Sashe 153
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida sukayi tafiya me nisa, kafun ahankali ya ɗaura ƴan yatsunsa biyu akan wuyanta yana shafawa, akasalance taɗan ɓude idanunta, giransa ɗaya ya ɗaga mata alaman
"Ya dai?." ɗan kwaɓe fuska tayi, cikin sakalci da kuma shagwaɓan daya zame mata jiki tace.
"Na fara jin yunwa." kyawawan Idanunsa ya É—an zaro, cikin yanayin mamaki, dan kuwa ko 30 minute ba'ayi ba, da ta gama cin su biscuits da snacks amma yanzu wai har tana maganan yunwa takeji.
Murmushin daya ƙara bayyana kyakkyawar fuskarsa yayi, ahankali yasa hannu ya ja dogon hancinta, in a body language ɗinsa yace. "To acici kazar birni, ni kam har tsoron wannan yawan cin naki nake, kodai kin zama rumbun gwamnati ne."
Ya ƙare yanayin maganan yana ɗan dariya.
Ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba, mintsininshi tayi tare da cewa.
"Ni ce ma acicin ko? to ai naga koma me kai ka jawo, tunda kaine kasamin yaro me ci acikin, haka kullum sai yata ƙwaƙulana, da zaran naci abinci sai ya kwashe, haka fa nakejin cikina kaman ba komai acikinsa, nidai wallahi kasan yanda zakayi dani ehe."
ta faÉ—i maganar tana me shafa cikin ta, yanayin yanda tayi maganan yasa gaba É—aya alamomin yarinta suka bayyana akan fuskarta.
Jawota jikinsa yayi da kyau, tare da zuba mata ido, acikin jirgin nasu kuwa kowa harkan gabansa yake, kasancewar ba a normal sit suke zaune ba, wajen nasu na musamman ne VIP, ahankali yake É—an goga hancinsa da nata, cikin nutsuwa ya kamo lips É—inta masu taushi, wani irin tsotsa yake mata me kwantar da zuciya, sannu ahankali yake tura mata yawunsa abakinta tana haÉ—iyewa, sosai taji komai ya fara lafa mata, dan tayi imani yawunsa kaÉ—ai sinadari ne ajikinta, kissing É—in juna sukayi sosai sama da 25 minute, saida sukaji suna neman wuce gona da iri, sannan suka tsagaita, lub tayi ajikinsa tana sakin ajiyar zuciya.
Tafiya suka sha asararin samaniya kafun jirginsu ya sauƙa airport ɗin, dake babban birnin Turkey wato _*Sahabi Gokcen International airport Instanbull*_ Yana riƙe da hannunta suka soma sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, wani irin daddaɗan iska da kuma matsanancin sanyi ne ya soma ratsa duk ilahirin jikinta, haka ma Saifuddeen ɗin, saidai baza'a haɗa jin sanyinsa da nata ba, because ita me lafiya ce, shikuwa lafiyar tasa har yanzu da ɗan saura, saidai shima kuma yanajin sanyin. maƙalewa tayi ajikinsa ƙam, tana me ƙarewa yanayin garin kallo, Gari ne wanda ya haɗu sosai komai nasa atsare yake gwanin burgewa ko ina korayen itatuwa ga ruwan dake malale a lugguna da soƙoƙin garin, duk da cewa dare ya ɗan soma yi, hakan baisa mutanen cikin garin sun tsaida hada hadan da sukeyi ba, kowa rayuwarsa yake babu ruwan wani da wani, ganin yanda take ta kakkame jikinta alaman sanyin na shiga jikinta ya sashi tsaida musu me taxi wanda duk na cikin airport ɗin ne, me taxi ɗin da kansa ya sa musu kayansu abayan motan, sannan suka shiga suka zauna, wata ƴar farar takarda ya ciro daga aljihunsa, rubutu yayiwa akan paper'n sannan ya mikawa mai taxi ɗin, karɓan takardan yayi ya karanta, sunan hotel ɗin. _*Swissotel The Bosphorus Luxury Instanbull Hotel*_ ya rubuta masa, hakan kuma na nufin cewa, wannan hotel ɗinne yake so ya kaisu, take kuwa babu ɓata lokaci suka kama hanyar hotel ɗin.
