← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 154

Sashe 38

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saifuddeen kuwa yana shiga ɗakinsa, ya soma rage kayan jikinsa,  ƙarasawa gaban tankamemen bed ɗinsa yayi, nan ya sauƙa akan wheellchair ɗinsa, inda ya hau gadon.
Lumshe idanunsa yayi tare da jawo blanket ya rufe jikinsa,   maganar ƙarin auren nasa daya dawo cikin kunnensa ne, ya sashi jin wani ɗaci a maƙoshinsa, sam shi baima ɗauki abun agaske ba, yasan suna faɗa ne kawai, amma shi ina yaga ta wani ƙara aure, shiru zaiyi ya ƙyalesu, yasan nan da kwana biyu suma zasu daina batun.

Yana nan kwance, yaji vibration na wayarsa, don dama akusa dashi take.
Kasancewarsa wanda bayajin magana, ko kuma wani sauti, hakan yasa koda yaushe wayarsa a vibrate take,  domin ta hakanne kaɗai zai gane cewar an turo masa saƙo, domin idan kunnensa baya ji, to ai jikinsa naji, don aduk sanda wayan ke kusa dashi, ko kuma take jikinsa, to zai jita tana rawa, hakan kuwa alamane na cewar an turo masa saƙo, ɗaukan wayar yayi tare da dubawa, ganin  saƙon na Ummin sane ya sashi buɗewa.
Number'n wayane arubuce da kuma rubutu aƙasan sa kamar haka.
"Wannan number'n itace number'n matar da na zaɓa maka amatsayin wacce zaka aura, saboda haka kayi saving ɗinta."
Yana gama karanta saƙon ya tashi zaune cikin hanzari, jiyayi gabansa ya faɗi, cikin sauri ya jawo rigarsa wanda ya cire, nan ya sanya tare da hawa kan wheellchair ɗinsa, ahanzarce ya nufi part ɗin Ummi'n dan yafa lura su da gask suke nufin ƙara mishi auren.

Koda yaƙarasa falon ta bai ganta ba, kai tsaye yanufi bedroom ɗinta.
Tsayawa ajikin ƙofar yayi, tare dayi mata knocking,  Ummi dake kwance jin ana knocking yasa ta tashi ta zauna, murmushi tayi don tasan cikin biyu za'ai ɗaya, ko Saifuddeen ko kuwa Raleeya.
"Shigo." Ta faɗa ataƙaice.
Da sauri ya tura ƙofar ya shiga, Ummi na ganinsa taɗan tsume, tare da dubansa.
Ƙarasowa yayi har gabanta, inda ya kamo duka hannayenta, kansa ya shiga girgiza mata, alaman "a'a."
murmushi tayi tare da cewa.
"A 'a me? bazakayi auren ba ko kuwa me? ko bakason zaɓin danayi maka, ba kuma zaka iya karɓanta matsayin zaɓina ba?."
Shiru yayi tare da É—an lumshe idanunsa, kansa ne ke sarawa, cikin body language É—insa, yace.
"Bawai zaɓinki bane banaso Ummi, ni auren ne banaso, ki dubeni ki gani fa, tayaya zan iya rayuwa da mata biyu, ko kun manta abun da Dr. ya faɗa ne, ina ɗauke da nakasa banjin cewa, zan iya bawa mata biyu kulawan daya dace dasu ba."
Dariya Ummi tasanya, tare da dubansa, saida tayi dariya sosai sannan taÉ—an soma tsagaitawa, shikuwa Saifuddeen kafeta yayi da idanunsa, tare da sanya mata fuskan tausayi.
ÆŠan tsagaitawa da dariyan Ummi tayi tare da cewa.
"Ikon Allah, Yau kuma Saifuddeen kaida kanka kake ƙiran kanka da Nakasashshe? duk saboda ance ka ƙara aure shine har ka aminta cewar kai nakasashshe ne, har kuma ma kake ƙiran kanka da hakan, tsawon lokaci ban taɓa ji kaƙira kanka da wannan sunan ba, amma yau sai gashi da bakinka ka faɗa, ka kuma nanata.  hmmm lallai ma kuwa to wallahi in sha Allah auren nan babu fashi, sai anyi shi, na kuma gama yi maka zaɓi, umarni ne idan kuma kace a'a, shikenan saika ƙira surukin naka wanda ya yanke hukuncin, kace masa kai bazaka bi umarninsa ba."

