← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 154

Sashe 23

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

koda suka ƙarasa cikin kitchine ɗin, hayewa kan wata kujera Hayatuddeen yayi ya zauna, wayarsa ya fiddo daga aljihunsa tare da soma latsawa, ita kuwa Zaleeha, direct wajen fridge ta nufa, buɗe cikin firjin dake shaƙe da kayayyakin abinci tayi, nan ta zaɓo manya manyan kaji guda biyu,  sake wankesu tayi sannan ta ɗaura akan wuta tare dasa kayayyakin ƙamshi dana danɗano.
nan ta ɗibo irish patatoe tasoma ƙoƙarin ferewa,  Hayatuddeen ne ya taso tare da soma taya ta,  haka suka cigaba da firan, yana ta zuba mata surutu,    mayafin dake jikinta ta ajiye, tare da soma yin aikinta cikin nutsuwa, yayinda Hayatuddeen gaba ɗaya ya sakota gaba da surutunsa,  cikin abun da bai wuce awa ɗaya da rabi ba, ta kammala haɗa barbecued chicken da kuma patotoe balls,  sai kuma bread Pizza, wanda gaba ɗaya ƙamshinsa ya cika kitchine ɗin, Hayatuddeen dake zaune agefe sai haɗiye miyau yake, dan har ya tsara irin cin da zaiyiwa bread pizza ɗin, da ƙamshinsa ya cika masa hanci, spearmint tea ta haɗa, sannan ta juyesa acikin flask, nan ta kimtsa gaba ɗaya kayan akan wani babban tray, duban Hayatuddeen tayi tare dayi masa alama akan yazo ya tayata ɗauka, aikuwa shi ya kwashe komai inda ya jere musu break fast ɗin akan dinning table, ita kuwa Zaleeha har yanzu tana kitchine, fruit salad ta haɗa, inda ta zubashi cikin wani babban glass bowl, tunanin haɗa chocolate fudge cake ne yazo mata, nan ta duba taga akwai komai na buƙata, kanta ta jinjina, sannan tashiga ƙoƙarin haɗawa, cikin mintuna ƙalilan kuwa ta kammala, ita kanta saida tayaba da ƙamshin chocolate fudge cake ɗin, Hayatuddeen dake falo kuwa koda ƙamshin yaje masa, saida yakasa haƙuri ya biyota zuwa kitchine ɗin, ganin, fudge cake ɗin yasan yashi cewa.
"Wow fantastic, Aunty Zalee dama wai kin iga girki har haka ne?, na É—auka a faÉ—a da masifa chart da zuwa wurin aiki kawai kika iya."
Hannu tasa takai masa bugu, da sauri ya kauce yanayi mata dariya, hararan wasa ta watsa mai, tare da cewa. "KaÉ—auka yanda kuke sakarkaru kaida Zakariyya haka kowa ma yake ne baku da aikin sai yawo a gari dama tsokana da ci."
Taƙare maganar tana me miƙo masa, wani haɗaɗɗen tray wanda ciki tashirya chocolate fudge cake ɗin, amsa yayi yana wani malau malau da baki, tare da cewa.
"Hmmm ai yanzune ma zakuga tashen jami'a zakusha mmki bari dai in gama sabawa da jami'ar kin san banfi sati É—aya da fara zuwa ba."
Dariya ta É—anyi tare da cewa.
"Yo ai da an ganka ansan kanka na fizga da igiyar iskar sabin shiga jami'a ka dai yi a hankali yaro dan ita jami'a gidan ban kashine."
Murmushi ya É—anyi tare da cewa.
"Gobe zan kawo miki sabon abo kina Khamis ku gaisa. kiga irin salon takun mu, yaseen ki kuma cewa mijinki ya saya min mota.
Dan ni ba yaro bane da za'a rinƙa kaini ana ɗaukoni kamar wani ɗan primary ko kayan wonki da za'a rinƙa kaini ana ɗaukoni".
Ya ƙarishe mgnar yana wuce zuwa dinning, food flask ɗin dake gefenta wanda ciki ta shiryawa Raliya abinci ta ɗauka.
Koda ta fito falo, nan ta iske Ummi, da kuma Saifuddeen, da Ahmad, Hayatuddeen kuwa tuni ya baje kan dinning, inda ya turo baki gaba, wai don saboda yace suzo suci, sunce yajira Zaleehan tagama sai suci tare, sam shi gaba ɗaya yaƙosa yaji yana tauna abincin, musamman ma da ƙamshin abincin ya cika masa hanci.
Zaleeha na fitowa daga kitchine É—in ta dubi Hayatuddeen, fuskarta É—auke da murmushi tace.
"Autan Ummi sarkin ci!."
Baki Hayatuddeen yaƙara turowa gaba, ashagwaɓe yace.
"Eh naji, amma please kice musu suzo muci, I swear am feeling hungry fa!."
yafaɗi maganar yana me shafa cikinsa, wanda hadda ganin abincin ma yaƙara masa jin yunwa.
Murmushin daya bayyana zallan cute face É—inta tayi, tare da girgiza kanta.
Ummi ne tayi murmushi tare da duban Zaleehan, cikin so da ƙaunar yarinyar tace.
"Sannu da aiki, Allah yasaka miki da al'khairi, ya kuma baki Æ´aÆ´a masu al'barka, wanda zasuyi miki fiye da haka."
SaÉ—a kai kasa Zaleeha tayi tare da É—an sakin guntun murmushi a kunyace murya a sanyayaye tace,
"Amin Ummi."
Saifuddeen kuwa a fakaice ya ƙura mata idanu, yana kallon duk wani motsinta sosai yake mamakinta, har yau har yanzu ya rasa ita wace irin mutum ce mai fuska biyu da jujjuyawa tamkar hawainiya, ji yanda take ta murmushi tare da sakewa dasu, tanayin komai kamar wata wanda keson zama dasu da gaske.
Shi mamakinta ma yake, tawani irin sakewa sai kace ba itace, su keta gantalin nema ba jiya.
Kawar da kansa yayi daga kallonta, tare da maida hankalinsa, ga laptop É—insa,
wanda a zahiri laptop yake kallo a baÉ—iri kuwa fuskata yake kallo ta cikin madubin system É—in,
rumtse ida nunshi yayi a hankali tare da sauƙe nannauyan ajiyan zuciya,
"To ina take zuwa ta kwana dasu waye take kwana, me take aikatawa a inda take kwanan?."
haka yaji waɗannan tambayoyin sun cika mishi zuciyarshi dake cike da azabebben kishi, gaba ɗaya ya rasa wani irin kishi Allah ya ɗora mishi a kanta ji yake tamkar zai faɗi ya mutu dan baƙin ciki.
Ahmad kuwa dubanta yayi tare da sakin murmushi, cikin ransa yayi ƙwafa, ahankali yace.
"Zaki sanine yarinya."

