← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 154

Sashe 87

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari.
Zaleeha ne zaune nan kan ɗaya daga cikin kujerun falon, kamar kullum sanye take da baƙar doguwar riga, Adeel ne riƙ ahannunta, wanda yasha wanka aka kuma shiryasa tsab cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na yara.
Sosai Zaleeha ke tayiwa Adeel ɗin wasa, shi kuma sai ƙyaƙyata dariya yake.
Raleeya dake zaune agefensu kuwa murmushi kawai take ta yi musu, dan ita kanta tanajin daɗin yanda Zaleehan ke nunawa Adeel ɗin ƙauna.
Ameena ce ta shigo falon cikin É—an sauri sauri tare da shirinta na zuwa aiki,
Raleeya ne ta dubeta da murmushi akan fuskarta tace.
"Monday tushen aiki ko na sara na tsoranka, kina ta sauri karki makara kenan." Jakan dake hannunta ta rayata tare da cewa.
"Eh wallahi, kinga lokaci nata tafiya, gashi sam banason yin late wallahi." ta ƙare maganar tana me ɗan miƙawa Adeel dake kallonta hannu, Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Ummun Adeel barka da safiya."
Itama Ameenan murmushin tayi tare da cewa.
"Yauwa Auntyn Adeel barka, yi haƙuri na ɗaura miki ɗawainiya, ai danaga idan na tsaya shiryasa zan makara ne, shi yasa naƙira Hayatuddeen nace kawai ya kawosa ashiryamin shi anan ɗin."
ÆŠan murmushi Zaleehan tayi tare da cewa.
"Ayya to ki barmin shi yau kam mu wuni mana."
Haɓa Ameenan ta kama tare da cewa.
"Chab aikuwa zaki sha kuka, dan Adeel baya wasa da ci, nan da anjima zakiga ya fara neman nono."
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Ya gado Bappanshi autan Ummi a cici kazar birni."
dariya sukayi baki É—aya su,
shi kuwa Hayatuddeen da yanzu yake fitowa tura baki yayi tare da cewa.
"A,a zakarar birni dai." Ummi wanda fitowarta kenan daga É—aki ta kawar musu rigimar autanta da cewa.
" To ki barshi mana, ba akwai madara da kuma abincin nan na yara basai adama masa yasha ba." ÆŠan murmushi Ameenan tayi, tare da cewa.
"Ai idan na fita yau Ummi bazan dawo ba har sai bayan magriba, kuma kinga kafun nan zaita damunku da kuka, saidai gobe ƙarfe 5 zan tashi a aiki, kinga saina bar muku shi goben ko." Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"To Adawo lafiya, dan dama nasan idan kika barsa ni zai dama da wannan rakaÉ—in muryan nasa."
Dukansu murmushi sukayi sannan Ameena, ta amshi Adeel ɗin ta saɓashi akan kafaɗunta, suka fice daga cikin falon, sai kallon Zaleeha yake, har yanayi kaman zaiyi kuka. Ita kuma Zaleeha hannu ta ɗaga masa tana murmushi.

