← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 154

Sashe 62

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sbpejy Su Baba Malam kuwa tsayuwa sukayi, gaba ɗaya jikinsu asanyaye y'ake, babu wanda yayi yunƙurin zama acikinsu, Mamy kuwa hawaye take ta sharewa, zuciyarta cike take da tausayin Maryam.
Can cikin theater room kuwa, alluran nan dake gusar da hankali, likitotin sukayiwa Adda Maryam, Doctors kusan guda huɗu ne suka duƙufa akanta, cikin ƙwarewa kuwa suka soma yi mata aiki.
Shiru É—akin theater'n yayi bakajin motsin komai, sai na kayayyakin aikin da likitotin ke amfani dasu.
Sosai aikin nasu ya ɗauko nisa, gefe kuwa Ameena ne da wata nurse wanda sune ke taimakawa wajen miƙawa doctors ɗin kayan aiki.
Ahankali ƙwayar idanunta ke tsiyayar da wasu sassanyan hawaye, sosai kuma hawaye suka rinƙa kwaranyowa daga cikin idanunta, Ameena wanda gaba ɗaya hankalinta naga Maryam din ne, ganin idanun Maryam ɗin na zubda hawaye, yasa amatuƙar firgice ta matso kusa da ɗaya daga cikin doctors ɗin dake yi mata aiki'n, ɗan taɓasa tayi yana juyowa kuwa tayi masa nuni da fuskar Maryam, cikin yanayin tsoro haɗi da mamakin ikon Allah likitan yayiwa ƴan uwansa nuni da Maryam ɗin, wanda idanunta suke ta zubda hawaye, koda suma suka ga yanda Maryam ɗin take , sosai suka shiga shock, saboda sunsan sunyi mata alluran gusar da hankali masu ƙarfi, wanda baiyiwuwa ma ta farfaɗo koda nan da awa 2 ne, sai gashi abun mamaki ko mintuna 30 ba acika ba idanunta na zubda hawaye kamar dai kuka takeyi mamakin hakanne yakamasu ƙwarai, saboda koda jinin mutum nada ƙarfi, idan akayi masa wannan alluran yana tasiri sosai ajikinsa, ɗaya daga cikin doctors ɗinne ya sake haɗa wani alluran yayi mata, bayan ya mata alluran da kamar mintuna uku ne, suka ga idanunta sunyi lib sun dena ɗan motsawan da sukeyi saidai kuma har yanzu hawaye na fita daga cikin idanunta, yana bi ta cikin kunnenta, kana yana sauƙa akan matashin kanta.
Sosai abun ya ɗaure musu kai, dan kuwa basu taɓa samun irin haka a cikin aikin su ba, nan dai suka maida hankalinsu wajen ciro yaron dake cikin nata.
Cikin ikon Allah kuwa suka fito da santalelen yaro, saidai kuma yariga daya rasu, tun jiya shiyasa ma haihuwar ta gagara, ya zama sai an mata tiyata, ɗayar nurse ɗin da suke aiki tare da Ameena suka miƙawa yaron, sannan suka duƙufa wajen ɗinke ta, cikin mintuna kaɗan suka gama yi mata duk wani abun daya dace cikin iya da kwarewa da sanin makaman aikinsu.
ÆŠaya daga cikin doctors É—inne yayiwa su Ameena alama kan cewa su fita da ita, zuwa É—akin hutu.
Hakan kuwa akayi, inda Ameena da wannan nurse din suka turo gadon da Adda Maryan É—in ke kai.
Gaba É—aya jikin Ameena yayi sanyi, tausayin maryam É—inne ya cika zuciyarta, tana tausayin halin da Maryam din zata shiga, idan ta tashi, taji cewa yaron nata baizo da rai ba, tasan tabbas zata shiga damuwa.
Haka dai suka turo gadon, inda suka fito daga theater room É—in, direct É—akin da zasu kaita dan hutuwa suka nufa, wanda yazama kuma dole sai sun wuce ta gaban su Baba Malam, kasancewar su Baba Malam É—in sunyi kusa da É—akin theater'n.
Dab da sun kusa ƙarasowa wajen su Baba Malam ɗinne, Maryam ta bude idanunta a hankali lokaci guda kuwa hankalinta ya dawo jikinta, ahankali ta buɗe idanunta, cikin wata irin murya me sanyi, da kuma yanayin mayen jinya taƙira sunan.
"Baba Malam!!."
