← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 154

Sashe 83

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka baro gidan take sakin sheshsheƙan kuka, haka ta ɓoye kanta acikin cinyoyinta tana sakin wani numfashi me zafi, duk abun da takeyi yana lure da ita, amma sai ya kawar da kansa gefe yayi kamar bai ganta ba,
saida tafiyar tasu ta ɗanyi nisa, kafun ta ɗago kanta, ahankali ta sauƙe idanunta akansa, wasu hawaye masu zafine suka sauƙo daga cikin idanunta, ji tayi gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni sosai, wani irin ƙima da kuma girmansa ne suka cika idanunta, tabbas ayau ya taimaketa, yayi mata abun da mutane da yawa suka kasa yi mata shi, yau ya zame mata inuwa kuma majingina, ya kareta daga rana, sannan yayi ƙoƙarin haskaka rayuwarta, ya ɗaukota daga duhu ya kawota cikin haske, dame zata saka masa? wani irin kuka ne ya zo mata, hakan yasa ta faɗa jikinsa tare da rungumesa ƙam-ƙam tamkar zata haɗesu wuri ɗaya.
asakamakon hakan kuwa wani irin shock yaji ajikinsa, karon farko kenan da ta fara shiga cikin jikinsa dan kanta, hannayenta ta sanya ta zagayeshi, tare da ɗaura kanta akan faffaɗan ƙirjinsa, ta saki wani irin kuka mai taɓa zuciya, cikin kukan nata ne ta cusa fuskarta acikin ƙirjinsa, wanda hakan yasa aninayen dake gaban rigarsa ɗan ɓallewa, take kuwa fatan ƙirjinsa ta bayya, hakanne kuma yasa ahankali hancinta da laɓɓan bakinta ke gogan skin chest ɗinshi, wani irin kuka takeyi me taɓa zuciya, still kukan take tana ɗan jujjuya kanta acikin ƙirjinsa, hakan da takeyi ne yasa gaɓa ɗaya jikinsa yayi weak, wani irin abu ne yakeji na yawo ajikinsa, wanda zai iya rantsewa, cewa tunda yake aduniya bai taɓa jin irin hakan ba, wani fitinannen feeling yakeji, gefe guda kuma ga wani pleasure wanda ko sex suke da Ameena bai taɓa jin irin wannan pleasure da kuma feeling ɗin ba, babu abun dake neman zautar da tunaninsa kaman yanda tausassun laɓɓan bakinta ke gogan fatar ƙirjinsa,
A hankali ta ɗago kanta ta zuba mishi,ido shima idon ya zuma mata, goshinta na manne da haɓarss cikin Muryar me sarƙewa haɗi da sheshsheƙan kuka tace. "Nagode! Nagode!! Nagode!!! sosai Hamma Saif, tabbas ka taimakeni arayuwa, sanadinka gashi Baba Malam ya yafemin, nagode maka ƙwarai matuƙa, Allah Ubangiji ya biya maka buƙatunka na duniya da lahira, Allah yafaranta maka kamar yanda ka faranta min, Allahu rabbi ya gafarta maka zunubanka, kamar yadda kayi sanadin yafe min da Baba Malam yayi, tabbas kamin abun da kowa ya kasa min, nagode sosai Hamma S..a..i..f."
Kukane ya ci ƙarfinta, sai kawai ta sake rungumesa sosai. Ahankali yaɗan lumshe kyawawan idanunsa wanda suka soma runewa zuwa kalan ja, hannunsa yasa ya tallafo haɓarta, tare da ɗan ɗago fuskarta, hakan shi ya bawa fuskokinsu daman kusanci da juna, idanunsa wanda suke ɗan lumshewa kaɗan kaɗan ya zuba mata, ahankali ya matso da fuskarsa gareta har hancinsu na gogan na juna, goshinsa ya ɗaura kan nata hancishi na bisa tsinin hancinta haɗuwar numfashinsu waje ɗaya, shiya sanya suka lumshe idanunsu atare, ahankali laɓɓanta suka ɗan buɗe, saboda sheshsheƙan kukan da takeyi.
