← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 154

Sashe 125

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Kanta ta shiga jinjina masa, cikin kuka me É—auke da murmushi tace.
"Ya Adnan Kunnuwan Saifuddeen sun buÉ—e, Saifuddeen ya fara jin magana da yin magana." Idanu ÆŠr Adnan ya É—an zaro cikin yanayin mamaki haÉ—i da kaÉ—uwa yace.
"Kinsan me kike faÉ—i kuwa Rahama, Saifuddeen ya fara jin magana fa kikace?". Kanta ta jinjina masa, tare da É—an sharce hawayen farin cikin dake kan fuskarta, cikin farinciki tace.
"Eh Ya Adnan wallahi dagaske yanzu Raleeya ta ƙirani tana kuka take faɗamin".
wani irin matsanancin farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Dr Adan jawo Adda Rahma'n jikinsa yayi tare da rungumeta ƙam, take suka shiga yiwa Allah godiya.
miƙe Ya Adnan ɗin yayi tare da mikar da ita cikin tsantsar jin daɗi yace. "Maza tashi muje gidan Ummi'n, tashi da sauri mu tafi".
cikin farinciki kuwa ta miƙe ɗaki tashiga ta ɗauko mayafinta,
Shi kuwa Ya Adnan miƙewa yayi, zuciyarsa cike da farinciki, ya nufi ɗakinsu Faruq yana shiga ya kamo hannun Farouq da kuma Adam tare da cewa.
"Yaran kirki kuzo mu tafi gidan Ummi".
Cikin Mamaki Faruq ya kalleshi tare da cewa.
"Daddy da sassafen nan".
Kai ya gyaÉ—a mishi tare da cewa.
"Uncle Saifuddeen ne ya worke shi zamuje mu dubi".
Wani irin zabura sukayi a tare tare da cewa.
"Dady ya worke? yana yanaji? kuma yana magana? da tafiya?".
Cikin sauri Ya Adnan yace.
"Ku dai kuzo muje".
aifa tuni sunyi gaba, Adda Rahma kuwa tana fitowa suka É—unguma zuwa mota.

Raleeya kuwa tana jin Adda Rahama ta katse wayan, numbern Raihana ta nema, wayar bata wani jima tana ringing ba, Raihanan ta ɗauka, kaman yanda Raleeya ta sanarwa Adda Rahma muryarta na rawa, haka ma ta sanarwa da Raihana, kusan sumewa Raihana tayi saboda tsananin mamaki da kuma shiga shock, sosai taji abun wani iri acikin kunnuwanta, saboda abune da bazasu taɓa zato ba, duba da irin yanda aka kwashe tsawon shekaru baya ji ba kuma ya magana, kuka ta fashe dashi, dan takasa jurewa bare ita dama saurin kukane da ita,
ji take kaman tayi tsuntsuwa ta ganta acikin garin Gombe, Sameenu dake zaune agefenta, wanda shima yaji komai ne ya jawota ya rungumeta ƙam acikin jikinsa, shi kansa saida idanunsa suka kawo ƙwalla, sosai shima yaji hankalinsa ya taho Gombe, take ya miƙe cikin kula ya janyeta daga jikinshi cikin tsananin farin ciki yace.
"Zauna Ummu Affan, bari yanzu inje airport inda in bincika man in akwai jirgin da zai tafi Gombe, yau ko gobe zamu taho Gombe'n.
Cikin tsananin jin dadi tace to.
Kana ta kuma jawo wayar ta kira Raliya kan zata ce mata ta haɗata da Hammansun taji muryanshi to kuma wayar Raliya sai tana sa mata line busy dole ta haƙura.

