← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 154

Sashe 126

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gaba ɗaya hankalin Ummi, da kuma na Adda Rahama atashe yake. tun daga falo suka hango ƙofar bedroom ɗin nasa a buɗe,
cikin sauri Ummi ta ƙarasa Adda Rahma na biye da ita, inda suka kutsa kansu cikin ɗakin, hango Zaleehan da sukayi nannaɗe acikin bargo ne, yasasu ƙarasawa cikin ɗakin da sauri.
Hankalin Adda Rahman a tashe ta É—an yaye bargon, tare da É—ago hannun Zaleeha'n, luuu haka taji hannun ya sake, idanu taÉ—an zaro, tare da kai hannunta saitin hancin Zaleeha'n, jin har yanzu bata numfashi yasa hankalinta sake tashi cikin kiÉ—ima ta kalli Ummi data É—an kauda kanta dan surkunta. Atsorace Adda Rahman tace.
"Ummi Zaleeha fa bata numfashi, meya sameta ne?".
Cikin fargaba Ummi ta janye blanket ɗin da Zaleehan ke lulluɓe dashi dan ganin akwai sutura a jikinta, idanunta ne suka sauƙa akan jinin da ya ɓata farin zanin gadon, wanda har aƙafan Zaleehan, akwai ɗigo ɗigon jini da ya bushe ajikin fatarta.
Wani irin matsanancin tausayin Zaleehan ne ya daki zuciyar Ummi, har saida taji ƙwalla sun cika mata ido.
Adda Rahama ma da idanunta suka sauƙa akan jinin dake jikin zanin gadon, ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, tausayin Zaleehan ne ya kamata, cikin sanyi hawaye na tsastsafo mata cikin ƙwayar idonta ta zauna abakin gadon tare da tallafo kan Zaleehan ta ɗaura akan cinyarta, dan dukkansu sun fahimci me ya faru da Zaleeha'n.
Cikin sauri cikin kiɗima Ummi ta wuce toilet, da kanta ta haɗa wa Zaleehan ruwan wanka me zafi acikin bathtube, wanda tasan idan ta shiga zata ɗanji dama dama, saida ta haɗa komai daya dace, sannan ta fito daga cikin toilet ɗin dan tama mance a samu ta farfaɗo yafi dacewa. Haryanzu kuwa Adda Rahama na riƙe da Zaleehan,
ɗan ƙaramin fridgen dake ɗakin, Ummi ta buɗe, tare da ɗauko goran ruwa, dawowa kan gadon tayi ta zauna, hannu tasa taɗan ɗago kan Zaleeha dake cinyar Adda Rahama, buɗe murfin goran tayi, tare da ɗan tsiyayan ruwan ahannunta, ɗan yayyafa ruwan tayi akan fuskar Zaleeha, waiko zata farfaɗo amma shiru, hakanne yasa zuciyar Adda Rahama soma bugu da sauri sauri, saboda tsoro.
Ummi ma kanta ta tsorata da hakan, sai-dai batayi ƙasa a guiwa ba, saida tayi hakan kusan sau uku, kafun taji Zaleehan ta saki wani irin numfashi, tare da sauƙe nannauyan ajiyar zuciya. Ganin ta farfaɗo yasa su Ummi sauƙe ajiyar zuciya.
Ahankali ta shiga ɗan jujjuya kanta, batare da ta buɗe idanunta wanda sukayi nauyi haɗi da kumburi, cikin muryarta da ta dashe wanda ko fita da kyau batayi, amatuƙar wahalce batare da ta dawo cikin hayyacinta ba tace.
"Dan Allah Hamma Saif kayi haƙuri, zafi nakeji zan mutu, wayyo Allah na Hamma Saif kayi haƙuri dan Allah zafi....".
Wani irin kuka ta fashe dashi me tsuma zuciya, still bata buÉ—e idanunta ba.
Matsanancin tausayinta ne ya cika zuciyar Ummi, ahankali cikin sassanyar murya tace.
"Zaleeha, buÉ—e idanunki kinji, ba Hamma Saif É—inki bane nice Umminkune, buÉ—e idanunki kinji."
Jin muryan Ummi acikin kunnuwanta, yasa ahankali taÉ—an soma bude idanunta wanda sukayi dishi-dishi, suka kuma kumbura kaman wanda ta yi sati guda tana kuka.
Ganin Ummi yasa ta faɗa jikinta tare da ƙanƙameta ƙam, sosai ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya dan gani take kamar zai sake zuwa ya danneta. Bayanta Ummi ta soma shafawa, cikin tausayawa tace.
"Ya isa hakanan yi haƙuri ki daina kukan kinji, sannu ko."
Kanta ta shiga girgizawa, dan bazata iya tsaida kukan nata ba, saboda wani irin ciwo da zafi da takeji aƙasanta, ga kuma wani irin zazzafan zazzaɓin da lokaci ɗaya ya sauƙar mata,
Ummi ne ta dubi Adda Rahma, wanda tausayin Zaleehan yasa yanayinta ya sauya, idanunta duk sun kawo ruwa.
Cikin sanyi Ummi tace. "NahaÉ—a mata ruwan wanka, kamata kuje toilet, dan Allah Rahma kiyi mata duk wani abun daya dace duk wani abu da kika san zaki iya yiwa Raliya ko Raihana kiyi mata".
Sai ta kuma kalli Zaleeha cikin tausayawa tace.
"Daure Addanku ta taimaka miki,ki É—auketa kamar Adda Maryam É—inki kinjiko."
Kai Zaleeha ta gyaɗa cikin sanyi da zubda hawaye tayi ƙasa da kanta dan azabar kunyar Ummi da takeji.
Ita kuwa Ummi murya a tausashe tace.
"Bari naje nasa anemo mata magani, dannaji jikinta da zafi kaman wuta."
Kai Adda Rahama ta jinjina, cikin tausayawa ta jawo Zaleehan, da ƙyar ta iya ɗago ta, saboda yanda ta kasa tsayuwa da ƙafafunta, Cikin lallami Adda Rahama ta jata zuwa cikin toilet ɗin dake cikin ɗakin.