A can side É—insu kuma Saifuddeen ne zaune akan wheelchair É—insa, bayan ya gama shirya kansa tsab dan yanaso yaÉ—an fita.
Har ya juya xai fita daga É—akin, kuma sai ya É—an dakata, wayarsa ya É—auka tare da shiga Whatsapp chat É—insa, sunan Ahmad ya nemo dan dama yanaso suyi magana,
cikin sa'a kuwa ya samu Ahmad É—in online. typing ya shigayi inda yace da Ahmad É—in. "Aikin kenan always online baka ko gajiya, dama magana nakeso muyi."
Ahmad dake zaune nan kusa da Raleeya ganin saƙon Saifuddeen ɗin ya sashi buɗewa ya karanta, ɗan murmushi yayi tare da cewa "Inajinka wace magana ce?".
ganin saƙon Ahmad ɗin yasa ya ɗan gyara zamansa ataƙaice yace.
"Dama furnitures É—in bedroom É—ina zan sanja, so na ga wasu a online kuma har na biya kuÉ—insu, abun da dai ya rage kawai shine akawomin." Idanu Ahmad yaÉ—an zaro, cikin mamaki yace. "wani furnitures kuma Saifudeen, meya samu na É—akin naka, kwata kwata ma yaushe ka saya da har kakeson sanjawa?". ÆŠan guntun murmushi Saifuddeen yayi tare da cewa.
"To nidai banason gulma, na faÉ—a mane dan katsaya min akan kayan saboda suna da tsada sosai, mungama yin magana da masu company'n kuma sunce zasu kawomin har gida, dan na fiso idan aka cire na É—akina akaiwa Goggo Dada dan naga itama furnitures É—inta sun tsufa."
Kai Ahmad ya girgiza tare da É—anyin murmushi yace.
"Agaskiya yaron nan kana wasa da kuÉ—i da yawa."
Ahmad ya ƙare typing ɗin yana sakin dariya.
Ganin abun da Ahmad ɗin ya rubuta, yasa Saifuddeen ɗin cewa. "Lallaima Ahmad ni kake ƙira da yaro, koda kanmu ɗaya kardai ka manta cewar ƙanwata kake aure, saboda haka yazama dole kaƙirani da sunan Yaya." Dariya sosai Ahmad yayi, sannan yace wa Saifuddeen ɗin, "Bakomai zaiyi duk abun da ya dace, amma ya barshi yanzu lokacin matarsa ce tukun." Murmushi kawai Saifuddeen yayi, tare da aje wayar, dan yasan idan ya biye Ahmad, sai ya zaro masa wata maganar kuma.
ÆŠan jingina bayansa yayi da jikin wheelchair'n É—insa, tare da É—an juyowa ya kalli gadon nasa,
cute smile yayi, cikin zuciyarsa yace. "Wannan gadon ayanzu bashi da amfani agareni, saboda Ameena taci amarcinta akai son ranta, yanzu kuma lokacin Zaleeha yayi, saboda haka dole nakawo sabin furnitures kodan saboda Zaleeha, dan kamar yanda take sabuwa, haka ma dole gadona yakasance sabo bazan haÉ—a mata komi sauran ta'annabina ba."
wani murmushi ya sake yi, wanda shi kaÉ—ai yasan ma'anarsa da kuma abunda yake nufi. Ahankali ya tura wheelchair É—insa ya fice daga cikin É—akin, kaitsaye part É—in Ummi ya wuce.
A falo ya sameta zaune ita da Raleeya, ƙarasowa cikin falon yayi, ganin haka yasa Raleeya tashi taje ta kawo masa kunun aya me sanyi, wanda ɗazu Zaleeha ta haɗa. Babu musu ya amsa kuwa yasha, tun aɗanɗanon farko yasan cewa ba Raleeya bace tayi, haka yaji kunun yayi masa daɗi, har baisan sanda yasha fiye da rabin ƙofin ba.
ÆŠan É—agowa yayi ya dubi Ummi, cikin body language É—insa yake faÉ—a mata cewar, zai sanja bedroom furnitures É—insa.
Da mamaki Ummi tace. "Zaka sanja kayan ɗaki kuma Saifuddeen, me ya samu waƴan can ɗin, da kake ƙoƙarin sanjasu ka kawo wasu?". Murmushi ya ɗanyi cikin body language ɗinsa yace.
"Ummi basuyi komai ba, kawai dai naga furnitures É—in Goggo Dada duk sun tsufa ne, shiyasa nakeso idan aka kawomin sabi sai akai mata waÆ´ancan É—in." Murmushi Ummi tayi tare da jinjina kai, cikin kulawa da jin daÉ—i tace.
"Masha Allah, to Allah ya ƙara arziki, ai kuwa kam gaskiya Goggo Dada taci sabin furnitures, gaskiya ka kyauta."
da "Ameen" ya amsa, sannan ya ce da ita
"Zai dan fita wajen aiki." "Adawo lafiya." Ummi da Raleeya sukayi masa, sannan ya juya yafita daga falon, bayan ya shanye gaba É—aya kunun ayan da Raleeya ta zubo masa cikin kofi.