Basu wani jima suna tafiya ba suka iso bakin tangameme kuma haɗaɗɗen hotel ɗin, hotel ne da akayi masa tsari me kyau, komai gwanin burgewa kana a saman ruwa yake. Biyan me taxi ɗin, yayi sannan suka shiga cikin hotel ɗin, daga gefe Zaleeha ta zauna, inda shi kuma ya ƙarasa yayi musu duk wani abun daya dace.
Wani haÉ—aÉ—É—en É—aki ya kama musu, me shegen tsada da kyau, dan ko anan wajensu VIP ne sukafi kama É—akunan dake area'n, wato Very Important People, hannunta ya kama suka nufi É—akin nasu.
Key yasa ya bude ƙofar ɗakin, da addu'a acikin zuciyarsa ya kutsa kansa cikin ɗakin, kana itama ta rufa masa baya, yayin da suka samu kansu acikin haɗaɗɗɗen falo, wani irin sassanyan ƙamshi ne ya daki hancinsu. Cikin mamakin haɗuwan falon Zaleeha tace. "Wow, gaskiya wajen nan ya haɗu, can you imagine seriously ban taɓa tunanin haka wajen nan ya haɗu ba."
yanayin yanda tayi maganan tana ɗan yawo acikin katafaren falon, shi ya sashi sakin murmushi, yasan Zaleeha tanason abubuwan ƙyale-ƙyale, da kuma duk wani abu daya shafi shaƙatawa, shiyasa yayi amfani da hakan, wajen kama musu ɗakin da yasan zai gamsar da ita, burinsa akullum shine ya faranta mata, saboda bayan so da ƙaunarta dake kwance acikin zuciyarsa, akwai tarin tausayinta, shi me rauni ne akanta ƙwarai.
Zaleeha dake ta santin falon nasu, wanda yake ɗauke da two bedrooms acikinsa, sai gefe kaɗan kuma wani haɗaɗɗen dinning area ne, idan ka ƙara gaba kuwa, wani haɗaɗɗen decoration akayi, sannan aka kewaye wajen da wani haɗaɗɗen cottings me shara shara, daka yaye cotting ɗin kuwa, wani haɗaɗɗen swimming pool ne wanda aka masa tsari me kyau, ruwan cikinsa sky blue me masifar ƙamshi. Juyowa tayi ta kalli Saifuddeen ɗin, wanda tun shigowansu idanunsa akanta suke, murmushi tayi masa tare da masa waving fingers ɗinta, cikin son tsokanansa tace.
"Hey Bravo, wannan kallon fa duk na miyene? wato kaga big girl, big ajibo, shine kake neman haukacewa akaina ko, well kacigaba da kallo na, maybe anjima na iya kula ka."
Dariya irin marar sautin nan yayi sosai, dan yasan zallan tsokana ce kawai ke damunta, ƙwafa yayi tare dayi mata alaman cewa.
"Hmmm zan kamaki ne Æ´an mata."
Tagefenta ya raɓa ya nufi ɗaya daga cikin bedroom ɗin falon, ita kuwa Zaleeha tsayawa tayi tana ƙarewa kowani kusurwa dake falon kallo kujerune ɗika-ɗikane suka zagaye da falon sai wani tattausan carpet dake malale a tsakiyar falon da akayiwa daɓe da katakon ƙasashen wajen,
ga wani É—imemen tv a manne wanda kana zaune a gefe ma zakiyi control É—inshi da wayarka,
sai wani ɗan danda mali da akayi aka zagayeshi irin ɗan abun nan da suke hura wuta a ciki dan ɗumama ɗakunan, itakam har acikin zuciyarta wajen yayi mata hundred percent. Saifuddeen kuwa rage kayan jikinsa yayi, sannan ya shige bathroom, shi kansa bathroom ɗin abun kallo ne, dan sun tsarasa sosai yayi kyau, duk da madai duka jikinsa Glass ne, koda ta shigo ɗakin taga bayanan abakin haɗaɗɗen gadon ta zauna, tare da ɗan jingina kanta, numfashi take fitarwa ahankali, dan kowani gaɓa na jikinta ya amsa da sanyin Instanbull, dan idan tana taka ƙafarta ji take kaman tana taka ƙanƙara, aranta tace. "Gaskiya garin nan akwai sanyi, dashi da Mascow ko wanne yafi sanyi oho." Fitowarsa daga cikin toilet ɗinne yasa ta kalleshi, ganin ya nufi gaban mirror yasa itama ta tashi ta shiga toilet din, ruwan zafi ta haɗawa kanta, cikin nutsuwa tayi wanka, wani jibgegen bathrube tasa ajikinta, kasancewar duk da tayi wanka bata daina jin sanyi ba.
