← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 154

Sashe 8

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren Dalla kuwa aranan yaransa sukazo masa da labarin gano gidansu Zaleeha, harma da wajen aikinta, nan Dalla yacika da matsanancin murna, sai-dai kuma murnar tasa taso komawa alokacin da suka sanar dashi labarin aurenta da ake shirin ɗaurawa gobe, inda suka sanar masa cewar wani kurma kana gurgu zata aura, dariyan mugunta Dalla ya fashe dashi, inda yace.
  "Ta kwana gidan sauƙi" nan yatsara irin rashin mutumcin da zaiyi mata,  nan ya ƙudurta aransa cewa dazaran an ɗaura mata aure da gurgun mijinnata ayayin da ake ƙoƙarin ɗaukan aure alokacin shikuma zaisa yaransa su ɗauko masa ita, tabbas shine zaisha wannan romon budurcin, al'ƙawari yaƴiwa kansa cewa saiyayi mata dalla-dalla tayanda bazata sake moruwaba.

Saturday. 26/january/2019

Rana bata ƙarya.

Ranan yau takasance wata muhimmiyar rana awajen Saifuddeen da duk wani mai ƙaunarsa, haka ranan tayau takasance wata rana wanda Zaleeha bazata taɓa mantawa da itaba a iyaka tsawon tarihin rayuwarta, ayau ne baƙin cikinta yafi na koyaushe ninkuwa acikin zuciyarta, ayaune takejin tsanan kanta da rayuwa fiye da kullum, ayau tanaji tana gani zata zama mata ga ga wani ba wanda ya taimaketa ba zata zama matar wancan mutumin da kyawawan manyan idanunshi ke bata tsoro.

Federal lowcost.

9:30 am, gaba É—aya gidan nasu acike yake da jama'a, Æ´an uwa maza da mata haÉ—i da abokan ariziki, ko ina dake cikin gidan cike yake da mutane kowa ka gani fuskarsa É—auke take da zallan farinciki.
Can ɓangaren Saifudden nake jiyo hayaniyan mutane hakan yasa natafi don na duba meke tafiya acan, gaba ɗaya falon nasa cike yake da abokansa maza su, Ahmad, Jabeer, Ishaq, Saminu mijin Raihana, Wareesu, Saleesu, Mudassir, ibrahim, Rabi'u, Hisham, Jabeer da kuma abokanshi da sukayi karatu tare Hashim, Jafar,Abdulhakim. Gaddafi, Aziz da dai sauransu gaba ɗaƴansu sanye suke da tsadaddun shadda ƴan ubansu yayinda kowanne daga cikinsu yayi kyau sosai, gaba ɗayansu cike suke da farin ciki, domin dama ganin auren Saifuddeen ɗin shine cikar burinsu. dan duk da suna tare da taraddadin kar dai nakasar Saifuddeen tashiafi mazantakanshi to shiyasa ganin aurenshi shine burinsu.