Raleeya kuwa suna gama waya da Raihana, numbern Bappa Ali ta dannawa ƙira, yana ɗagawa taji wani sabon kuka yazo mata, saboda jin Bappa Alin suke kaman Babansu mahaifi, hankalin Bappa Ali ne ya tashi sosai, jin yanda muryan Raleeyan ke rawa, cikin nuna damuwarsa yace. "Raleeya lafiyanki kuwa, me yake faruwa? Meya samu gidan?."
Ɗan jan sheshsheƙa tayi murmushi ne kuma yazo mata, cikin zumuɗi tace.
"Bappa Ali kunnuwan Hamma Saifuddeen sun buɗu, yanzu Hamma yanajin magana kuma yana iya mayarwa." amatuƙar ba zata Bappa Ali yaji sauƙar maganan Raleeyan acikin kunnensa, wani irin farinciki ne yaji ya lulluɓe zuciyarsa, irin wanda bai taɓa jiba a rayuwarsaba ko randa aka haifa mishi Dady baiji wannan farin cikinba, Idanunsa ne suka ciko da ƙwalla, jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi, sanyi, cikin ƙarfin guiwan da ya samu kansa aciki, yace. "Alhamdulillah,
Allah abun godiya. Tabbas dama idan da rai to tabbas da rabo, sannan ba acire rai da ni'ima haÉ—i da kyautar Allah, ni dama tun can bancire rai da cewar Saifuddeen bazai sake ji ko magana ba, tunda dama ciwo ne daya sameshi a sama, bawai da shi aka haifesa ba.
Alhamdulillah Raliya mun godewa Allah mai rayawa mai kashewa mai badawa mai hanawa mai cuta da waraka".
Sosai ya nuna farincikin sa akan hakan, har ma yace gashinan zuwa Gombe'n, dan idan ba zuwa Gombe'n yayi ba, kwata-kwata bazaiji zuciyarsa ta gamsu ba.

Suna gama waya da Raleeyan ya shige cikin gida dan ya faÉ—awa Aunty Meena, fuskarsa cike take da fari'a, kallo É—aya zaka masa ka fahimci cewa yana cikin matsanancin farinciki.
Kai tsaye makullin matarshi ya ɗauka wacce Baga daɗe da saya mishi ita kuma hannunshi bai gama faɗawa a tuƙin sosaiba. Kai tsaye unguwar Sirankiyo ya nufa gidan ƙanwarsa Goggo Dada mahaifiyar Ahmad,
koda taji wannan dadɗan labarin da sanyin safiya cewa tayi ƙafarshi ƙafarta da ita zaije.

Acan ɗakin Hayatuddeen kuwa, Ahmad ne ya ƙira Ishaq ya faɗa masa buɗuwan kunnen Saifuddeen ɗin, sosai Ishaq ya shiga shock dajin haka'n, lokaci ɗaya kuwa ya zube akan guiwowinsa inda yayi sujjada, tare da yiwa Allah godiya, sannan ya fashe da kukan farinciki, wanda shi dama yanaji ajikinsa cewa, watarana Allah zai dubi Saifuddeen ya yaye masa koda ɗaya daga cikin larurorinsa, kukan farinciki yayi sosai cikin gida ya shiga ya sanarwa Ummanshi da Babansu sosai sukayi farin cikin wannan labarin inda shima sukayi mishi addu'ar Allah ya yaye mishi tasa larurar shima ɗin.
, take kuma ya miƙe tsaye, waje ya nufa, dan so yake yaji muryan abokin nasa acikin kunnuwansa.

Shi kuwa Saifuddeen har yanzu akwance yake, sai nannauyan nishi yake saki akai akai, dan har zuwa yanzu bayan nasa bai sake ba.
Ummi na fitowa daga sashin nata, sukayi karo da su Adda Rahama, wanda zuwansu kenan. Cikin sauri Adda Rahama ta faÉ—a jikin Ummi tare da sakin kuka mai É—auke da dariya.
Saboda farinciki Ummi ma rungume Adda Rahaman tayi, cikin matsanancin farinciki Adda Rahama'n tace. "Ummi ina Saifuddeen, inason naji muryarsa, ina kuma so yaji magana ta, wanda tsawon shekara 20 kenan da ya daina jinta".
Hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Ummi, hannun Adda Rahman ta kama.
cikin sanyin murya tace. "Zakiga Saifuddeen Rahama, amma yanzu mutafi zuwa ɓangaren Zaleeha, saboda Saifuddeen yace min tariga da ta suma, muje tana buƙatar taimakon mu".
Idanu Adda Rahama taÉ—an zaro atsorace, bakinta na rawa tace. "Subahanalli Ummi me yake faruwa ne?".
ɗai-dai lokacin Dr Adnan ne ya ƙaraso inda suke tsayen, cikin girmamawa ya durƙusa har ƙasa inda ya gaishe da Ummi'n, amsa masa tayi tana murmushi, cikin kulawa dan Ya Adnan kamar Nuruddeen take ganinshi cikin jin daɗin zuwansu tace.
"Yauwa Adnan kaje ciki, Saifuddeen yana ta kukan cewa bayansa na riƙewa ka isa ka duba shi yana ɗakin auta".
Cikin sauri Dr.Adnan É—in yace.
"To." take ya wuce sashin Ummi'n. Ummi kuwa hannun Adda Rahama ta kama suka nufi sashin Saifuddeen, dan dama Saifuddeen din yace mata Zaleehan nacan sashinsa.
Chapter 125 · 0% Book details