← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 154

Sashe 3

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saifuddeen kuwa, kafin ta tura mishi texts d'inma yayi bacci sabida a gijiye yake.

Washe gari tun da sanyin safiya, Ahmad da Salisu suka shigo da masu gyaran gida,
dan sabunta fentin gidan.

Kai tsaye sashin wannan part guda biyun nan wanda yakeda ciki da parlour da dinning area, a tsakanin part d'in da komansu iri d'aya suka nufa.
In da nan Raliya da Ahmad suke a d'aya part d'in.
Nuna musu duk gyaran daya dace sukayi kamar farfasa steps d'in tsakanin parlour da dinning area, yadda wheelchair D'inshi zaibi ko ina a part d'in har zuwa cikin parlour'n nan mai 2 beedroom dan nanne zai zama turakarshi.

Suna gama nuna musu suka fara aikinsu,.
Su d'in kuwa kai tsaye cikin gidan suka nufa,
jin shiru parlour ba kowa yasa suka wuce parlour Saifuddeen,
suna shiga suka hangoshi kan wheelchair d'inshi mai azabar kyau. Ya bawa k'ofar shiga baya.
Ba jin takunsu zaiba bare yasan akwai mutane a bayanshi,
Wayarshi ya zubawa ido yana maimaita karanta text d'in da Zaleeha ta turo mishi a karo na barkatai.
Wani irin zaro ido Ahmad yayi lokacin da idanunshi sukayi arba da abinda ke rubuce a wayar, wani irin zazzafan numfashi ya sauk'e da k'arfi tare da...!

Littafina na kuɗine in kin karanta na sata kin san sauran in kina ɓuƙata turo katin mtn na raɗi uku kacal ta wannan number 09097853276 ko kuma ki biya ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Zazzafan numfashi ya sauƙe, da ƙarfi ya fusge wayar daga hannun Saifuddeen, sosai hankalinshi ya tashi ransa yayi mummunan ɓaci dan ganin kalaman da Zaleeha ta rubutawa Saifuddeen tacikin text message, wani irin ɓaƙin ciki da ɓacin raine suka tokarewa Ahmad maƙoshi, shikam baisan meyasa Saifuddeen ya maƙalewa Zaleeha ba, yarinyar da bata ganin mutumci da ƙimarsa ko kaɗan, yarinyar da ta maida rashin kunya man shafawanta.
Ɓata fuska Saifuddeen yayi tare da miƙowa Ahmad hannu, alaman ya bashi wayarsa.
Fuska Ahmad ya haɗe sam babu alaman wasa akan fuskarsa haka ya juya ya nufi hanyar fita daga ɗakin, da kallo Saifuddeen ya bishi, wani ɗan guntun murmushi ya sake, haƙiƙa yasan Ahmad sam bayason aurensa da Zaleeha, ya kuma san dalili, amma yasan nanda wani lokaci kaɗan Ahamad ɗin zai fahimta.
Cikin   zafin zuciya haɗi da fusata Ahmad ya nufi ɓangaren Ummi.
Zaune Ummi take akan kujera gefenta kuwa Raliya ne zaune tana ta yabawa da koda d'inkunan zafafan laces É—in dake gabanta, wanda Saifuddeen ne ya saya musu donyin fitan biki.
Murya can ƙasan maƙoshi Ahmad yayi sallama, inda ya kutsa kansa cikin falon, fuskar Ummi cike da fara'a ta amsa masa, saidai kuma yanayin yanda taga fuskarsa yasanya taji ba daɗi, domin Ahmad mutum ne me yawan fara'a, baƙaramin abu bane zai sanya kaga ya ɓata fuska.
Raliya kuwa ji tayi gabanta ya faÉ—i, sakamakon ganin mood É—in mijin nata.
Zama Ahmad yayi akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunsa.
Dubansa Ummi tayi cikin sanyin murya haÉ—i da bayyanar da damuwarta tace.
"Ahmad lafiya kuwa?."
Ɗago idanunsa wanda sukayi jajur yayi ya kalli Ummin tare da miƙo mata wayar Saifuddeen dake hannunsa.
Amsan wayar Ummi tayi tare da kai dubanta ga screen É—in wayar, wanda har yanzu screen É—in keda haske bai É—auke ba, wanda shi Saifuddeen azatonsa Ahmad baisan security É—insa ba, shiyasama yabar Ahmad yatafi da wayan, shikuwa Ahmad dama tun tuni yasan securityn Saifuddeen É—in, don ranan agabansa Saifuddeen yacire wayartasa a security.