Cikin ikon Allah da yamma kuwa sai gashi ankawo furnitures É—in, wanda kyawunsu ya zarta gaba É—aya kayan Æ´an gidan, wasu irin haÉ—É—aÉ—É—un white furnitures ne masu kyau da tsadar gaske, saboda tsabar haÉ—uwansu haka akayi design É—insu kaman na sarauta. Ma'aikatan companyn da kansu suka shirya masa kayan bayan suncire tsofin furnitures É—in.
Gadon da aka sanya masa, irin gadon nan ne da ake ƙira aljannar duniya.
Makeken gadone me ɗauke da tambarin MEGO luxury furnitures, wanda aka ƙawata kwalliyan jikinsa, da white and golden colour, yayinda samansa kuwa aka ɗanyi masa wani abu kaman rumfa, wanda yasha decoration mai masifar kyau, shikansa gadon kaɗai abun kallone, domin ya isa tafiya da hankalin mutum, gefe dashi kuwa, wasu haɗaɗɗun bedside ne wanda samansu ke ɗauke da mirror gold, sunyi kyau har sun gaji, idan aka matsa daga gefen dama kuwa, wani irin haɗaɗɗen drawer ne mai girma da tsari, kusan duka murafensa mirrors ne amma me zubin gold, ga kuma design na royal da akayi ajikinsa, yayi masifar kyau da burgewa.
Daga gefen hagu kuwa, wani dan ƙareren dressing mirror ne wanda shima aka tsara masa zane me kyau na royal, wanda suke shige da zubin gold, daga gefen mirrorn kuwa wani ɗan ƙaramin drawer ne, irin wanda ake aje takardu ciki, asaman sa anyi masa wani design na gold me masifar kyau da burgewa, har wani ɗan flower green aka sanya aciki. Sosai kayan furnitures ɗin sukayi kyau, sun kuma dace da ɗakin nasa ƙwarai, Ummi ita kanta da ta shigo ta matuƙar yabawa da kayan, gashi sun zauna aɗakin sunyi ɗas, saikace fadar shugaban ƙasa, saidai kuma kallo ɗaya zakaiwa kayan kasan sunja million's of Naira, dan kayane masu kyaun gaskene. Haka dai aka kwashi furnitures ɗin daya cire din, aka wuce dashi Dukku gidan Goggo Dada.

Koda ya dawo daga wajen aikin nasa kuwa sashin Ummi ya wuce. Anan ne Ummi take sake tambayar sa kan cewa. "Har yanzu baiga key É—in É—akin Zaleehan ba?" wani irin murmushi yayi tare da jinjina mata kai alaman.
"Eh." Idanu Ummi ta zuba masa, aɓoye itama tasaki murmushi, cikin ranta tace.
"Hmm dama ni ai najima da sanin cewa akwai abun da kake ƙoƙarin shiryawa, ajuri zuwa rafi dai wata rana dai tulu saiya fashe." Hira suka ɗan taɓa kaɗan a falon Ummi kafun daga bisani ya tashi ya tafi ɓangarensa, shikansa ya yaba sosai da kyawun furnitures ɗin daya saya ɗin, wanka yayi sannan ya nufi ɗakin Ameena, dan yasa aransa cewar bazai sake barinta taje ɗakinsa ba, shi zaike binta ɗalibta , har sai randa ya amshe budurcin Zaleeha bisa gadon kenan, saboda kwata kwata shi bai sayi wannan gadon saboda ita ba ya sayane dan cin amarci in ya amshe m'budurcin in yaso suci gaba da zuwa turakanshi.
Ameena kuwa koda ta gansa aɗakinta tayi mamaki ƙwarai, amma sanin cewa bayason yawan tambaye tambaye yasa taja bakinta tayi gum, sai hakan ma ya zame mata kamar abun farinciki, dan yaune rana ta farko daya biyota ɗakinta shiyasa hakan yayi masifar mata daɗi.
Chapter 87 · 0% Book details