Idanunsa ya lumshe, jin zuciyarsa yake tayi masa nauyi, a kasalance, cikin yanayi marar daɗi yace da Ummi, ta sanar dashi, "Wacece zaɓin nata?."
Nan Ummi tace.
"Idan yana buƙatar sani, zai iya zuwa ya tambayi Adda Rahama, zata sanar dashi koma wacece."
Jin haka yajuya yafita jiki a mace, yana mai saƙawa ransa to wacece ina take ina suka samota da zasu liƙa mishi ita, tuno babu in da zai samu amsoshin duk waɗanan-nan tambayoyin sai wurin Adda Rahma.
Ae kuwa kaman jira yake cikin sauri ya juya ya fice daga cikin É—akin.
Kai tsaye ɓangarensa ya nufa, inda ya kimtsa kansa,  koda ya fito text message ya turawa Ahmad kan cewar yana son ganinsa.
Kasancewar Ahmad É—in na cikin gida, hakan yasa mintuna kaÉ—an sai gashi ya fito.
Cikin body language Saifuddeen É—in yace da Ahmad.
"Ya kaishi gidan Adda Rahama."
Sanin kwanan zancen yasa babu musu, Ahmad ya ɗauko musu mota, nan suka shiga, inda ya jasu zuwa gidan Adda Rahaman bayan sun biya jonapwd sun ɗauƙi ishaq wanda a zaton Saifuddeen ishaq zaibi bayanshi.

Koda Adda Rahama ta gansu batayi mamaki ba, don tun kafun zuwansu Ummi ta ƙirata ta yi mata bayanin komai.
Tray ɗin drinks masu sanyi ta dire agabansu, Ahmad ne ya ɗauki kwalin exotic ya miƙawa ishaq kana shima ya ɗauka inda yasoma kwankwaɗa, don shi fes yakejin ransa bashi da wata damuwa.
Hakama ishaq da shi yafi kowa jin haushin Zaleeha, kuma Babanshi ya mishi bayanin son ƙarawa Saifuddeen aure da Baban Zaleeya ya shiryawa.

Saifuddeen kuwa fuska ya marairaice, duban Adda Rahama yayi, tare da É—aukan wayansa, cikin message É—in Ummi ya shiga, nan ya nuna mata fuskar wayar, tare da yi mata alaman tambaya, kan cewa.
"Wacece? Ina take?".
Murmushi Adda Rahama tayi masa tare da cewa.
"Miye abun tada hankalinka haka ne Saifuddeen? da ka nutsu ma don amaryar taka ba ɓoyayya bace awajenka kasanta."
Cikin son ƙarin bayani ya zubawa Adda Rahama'n fararen idanunsa.
Duban tsab Adda Rahama tayi masa, kana cikin nutsuwa tace.
"Nasan kasan Ameena ae, wannan nurse ɗin da ta baka kulawa, lokacin da kake jinya a Abuja, kafun ku wuce India, to ita ce dai Ummi ta zaɓa maka, nima kuma nayi na'am don yarinyar akwai hankali, Masha Allah.
Ka tuna har gida tazo itada Mamanta suka dubaka da jiki."