Idanu Ummi ta ƙurawa rubutun dake kan screen ɗin wayar, sannu ahankali take karanta saƙon, lokaci guda jikinta ya ɗauki wani irin rawa, take yanayin idanunta suka sauya daga farare zuwa ja,  aƙalla ta maimaita karanta saƙon yafi sau uku, batare da ta sani ba, sosai zafafan baƙaƙen maganganun da aka rubuta cikin saƙon ke yawo acikin brain ɗinta.
Babu abun dayafi É—aga mata hankali kamar inda Zaleehan ta rubuta cewa.
```"Ka turo iyayenka su janye batun aurena da kai! Su zo su kwashi wannan tarkacen da kasa aka tarkato aka kawo mana jidali. In kuma kaki yin hakan ka kuskura ka bari akayi auren nan aka kawoni mushen gidan kunnan to.
Wallah Allah kenan``` Saifuddeen, in ka bari akayi auren nan cikin biyu za'ayi É—aya ko in mutu ko ks matu!!!."

Sosai tunanin Ummi ya tsaya cak, wani irin matsanancin tsorone ya daki zuciyarta, sosai kalaman Zaleeha suka ɗaga mata hankali, tabbas tanayiwa ɗanta Saifuddeen tsantsar so, bakuma tason wani abu da zai cutar dashi,  tayaya ma amatsayinta na Uwa zata zuba idanu tana kallo ɗanta yakai kansa ga inda ake neman halakasa, tabbas acikin kalaman na Zaleeha tagano cewa bata ƙaunar Saifuddeen ko kaɗan,  sam bazata taɓa bari Saifuddeen ya auri macen da take da bushashshen zuciya ba.
Hawayen da suka cika idanunta tasoma ƙoƙarin shanyewa, cikin raunin daya bayyana akan fuskarta ta dubi Ahmad.
Shi É—inma Ahmad dubanta yayi, cikin rauni yace.
"Ina takaicin tsananin son da Saifuddeen kewa Zaleeha, bata sonshi Ummi sam bata ƙaunarsa, bata ganin ƙima da darajarsa, tun awaje tana faɗa masa mugayen kalamai irin wannan inaga kuma idan anyi auren? ba fata nake ba Ummi amma sam banason abun dazai wargaza mana farin cikin mu, Saifuddeen kamar jigo yake agaremu baki ɗaya, bazan iya zuba idanuna naga ya jefa kansa cikin mawuyacin hali ba, Ummi zuciyar Zaleeha tayi zurfi sosai wajen tsanar Saifuddeen, saboda haka zata iyayin komai idan ya aureta."
Ɗan tsagaitawa da maganan yayi tare da maida ƙwallan da suka cika idanunsa, ci gaba yayi da cewa.
"Ai Nakasa Ba hauka bace bare tace baida hankali bazata iya zama da shiba, kuma Nakasar Saifuddeen bashi yake nuna cewa ya kasa ba,   mene aibun Saifuddeen Ummi? shin laifine don Allah Ya jarrabeshi da nakasa? ko kuwa laifine don yazamo kurma kuma gurgu, shi nakasashshe ba mutum bane kenan? Wallahi Ummi Saifuddeen bai dace da Zaleeha ba, saboda bata yarda da ƙaddara ba, hartanajin cewa ita watace, wacce ajinta ya ɗara nakasashshe, ta manta cewa da me lafiya da kuma nakasashshe duk halittar Allah Ne."

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da sakin wani murmushi wanda yafi kuka ciwo.
Cikin tsananin tausayin ɗannata Saifuddeen da irin ƙaddaran da Allah Ya ɗauro masa tace.
"Inajin tsoro Ahmad, Inajin tsoron abun da zai faru nan gaba, bana fatan yarinyarnan  Zaleeha ta cutarmin Saifuddeen cutarwa mafi muni."
Still ajiyar zuciya ta kuma sauƙewa, tare da miƙewa tsaye,  duban Ahmad takumayi cikin sanyin murya tace.
"Ahmad zanyi abun da ya dace, abunda  kowacce uwa zatayi dan kare rai da lafiyar danta zanyi abinda ya kamata ace  tayi a matsayina na uwa!."