Duban Ummi Zaleeha tayi tare da É—an rusunawa, cikin nutsuwa tace.
"Ummi bari na kaiwa Raliya abincinta, tunda batajin daÉ—i nasan ba lallaine tasamu fitowa ba."

Sosai Ummi taji daÉ—in kulawan da Zaleehan ta nuna ga Raliya'n, amma sai tace.
"A'a Zaleeha da kanki, bazaki bari Hayatuddeen yakai mata ba."
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Bakomai Ummi, kinga Hayatudeen É—in yace bazai iya komaiba sai yaci abinci,inaga bazai iya matsawa akan dinning É—innan batare daya lodawa cikinsa abinci ba, kin sanshi acicine kazar birni!."
Zaleehan tafaÉ—a tana kallon Hayatuddeen, ba iya Ummi ba harta Ahmad saida yaÉ—anyi murmushi sabida sunan data kira Hayatuddeen Acici kazar birni, Ummi ce tace, idan takaiwa Raliyan abincin ta dawo suci abincin, nan tace zasuci da Raliyan acan.

Koda ta ƙarasa ɓangaren Raliyan, akwance ta isketa, nan ta shiga ɗan kimtsa mata ɗakin, daga nan kuma ta zuba musu abincin inda suke ta hira ita da Raliya'n sosai Raliyan ta sake da ita har taji ciwon kan nata ya saketa.

A falon Ummi kuwa, tuni Ummi tayi serving É—in kowa, nan fa Hayatuddeen yasoma kai loma, yana me jijjiga kansa.
Saifuddeen kuwa ahankali yake tsakuran abincin yana kaiwa bakinsa, idanunsa kawai yake lumshewa sabida ƙuna da zuciyarshi keyi na kishi,
tabbas ya yaba da iya girkinta domin sosai abincin yayi masa daɗi, sam koda wasa bai taɓa tunanin cewa Zaleeha ta iya girki har haka ba.
Ummi ma sosai ta yaba da abincin,
Hayatuddeen kuwa cikin santi ya É—ago kai inda ya dubi Ahmad, cikin halinsa na tsokana yace.
"Wallahi Aunty Zalee ta iya abinci, mai daÉ—i kaman kunnena zai fita, hmmmm ai daga yau ita zatana mana girki, don sosai tafi su wance iyawa."
Dariya ne ya ƙwacewa Ummi, dan tasan tabbas Hayatuddeen dan tsokana yayi maganan da Raliya yake.
Harara Ahmad ya watsa masa tare da taɓe baki, cikin nuna cewa shima matarsa gwanace yace.
"Oho dai, da makaho ya rasa ido sai yace da wari, wannan har wani abinci ne, an haÉ—amu da tarkace saikace wasu yaran larabawa, jifa wani cake na chocolate, ko ance mu yaran larabawa ne, ai dai Raliya tafita iya girki ko Ummi."
Ahmad ya faÉ—a yana me duban Ummi.
Murmushi Ummi tayi tare da gimtse dariyarta, ita dai bata da tacewa, to ma mezatace komai tace yanzu zasuce tayi sonkai.
Hayatuddeen kuwa dariya yadinga yi, don yasan maganan Ahmad ɗin, a iya laɓɓan baki kawai take, ba taje zuci ba, ya faɗane kawai don ya kare matarsa, amma yasan cewa koma waye yaci girkin dole ya yaba, musamman ma spearmint tea ɗin dake ta ƙamshin kayan haɗi, uwa uba kanasha kanajin wani irin ɗan ɗanon zuma aciki.

Ahaka suka kammala cin abincin, inda Ummi tasa Hayatuddeen ya kwashe kwanukan yakai kitchine.

Acan gidan Baba Malam kuwa, tuni Baba Malam ya ƙira Habu, inda yace yaje gidan Zaleeha ya taho masa ita.
Babu ɓata lokaci kuwa, Ya Habu yashiga cikin motarsa, kai tsaye ya nufi gidan su Saifuddeen.
Chapter 23 · 0% Book details