← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 154

Sashe 6

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Ashiru ne yace. "Ƙwarai kuwa, ayanzu dai fatan al'khairi da sa al'barka kawai suke buƙata daga garemu."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayin ƙasa da kanta, sosai taji zuciyarta tayi mata nauyi, yayinda matsanancin rauni ya bayyana acikin idanunta, haƙiƙa ita abu ɗaya take gujewa Saifuddeen shine halin dazai faɗa bayan aurensa da Zaleeha, matuƙar bata sanja hali ba, tasan Saifuddeen bazaiji daɗin zaman auren ba, wanda ita kuma duk wani fata da burinta baiwuce Saifuddeen ɗinta ya samu mace tagari, mai share hawayensa.
Hawayen dake ƙoƙarin cika idanunta ta shanye tare da ɗan sakin murmushi, cikin sanyi tace.
"Babu komai, duk yanda kukace shikenan, dama ni baƙin Zaleeha nake ba kawai dai munanan kalamai da ƙudurinta akan Saifuddeen shine ke bani tsoro, amma zantayi musu addu'a Allah yasa auren yazama alkhairi, wanda kowa zai amfana dashi!."
Cikin jin daɗin sauƙin kai irin na Ummin dukansu suka amsa da "Ameen Ameen."
Nan Dirankadi yace acigaba da shirye shiryen biki kada afasa komai da akayi niya, baiwani jima agidan ba yashiga motarsa inda ya nufi gida, su kuwa su Baffa Ali can cikin BQ suka sauƙa, saboda dare yayi babu yiyuwar komawarsu Dukku aranan, saidai gobe da safe zasu kama hanya.