Dr Adnan kuwa koda ya isa ɗakin Hayatuddeen, duƙufa yayi akan Saifuddeen wanda zuwa yanzu bayan nasa ya sake riƙewa sosai. Hankalin Dr Adnan ne ya tashi saboda yanda yaga jikin Saifuddeen ɗin, ya sake ɗaukan zafi. Hayatuddeen kuwa ganin Dr Adnan yazo ya sa ya tashi ya fita daga ɗakin, zuciyarsa cike da murna ya ciro wayarsa daga cikin aljihu, inda ya dannawa numbern Zakariyya ƙira. Wayar bata wani jima tana ringing ba Zakariyya ya ɗauka.
Murmushi Hayatuddeen yayi, cikin jin daÉ—i yace. "Zakariyya kunnuwan Hammana sun buÉ—u, Hammana ya warke daga cutar kurumta Zakariyya".
Jin maganan Hayatuddeen ɗin yasa jikin Zakariyya ya ɗauki rawa, samun kansa yayi cikin wani irin farin ciki, dan sosai abun ya taɓa zuciyarsa, cikin matsanancin farinciki yace.
"Masha Allah Alhamdulillah, Hayatuddeen yanzu Hamma Saifuddeen najin magana kenan?" Cikin matsanancin farinciki Hayatuddeen yace.
"Eh Zakariyya, ni narasa inda zansa kaina ma saboda farinciki, yanzu Hammana ya zama kaman kowa, saidai kuma dan Allah kada ka faÉ—awa kowa hakan, dan Hamma Saifuddeen da kansa yace bayason Adda Zaleeha ta sani, wanda kuma bansan menene dalilinsa nayin hakan ba."
Kai Zakariyya ya jinjina, cikin tsananin jin daÉ—i yace.
"Insha Allah bazan faÉ—a mata ba Hayatuddeen, anjima kaÉ—an nima zanzo, bazan iya jurewa ba Hayatuddeen zanzo naga Hamma na kuma ji muryarsa."
Kai Hayatuddeen ya jinjina, tare da cewa. "Shikenan Zakariyya sai kazo, saidai kuma tun É—azu Hamma Saifuddeen ke cewa bayansa nayi masa ciwo, amma yanzu Ya Adnan yazo yana dubashi."
Cike da zumuÉ—i Zakariyya yace. "Ganinan zuwa Hayatuddeen, kuma insha Allah komai zai dai-da-ita."

Acan sashin Saifuddeen kuwa, Ummi naganin shigansu cikin toilet, ta fita daga cikin ɗakin, saboda tanaso taje ta duba Saifuddeen. Adda Rahama kuwa cikin kulawa haɗi da lallami tace da Zaleeha ta cire kayan jikinta, tare da miƙo mata towel tace ta ɗaura kana ta juya mata baya dan kauda idonta kanta, da ƙyar ta iya cire kayan nata, sannan ta ɗaura towel ɗin cikin hikima yadda bata tsaya ba komai a jikinta ba.
Da ƙyar Adda Rahama ta iya zaunar da ita acikin ruwan zafi'n, wani irin narkekken ƙara ta sake, saboda yanda taji ƙasanta na mata zafi da raɗaɗi kaman an watsa mata barkono, kuka ta saka tana ɗan yayyarfa hannunta.
Cike da tausayinta Adda Rahama tace "Sannu ko kiyi haƙuri kinji, idan ruwan ya gama ratsaki, insha Allah zaki ɗanji sauƙi."
Asakalce ta ɗan jinjina kanta, duk da zafin da takeji haka ta ɗan daure ruwan ɗumin ya ratsa cikin jikinta, saida ruwan yaɗan fara salancewa, sannan Adda Rahama ta sake zuba mata wani ruwan me ɗumi, tana sake shiga ruwan kuwa gumi ya fara fesowa daga jikinta, taji zafi sosai saidai bakaman na farko ba. Saida Adda Rahama tasa mata ruwan ɗumi sau uku, sannan ta fita inda tace mata taɗan ƙoƙarta tayi wanka tsarki.
Chapter 126 · 0% Book details