Tana gama fad'in haka ta juya ta nufi hanyar É—akinta.

Tuni hawaye sun wanke fuskan Raliya, duk da cewa bata karanta saƙon da Zaleehan ta turowa Saifuddeen ba amma tabbas ta fahimci duk abun dake faruwa, daga cikin kalaman na Ummi da kuma mijinta Ahmad.
Dubanta Ahmad yayi, itama kallonsa take, yayinda hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunta, shin menene aibun Hamman'ta don yakasance gurgu kuma kurma? shima mutum ne kuma Namiji kamar kowa, yana da cikakkiyar lafiyansa na ɗa namiji, sannan gurguntan sa bazai zama kasawa agareshi ba, don meyasa Zaleeha zata ƙisa?
Kai Ahmad ya girgizawa Raliya alaman ta daina kuka.
Kasa jurewa tayi, hakan yasa ta faÉ—a cikin jikinsa tare da sakin kuka mai sauti.
Rungumeta yayi ƙam tare da sake jawota jikinsa,  nan yamiƙe tsaye tana ajikinsa suka nufi hanyar barin falon.
Suna fita suka yi karo da Hayatuddeen wanda shigowarsa cikin gidan kenan, sanye yake da white t shirt da kuma 3 guater jeans, hannunsa riƙe da wayarsa ƙiran Samsung yayinda kunnensa ke saƙale da earpiece,  yana ganinsu yaɗan yi turus tare da turo bakinsa gaba, har acikin ransa shikam yagaji da ganin Yayar tasa Raliya da Ahmad manne da juna sunashan soyayyarsu kamar tattabaru, kullum haka yake ganinsu liƙe da juna kamar wasu tif da taya.
Hararansa Raliya tayi da jajayen idanunta,  sake kwaɓe fuska yayi yana shirin yi musu halinnasa na shagwaɓa ne, Ahmad ya miƙo masa wayar Saifuddeen, batare da Ahmad ɗin yace komai ba yaja Raliya suka nufi ɓangarensu.
Da kallo Hayatuddeen ya bisu har suka ɓacewa ganinsa,  bakinsa ya taɓe ƙasa-ƙasa yace.
"Hegu fitinanu, kuyi dai nima dana ƙara girma, ai dai zanyi auren nan ehe, don haka duk wani me ɗagamin kafaɗa ma gwara ya daina, nima ai zanyi auren bawai ba zanyi ba."
Haka ya nufi ɓangaren na Saifuddeen yanata ƙunƙuni aransa.
Koda ya ƙarasa part ɗin a parlour ya had'u da Salisu dake saurin fita, dan sunyi mgna da Saifuddeen kam batun Rashida na son su kai musu kud'in walima, so shine ya fita da sauri dan kai mata kud'in,
cikin girmamawa yace.
"Ina kwana Ya Salisu."
"Lafiya lau Auta ya sakalci."
Salisu ya amsa mishi ba tare da ya tsaya ba,
Murmushi Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Manyan angwaye sai b'are-b'are suke uwa hanji a langa."
yana musu tsiya ya wuce ya nufi bedroom d'in Hamma
Saifuddeen din nashi zaune ya sameshi akan wheelchair ɗinsa, inda ya tasa laptop ɗinsa agaba ƙiran company'n apple yana dannawa.
Akan cinyar Saifuddeen ɗin ya ɗaura wayar tare da yin super ya faɗa kan lallausan gadon na Saifuddeen, lumshe idanu yayi yana me shaƙan daddaɗan ƙamshin na Hammansa, aransa yana fata ace watarana shima yazama kamar hamman nasa.
Saifuddeen kuwa murmushi kawai yayi tare da É—aukan wayar tasa ya duba, ganin still akan message É—in Zaleeha yake, yasanyashi sakin murmushi, domin jikinsa ya basa cewa Ahmad bai cire wayan a security ba balle yayi amfani dashi.
Cigaba yayi da aikinsa,yayinda time to time yake sipping exotic juice É—in dake gefensa.
Chapter 3 · 0% Book details