Sashe 46
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Adda Rahama kuwa jawo ƙofar part ɗin Zaleeha tayi ta kullesa.
Nan ta wuce ɓangaren Ameena.
Afalo ta sameta, tayi jigum ganin Adda Rahaman yasa Ameena sakin murmushi tare da cewa.
"Sannu da zuwa.
É—anmurmushi tayi cikin sakin fuska ta zauna kusa da Aminan,
A hankali tace.
"Ke kaÉ—ai ne ma?."
Da sauri ta gyaÉ—a mata kai tare da cewa.
"Eh ni kadai gidan shiru."
ÆŠan gyara zama tayi kana tace.
"Gsky kam gashi kin saba zuwa aikin nan kuma shiru,
Amman dama Ya Adnan yace in sanar miki shida da Dr Aliyu sun sa an miki transfer zuwa nan F,M,C Gombe, in kin gama hutun bikin dai zakici gaba da zuwa aikinki a nan."
Cikin tsananin jin daÉ—i tace.
"Kai naji daɗi ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi."
Amin Amin Adda Rahma tace kana ta fuskanceta da kyau
cikin kulawa ta ƙira sunanta.
"Ameena." jin yadda ta kiratanne yasa ta
É—ago kai a hankali ta dube ta.
Gyara zama Adda Rahama tayi tare da sanya hannu ta dafa kafaÉ—an Ameenan.
Cikin kulawa tace.
"Ban san irin zaman da kukeyi da É—an uwana ba kuma basai namiki dogon tambaya ko bindiddiba, ko ko nace ki faÉ—amin sirrinku ba."
Shiru ta É—anyi ta zubawa Amina ido,
Ita kuwa Amina shiru tayi a ranta kuwa cewa take ina na ganshi mutumin da guduna yakeyi.
Ganin tayi shirunne yasa Adda Rahma taci gaba da cewa.
"Amma tabbas nasan dacewa, har zuwa yau babu wani abu da ya shiga tsakaninki da Saifuddeen, kiyi haƙuri wani zubin hakanan yake, bai fiye son shiga rayuwar kowa ba, bai shiga harkan mutun kai tsaye, kuma baida saurin sabo,
amma kuma kema ya zama dole kitashi tsaye, ke dai ba ƙaramar yarinya bace Ameena, saboda haka ke zaki zage ki jawosa jikin ki, kada kuma kijira cewa sai yazo, ko ko sai ya miki magana kafun ki amsa masa, a'a koda bai gayyaceki ba kije garesa, sabida ke halaliyanshi ne.
Haka yake duk yadda yake son abu baya nuna kulafashinsa, tunda yake a tsawon rayuwarsa kan abu ɗaya, abu ɗaya tai ya taɓa nuna mana kulafashinsa a kanta.
Tun yana yaro koda wani abin cine duk yadda yake son abin in dai ba an bashi bane bazai taɓa roƙaba ko ya nuna yana so.
Dan haka na roƙeki da Allah kada ki bari kinesanta kanki dashi idan dare yayi, kinsan hanyar da zaki bi wajen jawo hankalinsa, saboda haka wuƙa da nama duka suna hannunki, mu dai kwanciyar hankalinsa da farin cikinsa shine namu, kada ki bari kuna raba makwanci na roƙeki da Allah."
Ta ƙarishe maganar tana mai haɗe hannayenta wuri ɗaya alamun roƙo da neman al'farma.
Kai Ameena ta jinjina cike da gamsuwa sabida itama tana fatan samun kusanci dashi, nan tayiwa Adda Rahaman godiya, sannan suka ɗan taɓa hira, daga haka Adda Rahama ta tafi.
Haka dai Ameena ta wuni yau É—in cike da son dare yayi.
Ƙarfe 9 na dare dai-dai ta gama kimtsa kanta, cikin nutsuwa ta nufi ɓangaren nasa.
Zaune yake akan wheelchair ɗinsa, dagashi sai wani 3 guater jeans da kuma wata fara ƙal ɗin singlet.
Yau ɗin agajiye yakejin kansa hakan yasa shi yunƙurin kwanciya da wuri.
Turo ƙofar ɗakin tayi wanda kuma dama idanunsa na kan ƙofan.
Ganinsa yasanya taji zuciyarta na bugawa da sauri, sannan kwarjinin sa ya cika mata ido, haka dai ta ƙaraso cikin ɗakin, ƙarasowa gabansa tayi inda ta tsaya gefenshi kaɗan.
Dubanta yayi cikin yanayin mamaki, don dai baice yana da buƙatar wani abu ba bare yayi zaton wani abun ta kawo masa.
Hannu ya É—aga mata alaman "Lafiya dai."
Ɗan shagwaɓe fuska tayi tare da yin ƙasa da murya, a shagwaɓe tace.
"Ni dai tsoro nakeji, dana kwanta sai naga kaman abun tsoro zai zo ya kamani."
Idanunsa ya ƙura mata, cike da tsananin mamakin maganar nata, mintuna 3 ya ɗauka yana kallonta, kafun ya sauƙe ajiyar zuciya a ranshi yace anzo wurin tazo zata cinyeni ai na sani wannan harijar ƴarinyar bazata barni in samu salamaba.
cikin body language É—insa yace.
"To yanzu da kikazo nan, nine zan kare miki tsoron ko kuma me?."
Gane abun da yake nufi yasa tasake saka muryar shagwaɓa.
Dubansa tayi tare da cewa.
"Nidai gaskiya anan zan kwana, dan tsoron É—akin can nakeyi."
