← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 154

Sashe 118

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Da sallama abakinta ta shiga falon, Hayatuddeen dake zaune ne ya amsa mata, ƙarasowa cikin falon tayi, tare da dubansa cikin kulawa tace.
"Auta har yanzu bakayi bacci ba."
Kansa ya jinjina mata, tare da cewa.
"Wani latest film nake kallo Adda Zaleeha, yayi kyau sosai."
Murmushi tayi, tare da ƙarasawa kan kujeran da ta zauna ɗazu, tana ɗage pillown dake jikin kujeran kuwa, taga wayarta, ɗaukan wayar tayi, dai-dai lokacin Ummi ta fito daga cikin ɗaki. Ganin Zaleeha yasa tace. "Ikon Allah Zaleeha dama baki shiga bane." Ɗan murmushi tayi tare da cewa.
"A'a Ummi na shiga, harma na kwantama saina tuna nabar wayata shine na dawo na É—auka." Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Ai kuwa naji daÉ—in dawowanki, dama yanzu Hamman ku ya turo min text wai Hayatuddeen ya kai masa coffee, tunda gaki ai shikenan, shiga kitchine ki haÉ—a masa saiki kai masa ko." Kanta taÉ—an sunkuyar cikin yanayi na É—an jin kunya tace.
"To Ummi." kitchine ta wuce, inda Ummi kuma ta zauna anan falon. haɗaɗɗen coffee ta haɗa masa, wanda lokaci ɗaya ya cika falon da ƙamshi, fitowa tayi daga kitchine ɗin, hannunta ɗauke da ɗan tray wanda samansa ke ɗauke da ɗan ƙaramin flask da kuma cup, saida safe tayiwa su Ummin, sannan ta fice daga cikin ɗakin. Koda ta doshi sashin nasa, hakanan taji ƙirjinta na bugawa, wani irin fargaba ta samu kanta aciki, ɗan dakewa tayi tare da murɗa handle ɗin kofar falon nasa ta shiga.
Komai dake cikin falon nead, babu abun dake tashi sai ƙamshi, da kuma wani irin fitinannen sanyin ac mai ratsa sassan jiki da zuciya, ɗan Adam lumshe idanunta tayi, ahankali take ƙarewa falon nasa kallo, komai na cikinsa me kyau da burgewa ne, musamman royal chairs din da suka matuƙar burgeta, ɗan waige-waige ta somayi, ganin baya cikin falon yasa taɗan turo ƙaramin bakinta gaba, ashagwaɓe tace.
"To kuma ina yake?." ƙoƙarin aje tray ɗin dake hannunta tayi, wani tunani dayazo ranta ne, yasa ta juya tare da nufar ƙofar bedroom ɗinsa, sanin cewar idan ta ajiye masa coffee ɗin afalo, balallaine ya gani ba, maybe kuma yasake ƙiran Ummi yace akawo masa coffee, bata so kuma Ummi tayi zaton bata kai mishiba ne. ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga, bakinta ɗauke da sallama, daddaɗan ƙamshin airfreshener ne ya daki hancinta da wani shegen sanyin ac daya ninka na falo, cikin ranta tace.
"Na shiga uku wannan sanyin baya damunshi ne, haba shiyasa ko matarsa mutun ya shiga sai kaji sanyi har cikin Æ´aÆ´an hanjinka, Allah sarki Sule shi kam har ya saba,
da makaken gadonsa ta fara arba, É—an zaro idanunta waje tayi, abayyane tace.
"Wow, wannan wani irin gado ne?".
Tsayawa tayi tana me ƙarewa ɗakin nasa kallo, cikin ranta tace.
"Chab aljannar duniya kenan mutun komanshi kamar na É—awisu".
ɗan takowa tayi a hankali ta ƙaraso jikin gadon nasa, ahankali tasanya hannu taɗan shafa saman gadon, wanda design ɗinsa yayi matuƙar kyau.
Sam ta shagala cewar coffee ta kawo masa, hasali ma kuma rashin ganinsa aÉ—akin baida meta ba sai dai tanajin sanyi sweet É—inta dake cikin tafin hannunta.
Chapter 118 · 0% Book details