Koda ta fito ta samu har ya kimtsa kansa cikin dogon wando da kuma wata jibgegiyar rigan jeans, wayar dake ɗakinne a hannunsa, da alama saƙo yake turawa. Jakar kayanta ta buɗe ta zaro wata doguwar riga me ɗan kauri, duk da tasa kayan, sai faman rawa jikinta yake saboda sanyi, sam bata saba da irin yanayin ba, shiyasa takejin sanyin sosai, amma idan ta zauna agarin na wasu lokuta asannu sanyin zaibi jikinta.
Ƙaton darduma ya shumfuda musu, da hannu yayi mata alaman cewa tazo suyi sallah, babu musu kuwa tasa jibgegen hijab ɗinta, shi ya jasu sallan ƙasaru raka'a bibbiyu, dan lokacin har ma locakin sallan isha ya cika, koda suka idar da sallan, basuyi gaggawan miƙewa ba, saida suka ɗanyi karatun Alƙur'ani, lokacin daya gama karatun yana ƙoƙarin rufe alkur'anin ne, ta kwanto jikinsa, cikin shagwaɓa tace.
"Allah Hamma Saif yunwa nakeji."
Ajiye Alƙur'anin yayi, ya ɗagota, hannunta ya kama, sannan ya hau wheelchair ɗinsa, kallonta yayi cikin body language ɗinsa yace. "Naga alama nanda mintuna kaɗan, idan ban kaiki kin ci abinci ba, ni zaki cinye."
Dariya tayi sosai, tana ƙoƙarin cire hijabin jikinta tace.
"Shikenan ma ai da yaron cikina ya huta, dan nakusanta shi da Babansa."
Murmushi kawai yayi mata, ita kuma wani mayafi ta ɗauka ta yane kanta, hannunta ya kama suka fita daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa suke tafiya har suka iso, wani katafaren Restaurant dake cikin hotel ɗin, Oasis Restaurant kenan, restaurant ne me kyaun gaske dab kusa da ruwa yake haske a wurin tamkar da rana, suna da delicious foods da yawa, kan wani parmanent sit suka zauna. Ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗinne yazo, dan tambayansu abun da suke so, abun da Saifuddeen ɗin ya zaɓa itama shi ta zaɓa, saida suka ci abincin, kafun yasa aka kawo nusu new sim, wanda zasuyi amfani dashi, tun kafun su kammala cin abincin Zaleeha keta kakkame jikinta, saboda sanyin da takeji, shiɗin ma dai yanajin sanyin amma ba sosai ba, hannunta ya kama suka koma ɗakinsu, suna shiga ta faɗa kan luntsumemen gadon, tare da jawo babban blanket ta rufe kanta dashi, shikuwa Saifuddeen ɗayan ɗakin dake cikin falon ya shiga, yana shiga kuwa yayi locked ɗin ƙofar, wayarsa ya ciro tare da dannawa numbern Ummi ƙira, dai dai lokacin kuwa Ummi na zaune afalo, ita da Hayatuddeen, ganin ƙiran Saifuddeen kuma vedio call yasa ta ɗaga cikin sauri.
Sallama ya mata, cike da kewarsu yace.
"I miss you Ummi na." Murmushi Ummi tayi, tare da cewa.
"I miss you too Babana, ya kuke fatan kun sauƙa lafiya."
Kansa yaɗan shafa asakalance yace. "Lafiya ƙalau Ummi, yasu Hayatuddeen."
tun kafun Ummi tace wani abu, Hayatuddeen dake gefe jin an ambaci sunansa ya sashi matsowa jikin Ummi da sauri yanda Saifuddeen É—in zai gansa, cikin zumuÉ—i yace.
"Gani Hamma Lafiyata ƙalau, ina Adda Zaleeha, nasan tana nan tana ta fama da sanyin Instanbull ko." Murmushi Saifuddeen din yayi tare da cewa. "To sarkin surutu, ita ta faɗa maka haka." Dariya sukayi dukansu, ganin baiga Raleeya bane ya sashi cewa "Ummi ina Raleeya?" murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Raleeya tana sama, ko aƙira maka ita ne." Kansa ya girgiza alaman a'a, bama sai anƙirata ba, dama yana son sanin lafiyarta ne.
Hira suka ɗan taɓa da Ummi da kuma Hayatuddeen sannan sukayi sallama.