Al'amarin daya sanya su Baba Malam ɗago kansu kenan, dan dukansu kansu aƙasa yake, basu ma lura da fitowar su daga ɗakin theater'n ba, cikin hanzari su Baba Malam suka nufo ta, da sauri ɗayar nurse ɗin ta dakatar dasu, cikin sauri tashiga tura gadon, don ba aso kowa yaje kan wanda akaiwa theater sai bayan mutum ya huta tukun, Ameena kuwa cikin sauri haɗi da tashin hankali tanufi office ɗin babban doctor ɗinsu, hankalinta amatuƙar tashe yake, domin farfaɗowan Adda Maryam ɗin akaro na biyu, zai iya zama hatsari.
Maryam kuwa a hankali ta samu ta É—aga Æ´an yatsunta cikin wata dashashshiyar murya tace.
"Yaya Ameenu kazo, kazo kada su hanaka zuwa Yaya Ameenu mutuwa zanyi."
Dai-dai lokacin kuma nurse ɗin ta shige da ita wani ɗaki, cikin matsanancin sauri Ya Ameenu yazo dan bin bayan matarsa, wata nurse ce ta taresa dan ba'a shiga kai tsaye, sai an baka izini, cikin wani irin gigita Ya Ameenu ya daka mata tsawa, ransa amatuƙar ɓace hankali a tashe yace. "Matatace fa, tana ƙirana kuma kuce bazan je ba." Hannu yasa ya ture nurse ɗin gefe, nan ya faɗa cikin ɗakin su Baba Malam suka rufa masa baya.
Yana shiga cikin sauri ya ƙarasa jikin gadon, Adda Maryam kuwa da hawaye ke zuba daga cikin idanunta hannunsa ta kama, dai-dai lokacin su Baba Malam suka iso, ɗayan hannunta tasa ta kamo hannun Baba Malam ɗin.
Ƙam ta riƙe hannun Baba Malam, cikin wata irin murya me ɗauke da tsananin sanyi tace.
"Tun kwanaki nake ta ji ajikina cewa, mutuwa zanyi Baba, rayuwata tazo ƙarshe, Dan Allah Baba Malam kayafemin, sannan kaya fewa Zaleeha, nasan duk inda take tana cike da kewa, da kuma nadamar abun da ta aikata, natabbata kuma idan ta dawo zatayi maka biyayya fiye da wanda ni nayi ma, dan Allah Baba Malam ka yafewa Mama, ka barta ta dawo ɗakinta ta zauna, dan nasan itama tayi nadama, nikam nasan bazan sake zama acikin ku ba, nasan daga nan bazan koma gida da numfashi ba, lokaci na yazo, zan tafi na barku badan naso ba, zan yi nesa daku, zan tafi inda bazaku sake gani, ko jina ba."
Hannu ya Ameenu yakai ya rufe bakinta, tuni wani irin kuka ya taso masa, kansa ya shiga girgiza wa, murya na rawa yace.
"Bazaki mutuba Maryam, bazaki mutu kibarni ba Insha Allah zaki samu lfy. Rayuwata bazata taɓayin inganci ba, matuƙar babu ke acikinta, dan Allah kidaina faɗin cewa zaki tafi ki barmu, muna tsananin buƙatarki agaremu."
Hawaye ne suka tsananta zuba daga cikin idanunta, wani irin murmushi me ciwo tayi tare da girgiza kanta cikin sanyi tace.
"Dan Allah ya Ameenu idan na cika, ku maidani gidan Baba Malam kuyi mini wanka acan, sannan kusamin sutura, idan kun sallaceni, inaso kusani cikin kabarina da hannuwanku."
Shiru tayi sakamakon shaƙuwan daya taso mata, kuka Ya Ameenu ya fashe dashi, tare da soma girgiza kansa, sake damƙe hannun Yaa Ameenu da kuma Baba Malam tayi, cikin wani irin yanayi da muryarta wanda bata fita sosai tace.