Ahankali yake murza wheellchair ɗinsa, inda ya ƙarasa zuwa gaban dressing mirror, cikin nutsuwa yake shafawa haɗaɗɗiyar surar jikinsa body lotion, koda ya kammala cumb ya ɗauka inda yashiga taje lallausan sumar dake kansa, wanda ya kwanta luf-luf kamar ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, body spray ya fesa ajikinsa me daɗin ƙamshi, kana ya tura wheelchair ɗinsa zuwa kan gadonsa, inda anan ya aje kayan da zai sa.
Cikin yanayi na nutsuwa da alamun gajiya da ɗan kazar-kazar ɗinshi kamar yanda ya saba ako da yaushe ya zura dogon wandon haɗaɗɗiyar getzner mai kalan white ajikinsa, yana gama saka wandon ya sanya rigar wacce ta kasance half jumper, cikin nutsuwa ya ɗauko babban garen kayan wanda aka yajiwa wani irin fitinannen aiki da surfani blue colour mai masifar kyau, cikin nutsuwa ya zurata akan rigar tasa, lokaci ɗaya yayi wani irin azababben kyau mai tafiya da zuciya, ahankali ya zura wasu haɗaɗɗun toms ƙiran Italy aƙafafunsa masu azabar kyau da tsada, yayinda takalman suka kasance blue colour, wato kalan aikin garen jikinsa kenan, wasu tsadaddun links masu tsadan gaske yasanya ahannuwan rigar, kana yaciro wani tsadadden wrist watch mai tsananin kyau da tsada daga cikin wani ɗan ƙaramin box, agogon rolex ne me masifar kyau, ɗaura agogon yayi ahannunsa na dama tare da ɗaukan haɗaɗɗiyar hulansa mai tsada wacce take da kalan blue ajikinta yasanya, tare da dai-dai-ta zamanta akansa.
Tabarakallahu ahasanul khaliƙiyn! wani irin fitinannen kyau Saifudeen yayi wanda tunda yake bai taɓayin irinsa ba, gawani azababben kwarjini da yayi, wani irin ƙyalli da walwali fuskarsa keyi, sajen nan nashi yayi lib-lib akan farar fatar kekyawar fuskarshi, jajayen laɓɓansa sai sheƙi sukeyi tamkar ya shafa musu mai, gashin girarshin nan ya kwanta lib gwanin ban sha'awa, yayinda getzener ɗin jikinsa kuwa keta shinning, getzner ne me masifar tsada da kyau, wanda aƙalla kuɗinta yakai 95k, sosai kuma kayan suka amshi jikinsa.
cikin nutsuwa ya ƙarasa gaban dressing mirror, kallon kansa yayi acikin madubin tare da sakin murmushi, shi kansa ya aminta da kyawu haɗi da cikar halittan da Allah yayi masa, shiyasa akullum yake gode masa, tabbas Allah abun godiya ne, sam bazai iya fasalta matsanancin farin cikin dayakejin kansa aciki ba, yau zuciyarsa zata samu cikar muradinta, wani haɗaɗɗen parfumed mai ƙamshi ya fesa.
Kana ahankali ya danna madannin kekensa, kaitsaye ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, buɗe ƙofar yayi ya fito ahankali, idanu su Ahmad suka zuba masa, baƙaramin kyau yayi ba, wanda sukansu maza ƴan uwansa sun ƙyasa da gayun nasa inaga mata kuma? sosai suka shiga yaba tsantsar kyawun nasa, inda Ishaq keta tsokanansa, shidai Saifuddeen sai murmushi kawai yakeyi don kuwa yau yana cikin farin ciki, nanfa dukansu suka shiga yi masa hoto, bayan sun gama yi masa hotonne kuma suka shiga ɗaukan selfie dashi, inda sukayi kyau sosai, zuwa lokacin ƙarfe 10 har da kusan rabi tayi hakan yasa suka ɗunguma sukai waje, don kuwa ƙarfe 11 dai-dai ne za a ɗaura auren.
A falon Ummi kuwa tana ganin fitowansu ta ratso gefe tana zuwa Adda Rahma da Raihana da Raliya suka biyo bayanta, kanshi ta dafa tare da cewa.
"Allah ya bada sa'a Babana , yau kayi kyau sosai irin kyan da ban taɓa ganin kayiba."
Amin Amin sukace baki ɗanyansu, shi kuwa Saifuddeen alama ya mata da ya gode, su Adda Rahama kuwa selfie suketayi dashi. gannin zasu ɓata lokacine Salisu yace.
"Adda Rahma ku barmu mutafi".
to tace kana suka barsu.
Acan compound É—in gidan kuwa su Hayatudden da abokansa ne tsaye, sosai matasan yaran sukayi kyau cikin shigarsu ta shadda sky blue wanda yayi masifar amsarsu, dukansu cike suke da farin ciki inda suketa É—aukan hoto da sabuwar wayar ta Hayatudden iphone 7+ wanda Saifuddeen ne ya saya masa, fitowar su Saifuddeen yasa dukansu suka maida hankalinsu garesu, tuni Hayatuddeen ya shiga santin irin kyawun da Hamman nasa yayi, nan yashiga É—aukan Hamman nasa hoto, daga bisani kuma yashiga yi musu selfie.
Cikin yanayi naɗan sauri sauri kowanne ya nufi mota don kuwa lokaci nata ƙurewa, wata zazzafar RANGE ROVER black colour sabuwa dal mai azabar kyau da sheƙi da ƙyalli Saifuddeen ya shiga, wanda musamman ya sayeta saboda da ita yakeson yin hidiman biki, Ishaq ne yashiga gefensa ya zauna, su Ahmad kuwa kowa motarsa ya shiga hakama sauran abokansa baki ɗaya dan babu ƙaranta, yayinda aka warewa Hayatuddeen da abokansa motarsu guda ɗaya zazzafa wanda suma da ita zasuyi chilling ɗinsu wajen bik.
su Baffa Ali da Malam Ashiru kuwa wata haɗaɗɗiyar mota ƙiran mercedes suka shiga don sune suke matsayin iyayen ango, Dirankaɗi ma yazo da abokansa, inda su Alhaji Khabeer da Alhaji Ibrahim, haɗi da Alhaji Ishaq Ba miskila, San Husssain Alhaji Yawale Alhaji Aliyu mai dilan leda Malam Habu dama sauran manyan ya kasuwa duka Ya Rabi'u ma yayan Ishaq na Abuja yazo haka Dr Aliyu .Ya Adnan da abokan
shi hakama bappa Ali da abokanshi da abokan Abbansu Saifuddeen suma sunzo don halartan É—aurin auren, gaba É—aya haka motocinsu sama da talatin da biyar suna jera reras akan titi line by line haka suke tafiya cikin nutsuwa.
Duk inda jeren motocin suka wuce sai anbisu da kallo ahaka har suka isa cikin unguwar NEW G.R.A, can gefe sukayi parking motocinsu, don kuwa ƙofar gidan su Zaleeha cike yake da mutane maƙil, manyan malamai, manyan ƴan kasuwa, da kuma ƴan siyasa duk sun samu zuwa ɗaurin auren, saboda Baba Malam mutum ne da sunansa ke yawo acikin Nigeria, kusan kowa ya sanshi, kana ga Yaya Ahmad da sanadinshi yasa pilot suka rinƙa dirowa birnin gombe da jiragensu dan halartan ɗaurin auren ga kuma sojojin da ys Aminu suma sun gayyato nasu mutanen. Raveel ma ya gayyato duk abokan aikinsu.
Isowar su Saifuddeen yasanya gaba É—aya kallo ya dawo kansu, kowa kallon Saifuddeen yakeyi, wanda nagarta haÉ—i da haiba da kwarjini da kamalarsa ya cika idanun mutane, sam basai an faÉ—a maka ba da kallonsa zakagane cewa shine angon, sai-dai kuma da yawa suna mamakin kasancewarsa gurgu.
Cikin mutunta juna Baba Malam da tawagarsa suka amshi su Saifuddeen, kamar yanda lokaci baya jinkiri wajen zuwa 11:00 am dai-dai dubbanin jama'a suka shaida É—aurin auren SAIFUDDEEN Muhammad Ahamad Dukku da kuma ZALEEHA Bashir Sulamain Dukku akan sadaki naira dubu É—ari...!