ɗan buɗe idanunsa yayi, kana ya ƙurawa kyawawan laɓɓanta, shanyayyun idanunsa, wani irin abune ke yawo acikin jikinsa, haka yakejin kamar ya kamo kyawawan laɓɓanta yayi kissing ɗinta,
Idonshi ya maida ya lumshe tare da É—an zaro harshenshi ya É—an lashi tattausan lips É—inta,
da sauri ta buɗe ida nunta, ganin haka sai kuma ys janye fuskarsa baya yana sakin wata irin ajiyar zuciya yayi kamar bashi ya lashi laɓaɓɓan nataba, ahankali itama ta ɗan janye jikinta baya, nan kan kafaɗansa ta ɗaura kanta, ahankali take sakin ajiyar zuciya, har yanzu kuwa idanunta basu daina zubar da ƙwalla ba, saidai acikin zuciyarta farinciki ne me tarin yawa, ji take kaman anyaye mata duk wata damuwarta ta duniya, yafiyar Baba Malam da na Hamma Saif yasanya tanajin kanta, awata sabuwar duniya ta daban.
Hannunta ta saƙala acikin nasa, yayinda hawayenta ke ɗiga akan kafaɗansa.
Ahankali yaɗan jingina bayansa da jikin kujeran motar, tare da lumshe idanunsa, numfashinta dake sauƙa akan wuyansa, shiya sanya yaji gaba ɗaya jikinsa ya sake, yayinda tsikar jikinsa keta faman mimmiƙewa, dama akan Zaleeha shi namiji ne me yawan feelings, yanzu da take ajikinsa kuwa shikaɗai yasan me yake ji.
Zaleeha kuwa daɗin jikinsa da kuma sassanyan ƙamshin turarensa dake shiga hancinta, su suka taimaka wajen bata wani irin nutsuwa na musamman, sake lumshe idanunta tayi, tana me busa masa iskan numfashinta akan fatar wuyansa.

Gaba ɗayansu sun shagala, babu wani wanda yake cikin tunaninsa, musamman ma Saifuddeen daya tafi izuwa wata duniya ta daban, tsayuwar motar ne yasasu buɗe idanunsu, gani sukayi har sun iso gida. Akunyace taɗan janye jikinta daga na Saifuddeen ɗin, nan ta ɗan gyara mayafinta dake ƙoƙarin zamewa. Sule driver kuwa cikin hanzari ya zagayo ya buɗe mawa Saifuddeen ƙofar motar, bayan ya buɗe bot ya zaro masa kekensa.
Cikin nutsuwa kuwa ya hau kan keken nasa, Zaleeha ma jikinta asanyaye ta fito daga cikin motar, idanu ta zuba masa ganin ya nufi part ɗinsa, kanta ta ɗan sunkuyar ƙasa, sannan ta share ɗan gun hawayen dake maƙale ƙasan idanunta, cikin ɗan sassarfa ta nufi part ɗin Ummi, tun kafun ta ƙarasa shiga falon, take ƙiran sunan Ummi, Raleeya dake zaune acikin falon ne ta ƙurawa ƙofar shigowa ido, musamman yanda taji Zaleeha nata faman ƙiran sunan Ummi.
Murɗa handle ɗin ƙofar falon tayi ta shiga, fuskarta ɗauke da murmushi da kuma hawaye, ganin Raleeya yasa ta tafi da gudu ta faɗa jikinta, ganin murmushi da dariya akan fuskan Zaleehan yasa, Raleeya itama ta saki murmushi, ɗago kai Zaleehan tayi, tace. "Raleeya Baba Malam ya yafemin, haka Ya Ahmad dasu Mamy ma duk kowa ya yafemin, Raleeya Hamma Saifuddeen ya zama garkuwa agareni, ayau ya bani duk wani farinciki, sanadiyarsa Baba Malam ya yafemin, yanzu Baba Malam baya fushi dani." ta ƙare maganan hawaye na zuba daga cikin idanunta.
Itama Raleeya Idanunta ne suka ciko da ƙwalla, murmushin jin daɗi ta saki, tare da ƙara rungume Zaleehan, cikin farinciki tace.
"Masha Allah Zaleeha natayaki murna ƙwarai, yanzu kema zakiyi rayuwa cikin farinciki."
Dai-dai lokacin Ummi ta fito daga ɗaki, dan tun tana banɗaki takejin ƙiran da Zaleehan keyi mata,
ganin Ummi yasa cikin sauri tatashi daga jikin Raleeya, ƙarasawa tayi da sauri kaman wata ƴar ƙaramar yarinya ta raɓa jikin Ummi, tana sakin dariya me haɗe da hawaye.
Cikin nuna farin cikinta tace.
"Ummi Baba Malam ya yafemin, hakama su Mamy, Ummi har Ya Ahmad É—ina ma ya yafemin, kuma yanzu basa fushi dani, Ummi Hamma Saif ne yayi min komai, saboda shine duk kowa ya yafemin, shikenan yanzu Baba Malam É—ina baya fushi dani."
taƙare maganan tana me sake rungume Ummi, sam ita bata ɗauki Ummi mazaunin suruka ba, ko yaushe amatsayin uwa take ɗaukanta, dan abun da za tayiwa Mama da Mamy shi zatayiwa Ummin, saboda acikin jininta soyayyar Ummin take.