Jin ƙiran da Baban nata keyi mata yasanya taji gabanta ya faɗi, take tsoro ya shigeta saidai kuma babu yanda ta iya dolenta ta amsa ƙiran nasa, zumbuleliyar hijab ɗinta ta zura, kana tanufi ɓangaren mahaifin nasu.
Da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon,   cikin sanyi Baba Malam ya amsa mata,   ƙarasowa tayi inda ta zauna akan lallausan carpet ɗin dake malale bisa tsakiyan falon, duƙunƙune jikinta tayi acikin hijabin, cikin ƴar siririyar muryarta dake rawa tace.
"Barka da dare Baba Malam!."
Kansa kawai ya jinjina mata alamar "Yauwa."
Aƙalla ta ɗau sama da mintuna 5 baice da ita komai ba, nanfa bugawar zuciyarta ya tsananta, don amatuƙar tsorace take.
Gyara zama Baba Malam yayi tare da fuskantar ta,  cikin kulawa yaƙira sunanta.
ÆŠagowa tayi ta kalleshi tare da amsa masa murya na rawa jiki asanyaye.
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da yi mata duban tsab, cikin son tausasa lafuzansa agareta dan yi mta nasihar da wala Allah imaninta zai sabunta cikin kula yace.
"Haƙiƙa kowani uba yana al'fahari da ƴarsa ko ɗansa matuƙar sukayi masa biyayya,."
Sosai lafazinshi ya ratsa jikinta,
Shi kuwa cigaba yayi da cewa.
  "Bazance bana al'fahari dake ba Zaleeha saboda ke jininace, sannan kuma ko ba komai kin amshi zaɓin dana baki, kin kuma yi na am, saidai kuma labari yazo kunnena akan cewar kina rubuta saƙo irin na ɓaƙaƙen maganganu da kuma gargaɗi da barazana da kisan kai kina turawa Saifuddeen".
Tuni jikinta yake tsuma.
  "Kada ki watsamin ƙasa a ido Zaleeha! Dan in kikamin haka ,wallahi Allah zan barranta dake, kada kimin fuska biyu.
tabbas nasan cewa rashin sanin wanene Saifuddeen agareki shiyasa kike wulaƙantasa, yanunamiki ƙauna da gata tun kina ƴar ƙanƙanuwan yarinya, haka kuma har kawo yanzu bai janye ƙaunarsa daga gareki ba,  Saifuddeen maganarci ne wanda nayi imani samun kamarsa nada matuƙar wahala, ba'akowani gida ne ake haihuwar irin Saifuddeen ba haka kuma irinsu basu da yawa acikin al'umma, nazaɓa miki Saifuddeen amatsayin mijine saboda nasan bazaki taɓa danasanin aurensa ba, Saifuddeen bazai barki kiyi baƙinciki ba Zaleeha."
Tuni hawaye ke kwaranyo mata a ranta take faÉ—in.
"Wannan musakin wanne farin ciki zai samar min,mutun da bashi da bakin da zai furta min kalaman so, mutumin dake kamar dutse duk daÉ—in kalmar da zan masa ba ji zaiba,
haka zan rayu dashi babu so bare soyayya da ƙauna! muryar baban natane ya katse mata hasashenta. "Zaleeha kina ganin nakasasshe ne ko, to Saifuddeen da kike gani shi zai zame miki GARKUWA sannan bongo majingina na rayuwarki,  shin Zaleeha menene aibun Saifuddeen dan yakasance Nakasashshe? saboda shi nakasashshene shiyasa kawai kike gudunsa? Baki san cewa Nakasa Ba Kasawa Bace Zaleeha, kuma babu nakasasshe sai kasasshe musamman nakasa irin ta Saifuddeen da bata shafi lafiyarsa ba, sannan nakasar zuci itace nakasa ba wai ta gangar jiki ba,  Saifuddeen yana da kyakkyawar zuciya, kyawawan ɗabi'u, kyawawan halayya, ga  wadatan zuci  duk ya haɗa in kuma kyau ne tako ina Allah ya mishi kyau da haiba, haƙiƙa amatsayina na uba mahaifinki, ina matuƙar yi miki kwaɗayin samun managarcin miji kamar Saifuddeen, sanin cewa miƙa aurenki ga Saifuddeen danayi bazaisa nayi dana sani ba, shiya zuciyata ta aminta da shi sosai,  dan Allah Zaleeha, ki nutsu ki dawo cikin hankalinki, ki watsar da duk wani buri ki rungumi auren Saifuddeen amatsayin ƙaddarar rayuwarki,  kin kuma san idan kikayi haka Allah bazai bari ki taɓe ba,  ni mahaifinki ne Zaleeha, idan ban nusar dake ba, babu wani wanda zai nusar dake, saboda haka maganan tura ɓaƙaƙen maganganu ga Saifuddeen banasonshi dan Allah ki daina kinji ko Mamana?."
A hankali ta gyaɗa kanta alamar to yayinda cikin zuciyarta kamar ta mutu dan baƙin ciki.
"Saura ƴan kwanaki kaɗan yazamanto miji agareki saboda haka yazama dole ki girmamasa kamar yanda kike girmamani harma fiye da haka domin shi mijinki ne kuma al'jannarki tana ƙarkashi diga-diginshi ,sai ya ɗaga zaki shiga".
A ranta take cewa.
"Wannan gurgun kam ai ɗaga ƙafarma ba iyawa zaiba." hannu tasa tana share hawayenta jin Baba malam ɗiɓ yaci gaba da cewa. "Saboda matsayinsa na miji agareki yazama dole kiyi masa biyayya da ɗa'a, koda wasa kada kice zaki bijirewa umarninsa, ƙin bin umarninsa tamkar saɓawa Allah Ne saboda haka ki kiyaye!."

