuwa, amma babu wanda yace tazo, ko labarinta ma babu wani wanda yace yaji.
Take Ya Ameenu ya danna ƙiran Lambarta, haka wayar tayita ringing har ta katse, no answer, sake dialing yayi, still har ƙiran yasake katsewa ba a ɗauka ba, saida yayi mata 4 missed calls, amma duka no answer, Ya Habu ne shima yaƙira layin nata, nan ma bata ɗauka ba, sau 5 yana ƙira amma shima bata ɗauka, Baba Malam ne dakansa ya laluɓo lambar tata, nan ya danna mata ƙira, saidai shima kamar sauran haka har ya katse no answer,  nan fa akeyinta ran Ya Ameenu idan yakai million to saida ya ɓaci, take yasoma sakin huci, yayin da yakejin wani ɗaci aransa, har wacece Zaleeha da baba Malam zaiyi mata 2 missed call amma bazata ɗaga ba, lallai idan ya kama Zaleeha, saiya rabata gida biyu.
Ganin duk bata ɗauki wayansu bane, yasa Mamy ta ƙirata da layinta, duk dai abu ɗayane bata ɗagawa, nan hankalin Mamy yatashi, take tsoro ya shigeta, nan ta fara tunanin ko Zaleehan bata lafiya ne.
Ya Ameenu ne ya kirata da sabon SIM ɗinsa, inda ya sake dialing number'n Zaleeha'n, shi ɗin ma dai batai picking ba, maida wayarsa cikin alj'ihu yayi, inda ransa ke ƙara tsuma yana ɓaci.

Baba Malam ne ya dubi Ya Ameenu, nan yace.
"Yaje gidan su Saifuddeen É—in, don sanar dasu halin da ake ciki, idan kuma yasamu Zaleehan ta dawo, to ya basa umarni ya tattakata yayi mata duka irin wanda sai ta kasa tashi, sannan kuma ta faÉ—a masa gidan ubanwa taje."

Nan Ya Ameenu ya miƙe, haka ya fita yana huci don cika umarnin Baba Malam ɗin.

Acan gidan su Saifuddeen kuwa, sosai Ummi ta ɗaga hankalinta, tabbas tasan zuwa yanzu rashin dawowan na Zaleeha ba lafiya ba,  ita da Raliya harma da Hayatuddeen gaba ɗaya hankalinsu atashe yake, Adda Rahma wanda itama yanzu zuwanta, jin labarin rashin ganin Zaleeha'n , sosai ya tashi hankalinta.
Saifuddeen kuwa yana zaune afalon, laptop É—insa yake ta dannawa, sam baikula da harkan neman Zaleehan ba domin duk wani motsinta afa tafin hannunshi take yasan muddin ya maida na'urarshi kanta bata da mafakar da zata shiga ya gaza ganewa.

  Zuwan Ya Ameenu ne ya ƙara tada hankalin su Ummi,  nanfa abu kamar wasa ya zama gaske,  sosai aka shiga neman Zaleeha amma kamar ɓatan laya babu ita babu alamanta, Ahmad da Ya Ameenu ne suka shiga mota, inda suka soma zaga gari nemanta, har gidansu Rasheeda da Bilkeesu sunje, amma sun shaida cewa basu ganta ba, nan Ya Ameenu yasa Ahmad dake driving suka nufi family hause ɗinsu, wato gidansu Ya Ameenun kenan, nan ma dai bata nan,  gaba ɗaya ƙanne da yayyan Ya Ameenun saida yaƙirasu ko Zaleehan tazo amma haka suke cewa bata zoba, sosai hankalin familyn ya tashi, Zakariyya da Ziyada kuwa da labarin neman Zaleehan ya iskesu, haka suka shiga damuwa sosai, Hajja kuwa take tasoma kuka, abunka da tsufa, dama kuka baiwa tsofi wahala.

Gaba ɗaya ran Ya Ameenu yasake ɓaci, domin sosai shida Ahmad sukayi buji-buji dasu wajen neman Zaleehan, gashi yanzu har ƙarfe goman dare kenan amma babu ita babu alamanta, still wani abun baƙin cikin kuma shine idan anƙira wayarta bata picking,  koda kuwa za'ai mata ƙira ashirin ne bazata ɗaga ba, wannan dalilin yasa ran Ya Ameenu dana Baba Malam ƙara ɓaci,  can gidan su Saifuddeen kuwa, sosai ɓatan Zaleehan ya ƙiɗima Ummi da su Raliya, Saifuddeen kuwa, ganin yanda hankalin Umminsa ya tashi sosai ne, yasan yashi barin sashin na Ummi gaba ɗaya, part ɗinsu ya koma inda ya kwanta yayi shiru, sosai al'amarin Zaleeha ke ƙona masa rai wani lokaci, sai dai yayi rantsuwa bazai taɓa bari sha'anin haukanta ya damesa ba, wani abu can daban bai damesa ba, saboda haka haukan guduwanta bazai taɓa damunsa ba, yasani koma tana inane to ita takai kanta, sannan kuma ita ta zaɓa, abinda dai ya sani yasa a ransa ta boni da aurensa dan babu saki a tsarin rayuwarsa ta gama guje-gujenta aurensu takalmin kazane mutu ka raba ya rantse wa ransa ko shekara 30 zatayi bata dawoba ba saki ta shiga ukunta dashi dan babu ita babu wanda take cewa tana son.
Chapter 29 · 0% Book details