"Kuyafewa Zaleeha, kada kuyi mummunan kuma dogon fushi da ita, Mamy ke da Ya Habu ku yafe mata, nikam zantafi na barku nasan da cewa zakuyimin addu'a aduk lokacin da kuka tuna dani, sannan Baba Malam zan tafi, ina me al'faharin kasancewar ka mahaifi agareni." Hawayen da suka cika idanun Baba Malam ne suka samu daman gangarowa, take wani irin kuka ya taso masa, sake damƙe hannun Maryam ɗin yayi, Mamy kuwa tuni ta koma gefe tana kuka, Ya Habu ma kukan yake sosai. Idanunta wanda sukayi farare fat ta ɗago ta zubawa Ya Ameenu dake kuka, yana ta faman girgiza mata kai, murmushi tayi masa, kana kuma tamaida dubanta ga Baban Malam, lokaci guda ta soma wani irin shaƙuwa, ganin haka yasa Baba Malam fashewa da wani irin kuka, mai tsuma zuciya, sosai ya kama hannunta yana ji yana gani ƙudirin Allah na wakana bashida iko ko da, da ace duk duniya gatan Maryam ne da masoyanta bazasu tseratar da ita koda na second ɗaya ba, cikin muryar kukan yake. faɗin kalmar.
"La'ila ha'illallah, muhammadur rasulullah, sallallahu alaihi wasallam!!!." Haka yake faɗan kalman ararrabe saboda matsanancin kukan dayaci ƙarfinsa. Cikin muryarta, dake ɗauke da shaƙuwa itama tasoma bin bakinsa, tana faɗan kalman shahada'n, duk abun daya faɗa itama sai ta faɗa, atare suka kai ƙarshen salati'n shida ita, nan take yaji jikinta yayi sanyi, komai nata ya sake, idanunta sun kafe suna kallon sama, yayinda baƙin cikin ƙwayar idanun nata ya ɓace ɓat, sai farin kawai kake gani.
Ya Ameenu kuwa dama tuni ya daina gane komai, hakanne ma yasa bai lura da cewar ta daina motsi ba, cikin wani irin yanayi Baba Malam yaja da baya tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya, kuka irin wanda bai taɓayi ba arayuwarsa, wannan kukan nasa shine abun dayasa Mamy da kuma Ya Ameenu da Habu, suka kai dubansu garesa, ganin irin kukan da yake, yasa Mamy da Ya Habu suka tabbatar da cewa, Maryam ɗin tarasu, kuka Mamy tasa sosai, shima Ya Habu haka, Ya Ameenu kuwa hannunta dake cikin nasa yaɗan murza, idanunsa sun cika tab da ƙwalla, hakan yasa baya ganin yanda idanunta suka juye, cikin muryar kuka yace.
"Bazaki mutu ba Maryam, in sha Allah bazaki mutu yanzu ba, saboda muna da buƙatarki acikin rayuwarmu, kidaina faɗin cewa zaki mutu, mutuwa bazata ɗaukeki yanzu ba, idan kika mutu kuma ya kikeso ni nayi da rayuwata? bazan iya zama babu ke ba, ki tashi kinji!."
ya ƙare maganar yana meɗan jijjigata, jin hannunta dake cikin nasa, jin yayi nauyi ne, yasashi matse hawayen da suka cika idanunsa, har suka hanasa gani da kyau, duban fuskarta yayi, nan yaga idanunta sunkafe, take yaji wani irin abu ya bugi kansa, dai-dai lokacin kuma, Doctor'n da Ameena ta ƙira ya shigo cikin ɗakin da sauri, ganin yanda su Baba Malam ke kuka, ya sa shi ƙarasowa jikin gadon, idanunta daya gani akakkafe yasashi girgiza kansa, nan yaja wani ɗan mayafin dake jikinta ya rufe fuskarta bayan yasa hannu ya shafe idanunta. Girgiza kai Ya Ameenu yashiga yi, cikin kiɗima yace.
"Miye haka? meyasa ka rufe mata fuska?"
Cikin tsananin tausayawa Dr. É—in yace. "Am sorry to say Allah yayi mata rasuwa."
Tamkar sauƙan guduma haka Ya Ameenu yaji maganan doctor'n acikin kai da kunnuwansa, lokaci guda yaji gaba ɗaya lakar jikinsa ta tsinke, ƙafafunsa ne suka gaza ɗaukan nauyinsa, take yazube akan guiwowinsa, kifa kansa da jikin gadon Maryam ɗin yayi, yasaki wani irin kuka mai tada hankali, wani irin kukane, me matuƙar jijjiga zuciya, wanda hakanne yasa Ameena dake waje shigowa cikin ɗakin. kuka Ya Ameenu keyi me tsanani, irin wanda duk wanda yaji sa, dole ya tausaya masa, lokaci ɗaya jikinsa ya soma rawa, numfashinsa ne yayi wani irin fusga, take ya faɗi awajen sumamme.
Cikin sauri Ya Habu da Dr. É—in sukayo kansa, dan Baba Malam kam kuka yake sosai da sosai.
Chapter 62 · 0% Book details