← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 154

Sashe 95

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali ta ɗan raɓa gefe,
shi kuwa hannu ya miƙo mata alamun ta bashi Adeel ba musu ta miƙa mishi Adeel,
cikin sanyi tace.
"Ina wuni ya aiki?".
Kai ya gyaɗa mata alamun Alhamdulillah, shafa kan Adeel yayi tare da miƙo matashi ya mata alamun.
"Je ki ajiyeshi kiyi salla lokaci yayi kar kije ki tasashi gaba kuyita dariya."
Kai ta jinjina kana a hankali tace.
"Uhum Hamma Saif".
Ido ya zuba mata dan duk duniya ita É—aya yaji tana kiranshi da wannan sunan".
Ganin tayi shirune ya sashi É—aga mata hannu alamun lfy dai ko?
Cikin inda-inda tace.
"Uhum dama gobene za'ayi sadakan bakwai É—in Adda Maryam to kuma ina son zuwa in ka amince ka yerje min?".
Karo na forko kenan da Zaleeha ta nemi izininshi akan abu, shiyasa yaji kanshi tamkar wani sarki,
ita kuwa ganin yayi shirune yasa ta rumtse idanunta da suka cika da hawaye,
Cikin sanyi tace.
"Dan Allah kayi haƙuri, ka bani izinin zuwa inaso inje inga ƴan uwana".
Kanshi ya jinjina mata alamun
"Allah ya kaimu".
Cikin jin daɗi tace Amin Amin kana ta sunkuyo ta karɓi Adeel sannan ta wuce tayi ciki, shi kuma ya wuce ya nufi ƙofar gida.

Amina kuwa dake tsaye bakin falon Ummin ta cika tayi fam tuni sheiÉ—an ya shiga ingizata, sunkuyowan da Zaleeha tayi ta bashi Adeel É—in nan sai takega kamar, sumbatar ta Saifuddeen yayi, hakan kuma sheiÉ—an ya raya mata.
"To ai dai duk iyayinta yau dai kam girkinkine, tunda taci kwana biyunta ai sai ta bar miki mijinki yau kam".
Wani irin kishi da tsanar Zaleeha ne suka cika mata ciki da zuciya.
gaba É—aya ta hautsine a haka ta nufi side É—inta dan yin sallan magriba.

Koda sukaci abincin dere suka É—anyi hira,
ganin yadda Ameena ke watsa mishi harara ya sashi sanin lallai yau akwai aiki,

A can gidan Baba malam kuwa,
Ziyada ne ke zaune gaban Baba Malam a cikin falonshi sai ya Ahmad da Malam Adam , da kuma ya Ameenu,
shiru sukayi baki É—ayansu,
cikin tattausan lafazi Baba Malam ya kira Ziyada.
"Ziyada".
Cikin nitsuwarta irin ta Adda Maryam tace.
"Na'am".
A hankali yace.
"Wata al'farma nake nema a wurinki in Allah yasa kin amince zanji daÉ—in hakan,
Amman fa bawai umarni nake bakiba al'farmace nake nema".
ÆŠago kanta tayi wanda ida nunta tuni sun cika da kwalla cikin sanyin murya tace.
"Baba malam al'farma kuma?".
Kai ya gyaÉ—a mata alamar eh,
da sauri tace.
"A a baba ka bani umarni kawai, ko wanne irine zan bishi domin nasan bazaka sani yin abinda ya saɓawa shariya ba".
Cikin jin daÉ—i ya fuskaceta da kyau, murya a tausashe yace.
"Ga É—an uwanki Ameenu mijin yayarki Maryam, ko zaki amince in aura masa ke in mishi madadin Maryam dake? Kije ki zauna ki raini É—an Æ´ar uwarki?."
Kai ta sunkuyar hawaye na zuba murya na rawa tace.
"Na amince Baba Malam na yarda in dai Ya Ameenu ya amince nima na amince".
Wani irin sassanyan ajiyan zuciya Baba Malam ya sauƙe,
Ya Ameenu kuwa ido ya zuba wa Baba Malam cikin tsananin mamaki da kaÉ—uwa,
Ya Ahmad da Malam Adam kuwa sosai sukaji daÉ—in wannan batun.
Shiru ya Ameenu yayi jin Baba Malam na ce mishi.
"Ameenu ga Ziyada na baka ita, gobe da asuba in sha Allah za'a É—aura muku aure in ka amince ta koma É—akin Æ´ar uwarta".
Kai ya jinjina hawaye na zuba yace.
"Nagode Baba Malam Allah ya saka da al'khairi ya jiƙan Maryam".
Amin Amin sukace baki É—ayansu kana Baba Malam yace Ziyada ta tafi cikin gida.

Nan suka ajiye batun É—aura auren gobe da asuba.

Ƙarfe tara dai-dai Mamy ta shigo falon Mama ta sanar mata kiran Baba Malam, wanda tunda ta dawo gidan bai kulata ba,
Don tuni ya dai-dai ta larin aurenshi da ita.