Littafina na kuɗine duk wanda ya fiddamin shi aradun Allah yaseeeeeeeen doooooooguwa buluƙutu baƙar mutuwa!

*BY*
*GARKUWAN FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: *Wannan shafi nakine kyauta gareki kekyawar Æ´ar jaridar vison FM Gombe inai miki fatan al'khairi Zaleeha Babangida Hari mai shirin Babu Nakasasshe sai rago, dake da jonapwd gombe inai muku fatan al'khairi godiya ta musamman gareka malam ishaq*

_ZAIBA MASU KARATU KADA KU SAKE A BAKU LABARI BIYA ƊARI 200 KACAL ki samu littafin Zaiba na Ummee Garkuwa littafi ɗaya maidarrusa da dama karanta Zaiba kisha dariya tausayi shauƙi bege ƙauna karanta Zaiba kisha barkwanci Sufi ga masu buƙata ku nemi Ummee Garkuwa 08037251895 ta wannan number_

Wani irin matsanancin farin ciki ne mai tarin yawa ya cika zuciyar Saifuddeen, haƙiƙa yau takasance rana ta mussaman agaresa ranan da bazai taɓa mantawa ba acikin ƙuɗɗin tarihin rayuwarsa, cikin ikon Allah yau gashi Zaleeha ta zamo mata agaresa, zata rayu cikin ƙarƙashin iko da damansa, zata zama itace aƙasansa ta tabbata matar nakasasshe, wani irin ƙayataccen murmushi kawai Saifuddeen ke sakewa, hakanan yakejin kansa dai-dai da kowani cikakken namiji,  cikin son tayasa murna Mutane suka dinga bashi hannu suna musabaha, kowa sai Allah yasanya al'khairi yakeyi masa,   haka yadinga amsar hannun mutane masu tayasa farinciki, hatta Ahmad da bawani son auren yake sosae ba yau yayi farinciki saboda auren Saifuddeen babban abune awajensu.
Kasancewar al'adan Æ´an Gombe ne yin receiption bayan an gama É—aurin aure to hakanne takasance ga Saifuddeen domin kuwa tuni sun tsara haÉ—aÉ—É—en receiption wanda zasu koma gida shida abokansa da kuma wasu daga cikin jama'ar É—aurin auren don suyi, haka suka shiga mota aka nufi gidan nasu Saifuddeen.
Chapter 8 · 0% Book details