Idanunsa ya zazzaro waje tare da jujjuya kai da ƙarfi sosai yashiga mamaki, lokaci ɗaya yaji kaman an watsa masa ruwan zafi, amamakance ya ɗan ƙanƙance idanunsa, cikin yanayin maganarsa wanda ya saba, wato body language yace.
"Allah ya sauwaƙe ni dai na auri wannan Ameenan, mezanyi da ita bazawara ce fa!."
Cikin tsananin mamaki Adda Rahama ta dubeshi,  kallonsa tayi da kyau tare da faɗin.
"Kai Saifuddeen banda sharri bazawara kuma? wa ya faÉ—a maka cewar bazawara ce?".
Murmushin gefen baki yayi, tare da jijjiga kansa, in a body language É—insa yace.
"Impossible!, nine zan auri bazawara? chab hmmm Allah ma ya sauwaƙe, sam banason sauran wani wlh Allah ya kiyasheni suɗe ƙashin da wani ya rigani tsotsa."
Baki Adda Rahama ta buɗe fuska cike da tarin mamaki sauƙe a jiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Wai nikam wayace dakai itaÉ—in bazawara ce?."
A shagwaɓe ya rubutawa Addan nasa.
"Ae basai an faÉ—a min ba, duk ckekken Namiji in dai ya nitsu idan mace bazawara ce zai gane ta ido, kuma nayi imani cewa Ameena bazawara ce, saboda haka ni dai bana sonta wlh bazan iyaba, ba kuma zan aure ta ba."
Ahmad da Ishaq kam dariya sukeyi sosai fahimtar abinda yake faÉ—in.
Baki Adda Rahama ta taɓe, inda ta gyara zamanta, dubansa tayi da kyau,ido cikin ido tace.
"Naji koma dai bazawara ce, ita Ummi ta zaɓa maka a matsayin mata, sannan da kake ta maganar cewa, ita bazawara ce, kai ɗin dakake magana saurayi ne kai? inace kaima bazawarinne tunda dai kayi aure."
Bakinsa ya turo gaba, a shagwaɓe ya narke fuska, cikin body language yace.
"Wallahi ni banason Ameena, yarinyar da idanunta abuÉ—e suke, ta fa riga da tasan Namiji, sannan kuma har yanzu ni matashin saurayi ne, tayaya ma zan yarda na auri Ameena."
Duban Adda Rahaman yayi tare da kamo hannunta, cikin yanayin daya saba musu alaman magana yace.
"Kin sanni tun ina ƙaramin yarona ma ko ta yaya bana amfani da tsohon abu, hatta kaya idan ya kasance gwanjo ne bana sawa, sannan idan yakasance wani ya taɓa amfani da abu, bana kuma amfani da abun, a iyaka tsawon rayuwata nafison komai sabo, koda wajen zama ne nafison sabo, banason wanda wani ya taɓa amfani dashi, harta mota ko wayar hannu, ban taɓa sayan second ba, komai na nafison yakasance sabo, ko lokacin da nake makaranta, ko yaushe ni nake zuwa first a acikin aji, bana taɓa yarda nazo second akomai na, to me yasa yanzu zan yarda na auri mace second hand? sauran wani, wanda wani ya cakalkala ya bari, ragowar wani fa Adda tunda nake gidannane kawai nataɓa sayan abu second hand kuma kin san shima saida na sabunta mana shi, bazan iya auren sauran waniba kinfa san inada kishi."
Kansa ya girgiza tare da cije laɓɓansa.
Baki buɗe Adda Rahama ke kallonsa, sosai take mamakin ƙarfin hali irin na Saifuddeen ɗin.
Shikuwa Ahmad da shaq dake gefe sai ƙyalƙyala dariya suke tayi, don sosai show ɗin na Saifuddeen keyi musu daɗi.
Ajiyar zuciya Adda Rahama ta sauƙe tare da cewa.
"Koma menene dai Ummi ta gama magana, kuma ta yanke hukunci, wanda mu dukan mu mun gamsu, ta kuma ce zata sanar wa Bappa Ali, don asamu ayi bikin cikin gajeren lokaci, kaman yanda Baba Malam ya buƙata, kai da za'ayi maka auren gata ma, miye na damun kanka, sadaki, kayan aure, komai da komai, duk fa Baban Zaleeha yace ya ɗauke ma, wannan kaɗai bai isa saka farinciki ba, auren huce haushi fa zaiyi maka."
Jan kujeransa baya yayi, inda ya kwaɓe fuska, nan ya dubi Ahmad yace dashi.
"Su tafi." kana ya ja hannun ishaq
Shidai Ahmad dariya kawai yake, har hakan yaso ƙular da Saifuddeen.
Haka dai suka dawo gida, bayan sun sauƙe ishaq ko amota Saifuddeen fuskar nan tasa aɗaure take tamau.
Suna isowa gida, kai tsaye part É—in Ummi ya sake komawa.
Ganinsa yasa Ummi kafesa da ido, cikin sanya fuskar tausayi, yayiwa Ummi alaman cewa.
"Shi bayason Ameena, saboda bazawara ce, sannan kuma shi tsoronta ma ya keji, gata da kallon tsiya, sai kace mayya, gaba É—aya idanunta abuÉ—e suke."

Dubansa Ummi tayi, tare dayin dariyar zuci batayi mamakin jin cewa Ameenan bazawara bace, saboda kafun isowarsu Adda Rahama ta kirata tasanar mata.
gyara tsayuwa tayi tare da cewa.
"Allah mai iko, yau kuma Saifuddeen  kai ne me tsoron mace? uhmm saboda bakason auren ta  shiyasa kake tsoronta ko?"
Chapter 38 · 0% Book details