Duk mgnar da zatayi mishi takan haÉ—a da misalta mishi da yarensu na kurame, dan har yau bata san yana iya fahimtar mgnar mutunba.
Shikam dama ya jima da harbo jirginta, ace duk tsawon kwanaki ukun da tayi bata taɓa jin tsoro ba, sai yau, hmmm.
Taɓe laɓɓansa yayi tare da nuna mata kan gadon, alaman gata ga gadon ae saita kwanta.
Wani irin sanyi taji acikin ranta, saboda ko ba komai zata kwana tana jin sassanyan ƙamshinsa kuma bai koreta kamar yadda ta zataba ko ya nuna mata kyara.
Shi kuwa Saifuddeen sauƙa yayi daga kan wheellchair din inda ya hau kan gadon, abaki bakin gadon ya kwanta, tare da jan bargo yaɗan rufa rabin jikinsa, hannunsa yakai inda ya kashe hasken wutan dake ɗakin, bedsite lamp ya kunna.
Ta daɗe a tsaye jin shiru ya kuma kashe wutan ɗakin ne yasa Ameena ƙarasowa ta hau gadon, can bayansa ta kwanta, inda ta aje kanta bisa lallausan pillown dake ta fitar da ƙamshi.
Lumshe idanunta tayi sakamakon jin yanda ta nutse cikin lallausan katifan, ga kuma wani fitinannen ƙamshi da sanyi me dadi da wani irin azabebben sanyin ɗakin.
Ƙura masa ido tayi tana mejin matsanancin shauƙi na fusgarta, ji take kaman tayi hugging ɗinsa, amma kwarjini da nauyi bazai iya barinta ba.
Shikuwa Saifuddeen baya ya bata, tare da lumshe idanunsa, bacci yakeji sosai, hakan yasa batare da yayi tunanin komai ba bacci ya É—aukesa.
Ameena kam tajima batayi bacci ba, saboda tuni ta faÉ—a wata duniyar ta daban, sosai ta shiga tunani.
Sai wajen 10 na dare kafun bacci ya É—auketa.
Washegari kuwa koda ta tashi bata iskesa cikin É—akin ba, toilet É—insa ta shiga tayi al'wala, sannan tayi sallah, tana idarwa ta kimtsa masa É—akin, sannan ta je ta gaishe da Ummi, kamar kullum ita da Raliya suka haÉ—a kayan break, sannan ta koma sashinta.
Wunin yau ɗin kusan kab ɗinsa da Hayatuddeen suka ƙaresa, kasancewar yau ɗin ba school, sosai kuwa ya ɗebe mata kewa. A nanne ta gane ashe Saifuddeen na iya gane mgnar da mutun keyi muddun yana gani motsin bakin mutun, jin wannan abu yasa wata iriyar kuya ta rufeta,kenan duk abubuwan data faɗa mishi a asibitinsu yana jinta, wannan shine shuka a idon makorwa.
Taso ta ƙoƙƙefe Hayatuddeen taji labarin Zaleeha amman sai ta gane cewa Haytuddeen ɗin wayone dashi kamar dila, wato duk surutunshi yasan abinda yakeyi,
sam yama ƙi bata fuskar suyi mgnar,
Dan da tace mishi.
"Ni kam ina uwar gidan take ne?."
Sai ce mata yayi.
"Nine mijinku?." yayi mata halin É—an Nigeria amsa tambaya da tambaya, haka yasa tayi murmushi tare da cewa
"A a."
daga nan sai ya meda hankalinshi kan wayarshi.
Ita kuwa a ranta take cewa.
"Kaji yaro da iya zaro zance, ashe haka yakeda wayo kamar dila,
wato in ina son ji in tamɓayi mijinmu kenan."
Uhm ta nisa tare da maida hankalinta kan tv.
Yau ma dai da misalin ƙarfe 9 dai-dai, ta kuma kaiwa ɗakinsa ziyara, shidai baice da ita komai ba.
Hasalima yauÉ—in tarigasa bacci, don shi ya jima yana amfani da laptop inda yake aikinsa na sirri, ya daÉ—e yana aikin kafun ya kwanta nan baki bakin gadon.
Yau dai kusan kwana uku kenan da Ameena ke kwana a ɓangaren nasa, sai-dai kuma har kawo yau banda gaisuwa babu wani abun dake haɗasu, haka ma duk da cewa agado ɗaya suke kwana, amma ko ƴar yatsarta bai taɓa taɓawa ba, haka itama...
Kwanci tashi yau dai kwanan Ameena 13 agidan, sosai kuwa tashaƙu dasu Raliya, sannan idan suka haɗu a falon Ummi, sosai suke shan hira da Ahmad, Ishaq da Salisu kuwa suna yiwa ango tsiyar wai ya samu mace kusa dashi yayi bulum buƙui ya dena leƙa kasuwa ko kaɗan. ɓangaren Saifuddeen kuwa har yanzu ba wani sabo atsakaninsu, idan tashiga ɗakinsa kuwa iya kanta bacci, da gari ya waye kuwa tatashi ta fita....
Yau tun da safe taketa kiran Dr Batulu da suke cewa Mommy ta kirata a kalla sau uku dan tana buƙatar ƙarin bayanin yadda masu irin larurar Saifuddeen ke iya mu'amala da mace.
Amman sai ta kasa yiwa Dr batulu tambayar a ƙarshe dai text ta rubuta mata tambayarta,
aiko tana ganin tambayar Amina ta kirata da kanta ta bata duk wani ƙarin bayani.