Tuni hawaye sun wanke fuskar Zaleeha, sosai zuciyarta keyi mata ƙuna so take tasaki kuka mai sauti, hakan yasa tasanya hannuwanta duka biyu ta toshe bakinta, gudun kada kukan ya fito, kai kawai taketa gyaɗawa kamar Ƙadangaruwa.
Ganin haka yasa Baba Malam cewa.
"Tashi kije, sannan koda wasa kada ki taɓa mantawa da maganganu na, domin kuwa idan akace yau bana raye babu wani wanda zai faɗamiki makamancinsu." still kai ta gyaɗan
Da sauri ta-tashi ta fice daga cikin falon, tana rufo ƙofar falon tashiga tafiya cikin yanayi na gudu-gudu sauri-sauri, koda ta shiga falo, tsaye ta samu Mama tanata kaiwa da komowa,  Mama naganin Zaleehan tayo kanta, cike dason tambayarta me Baba Malam ɗin yace mata, saidai me tuni Zaleeha ta shiga ɗakinta inda ta rufo ƙofar tare da murza mata key, sulalewa tayi ajikin ƙofar tare da sakin kuka mai sauti,   galala haka Mama tasaki baki tana kallon ƙofar ɗakin Zaleehan, kana daga inda take tsaye tanajiyo sautin kukan da  Zaleehan keyi, rantane yayi matuƙar ɓaci, domin tasan babu wani abu dazaisa Zaleeha kuka haka, idan ba maganar auren wancan nakasashshen ba, gashi tanaji tana gani aka kwashi kayan Abdussalam aka meda, tsuka tayi cike da baƙin ciki haɗi da takaici ta wuce ɗakinta.
Kuka sosai Zaleeha tayi harsaida muryarta ta dashe, lokaci guda wani irin zazzafan ciwon kai ya kawo mata ziyara, gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta toshe harta rasa ma tunanin me zatayi, kullum kwanan duniya soyayyarsa ne keyi mata tsaye acikin rai da zuciyarta, sannan gefe guda kuwa ga yanda rayuwa keneman juya mata baya, tahanyar haɗa ta aure da wani wanda takejin tsanarsa acikin zuciyarta fiye da kowa.
Da ƙyar ta iya tashi daga jikin ƙofar, haka ta nufi bathroom, ko gani sosai bata iyawa saboda yanda idanunta suka kumbura sukayi luhu-luhu dasu,  wanke fuskarta tayi tare da dawowa ta kwanta luf akan lallausan gadonta,  sosai kanta ke ciwo kamar zai rabe gida biyu haka takeji, gawani irin zazzaɓi daya sauƙar mata, babban blanket ta jawo tare da rufe jikinta, kanta ta tura acikin pillow, sannu ahankali take fitar da sheshsheƙan kuka, cikin haka wani bacci wanda sam batayishi cikin daɗin rai ba yazo ya ɗauketa.
**

Yau ya kama saura kwana biyu biki, inda ake ta hidima haɗi da shirye-shirye daga ɓangarori guda biyun,  gidan su Saifuddeen sosai ake hidima inda tuni ƴan uwansu dake nesa sun zo, nanfa shirin biki ya ƙara armishi, ɓangaren Ango Saifuddeen da abokansa kuwa sunshiga busy sosai, babuma kamar yashi Saifuddeen, gaba ɗaya yanzu bashida wani lokaci koda na hutawa ne, yadage tuƙuru wajen ganin yaƙawata bikin nasa, inda yaketa ɓarnatar da kuɗi wajen ganin ya ƙawatar da kansa da kuma amaryarsa,  gudumawa yake samu sosai takota ina, wanda abun har mamaki yake bashi, sam shi baison mutane suna wahalar da kansu akanshi, musamman ma akan auren nasa yafiso yayi komai da kanshi, haka ƙungiyarsu ta Jonapwd ma ta basa gudumawarta mai tarin yawa, wanda bisa dole ya amsa, don ƙa'idar ƙungiyanne dazaran abu ya samu mutum na hidima, walau farin ciki walau akasinsa, to fa saisun bada nasu taimakon suma.

Birnin gombe da kewaye duk sun cika sun ɗauka batun auren Zaleeha da Saifuddeen wanda aketa tallashi a dukkan gidajen Radio kama daganan FM Gombe, PROGRESS, RAYPOWER, AMANA uwa uba, vision FM gidan radio su Zaleeha, yan uwa ƙawaye maƙota ,duk anji labari, Bilkeesu kuwa da gangan ta sanarwa duniya mijin da Zaleeha zata aura nakasasshe ne, wannan abun ya ƙara tada hankalin Zaleeha.
Rashida kuwa tuni ta gayyato ƙawayensu baki ɗaya harda waɗanda sukayi aure, haiƙan gadaran suketa shiryawa bikin ita da sauran ƙawayen nasu.

Kamar yanda ake ta shirye shirye shiryen biki agidan nasu Saifuddeen cike da farin ciki, aɓangaren gidansu Zaleeha kuwa abun ya banbanta, domin kuwa Baba Malam da Mamy haɗi da su Ya Ahmad ne kaɗai suke shirin auren, sai kuma Mamy wanda tazama kamar itace uwar amarya, don Mama kam fir tamaƙi zama agidan hakanan ta tsiro da tafiya garinsu, tayi hakanne kuma don bazata iya juran tarin baƙin cikin dake tunkarota ba, sam Baba Malam baihanata ba, dan yasan hanatan ma wani babban bala'i zai zama, kuma tama tafi ta basu fili ayi komai ba fitina, shiyasan tunda Mamy nanan bai da muwa da tafiyar Mama.
Ita kuwa Mama bazama tayi gidan bokayenta.
Chapter 6 · 0% Book details