Jiki a mace ta nufi side É—inshi.
Ganin baya falo ne yasa tayi sallama a bakin ƙofar bedroom ɗin shi,
A hankali yace mata.
" Wa alaikissalam,shigo".
Jiki da zuciyarta cike da kunya da nadama da dana sani ta shigo.
Gefen ta zauna cikin zubda hawaye tace.
"Gani". Ido ya zuba mata domin gaba É—aya ta zama wata jibiri-jibiri ta zama abar tausayi.
kanshi ya kawar tare da cewa.
"Batun auren Ziyada da Ameenu na haÉ—a kuma duk sun amince, gobe da asuba za'a É—aura auren me kikace a kai".
Cikin sanyin murya da nadama tace.
"Allah ya sanya al'khairi ya basu zaman lfy, ya kuma jiƙan Maryam da Rahma".
Cikin mmki da tsananin jin daÉ—i yace.
"Amin Amin,kin amince kenan ba fitina da masifa?".
Cikin jin kunya tace.
"Eh".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"To sai kuma batun yayarki Ruda, bana son zuwanta gidana".
Da sauri tace.
"Nima nace mata bana so".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"To Allah ya kyauta ya shirya min ke".
Amin Amin tace cikin jin kunya,
kana ta miƙa zata fita,
jin ya kamo hannunta ne yasa ta koma gareshi.

Ƙarfe goma duk suka watse kowa yayi side ɗinshi,
Koda ya gama shirin baccinsa, a tsastsaye ya leƙa Zaleeha yayi mata saida safe dan tunima ita ta fara bacci ji shine yasa ta ɗan ɗago ta kalleshi ganin ta zarro mishi ido alamun mmki ne yashi mata alamun ta konta saida safe.
Yana fita ta meda kanta ta konta taci gaba da baccinta.

11 dai-dai Saifuddeen ya shiga É—auki Ameena, hasken wayarshi ya kunna dan tuni ta kashe wutan É—akin dan bata da niyar zuwa É—akinshi.
kan gadon ya hau ya konta tare da sa hannu ya É—auki Adeel ya maidashi kan gadon shi dake kusa da nasun.
Matsowa jikinta yayi tare dasa hannunshin ya juyata suna fuskantar juna.
Da sauri ta sake komawa ta juya ta bashi baya....!

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Ngs,eÉ—É— Sake É—an mirgino ta yayi, tare da sanya hannunsa ya kama waist É—inta, da sauri ta ja baya, tare da É—auke hannunsa daga jikinta, fushi takeyi sosai dashi, saboda haka batajin zata iya biye masa awannan daren.
Asanyaye ya kuma kai hannunsa yana ƙoƙarin cire mata rigar baccin dake jikinta, ƙanƙame jikinta waje ɗaya tayi, tare da riƙe rigartata, fuska ta haɗe sosai tare da ɗan girgiza masa kai alaman bataso. Hannunsa ya zare daga jikinta, tare da zubawa bayanta idanu, dan dama ta bashi baya ne,
shi kam yarasa meke damun Ameenan kwana biyu, yasan duk bai wuce zafin kishi ba.
ÆŠan lumshe idanunsa yayi, tare da gyara kwanciyarsa, cikin ransa yace.
"Bazan taɓa takura miki ba, zanjira harsai kinyi ra'ayi dan kanki." Ameena kuwa ranta ne keta ƙuna, baki kawai take ta cijewa, da ace kuka zaizo mata ma da tayi, ko zata ɗanji salama acikin ranta da zaran ta rufe idonta sai taga lokacin da Zaleeha ta sunkuyo kanshi dan bashi Adeel ita kuwa a zatonta kissing ɗinta yayi.
Suna ahaka bacci ya É—aukesu dukansu. Washegari kuwa da sassafe ta wuce wajen aiki, ko gaisuwa ma, haka tayi masa fuskarta babu wata cikakkekiyar fara'a.
Shidai idanu kawai ya zuba mata, dan yasan fushin nata na babu gaira babu dalili ne.
Zaleeha kuwa ita da Raleeya sukayi komai na breakfast, kusan atare suka yi break fast É—in inbanda Ameena da tatafi wajen aiki.
Suna kammalawa kuwa, Zaleeha ɗaki ta wuce ta kwanta, dan anjima kaɗan ne tafiyarsu gidan Baba Malam. Saifuddeen kuwa anan falon Ummi suka zauna shida su Hayatuddeen yana ƙoƙƙofanshi kan sabon abokinshi da tuni ya dasa mishi ayar tambaya, kuma tuni ya liƙa bincikansa kan wayar ƙanin nashi.
hira sukayi sosai, kasancewar yau ɗin jumma'a ne yasa dukansu ba da wuri zasu fita ba, Hayatuddeen kamma sai kusan ƙarfe 11 yake da lecture, nan ma kafin ƙarfe 2 zai dawo bawai wani jimawa zaiyi ba. Ƙarfe 12 Zaleehan ta dawo sashin Ummi, dan ɗaura abincin rana, zuwa lokacin kuwa su Saifuddeen din basa falon, kowa yayi ɓangarensa, dan shirin masallaci, ita da Raleeya ne sukayi lunch ɗin, sannan suka juye acikin manya manyan food flasks.
Koda suka kammala ɗaƙi ta koma, inda tayi wanka, tare da ɗauro alwala'n sallan azahar tana tunanin zaman gidan na mata yawa da zata samu dai a barta ta koma aikinta, to amman ta inama zata fara maganar.
Chapter 95 · 0% Book details