Cikin farin ciki Ummi ta shafi fuskarta, tare da cewa.
"Alhamdulillah, tabbas kinzo da labari me daɗi, kuma naji daɗin hakan sosai, dama nasan ke ta gaban goshin Baba Malam da ya Ahmad ne, saboda haka yanzu kuka ya ƙare, idan kuma nasake ganin hawaye akan wannan fuskar to fa zamu ɓata, kindai ji kam."

Murmushi me kama da dariya tayi, kamo hannun Ummin tayi cikin sanyi tace.
"Nagode sosai Ummi haƙiƙa kin cika uwa tagari, samun irinki awannan duniyar zaiyi wahala, Inasonki Ummi na, dan Allah ki ƙara yiwa Hamma Saif godiya, duk ta dalilinshi ne Baba Malam ya yafemin, ku ɗin kunzama majingina agareni, sannan kunzaman to mini lema, wanda daku ne zan kare ruwa da zafin rana, nagode sosai!".
tafaÉ—i maganar tana sakin wasu hawayen farinciki, tare da sake rungume Ummin.
Murmushi Ummi tayi, sosai takejin soyayyar Zaleehan acikin ranta, tabbas tasan Zaleeha mutumiyar ƙwarai ce, kuma tasan bazata taɓayin danasanin samunta amatsayin suruka ba.
Hayatuddeen wanda tun ɗazu ya shigo falon, ƙarasowa garesu yayi, tare da haɗasu su duka ya rungume ta gefen Ummi cikin farinciki yace.
"Nima Inasonki Adda Zaleehan Hamma, saidai kuma zan iyayin kishi dake ako da yaushe, dan naga kaman kinason maidamin Ummi na taki ke kaÉ—ai."
Murmushi su dukansu sukayi.
É—an É—agowa Zaleeha tayi, tana share hawayen dake kan fuskarta tace.
"Ai dai kuma indai ina cikin gidannan Ummi tawa ce dan kai kayi ƙato. Ko Ummi?".
ta faɗa tana mutsutstsuka idanunta, hakan yasa tadawo kaman wata ƙaramar yarinya.
Ƴar dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa, amma fa saidai in kin ɗauki al'ƙawarin cewa bazaki sakeyin kuka ko abayan idanuna ba, sannan kuma kada kice zaki sakeyiwa Adda Maryam kuka, nasan kinsan cewa mamaci bayason kuka, addu'a kawai yake buƙata, saboda haka Adda Maryam addu'a take buƙata awajenki ba kuka ba, daga yau kuma banso na ƙara ganinki cikin ƙunci, tun da Baba Malam ya yafe miki, inason ki saki jikinki, ki zauna acikin ƴan uwanki, sannan kuma daga yau banason naga kina takura kanki kinji ko." Kanta ta jinjina alaman. "To." Murmushi Ummi tayi tare da shafa kanta, cikin kulawa tace. "Allah yayi muku al'barka, ya kuma baku zaman lafiya keda abokiyar zamanki."
sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa da ƴan yatsun hannunta tace "Ameen"
Hayatuddeen ne yaja hanunta suka dawo cikin falon, nan kusa da Raleeya suka zauna, kallonta yayi cikin nuna jin daÉ—insa yace.
"Wallahi Adda Zaleeha kinfi kyau idan kina murmushi, yanzu da kina murmushi bakiga yanda kikayi kyau ba, sannan kuma nasan yau da dare zamu buga game sosai tunda naga kina cikin farinciki ko?."
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ni dai bazan buga game da kai ba, abunda duk nasan halinka, rinto kakeyi, ranan ai naga kanata yiwa Raleeya rinto."
Ummi da Raleeya wacce waya takeyi da Raihana ne sukayi dariya, shikuwa Hayatuddeen murmushi mugunta yayi, cikin son tsokan Raleeyan yace.
"Adda Zaleeha bakisan wacece Adda Raleeya bane, itace fa bata iya game É—in ba, shine kuke ganin kaman rinto nake mata."
Hararansa Raleeya tayi tare da cewa.
"FaÉ—awa wanda baisan waye kai ba yaro,kowa ya sanka da rinto."
Nan dai dukansu suka ɗanyi murmushi, daga haka kuma suka shiga ɗan taɓa hira.
Chapter 83 · 0% Book details