Sashe 134
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan sun fitone ta maida kayan jikinta tasa hijabi, kallonshi tayi tare da cewa.
"Saida safe zanje in kwanta".
Ogogon dake jikin É—akin ya nuna mata,
da sauri tace.
"Ƙarfe biyu da rabi".
Kanshi ya gyaÉ—a mata a hankali tace.
"Ni dai bazan kwana a nanba".
Jawo hannunta yayi ya kontar da ita, tare da mata alaman kwana kuma na nawa.
Hira suka ɗanyi kana bacci ya kwashesu, kiran sallan forko a kunnenshi. Da kyar ya lallaɓa yayi wonka da al'wala kana ya fito ya tada ita,
ya rubuta mata ta tashi ta tafi tunda bata son asan tazo, ya ƙara da ce mata in taje tayi salla ta kawo mishi kayan da zaisa.
sanna ta haÉ—o mishi wanda zai tafi dasu ta kuma haÉ—a mishi da system É—inshi.
Hakan kuwa akayi
Ƙarfe shida dai-dai duk suna falon Ummi Ishaq ma yazo,
Ahmad ne ya kalli Zaleeha tare da cewa.
"Ko dai za'a bar miki Adeel ne?".
Da sauri ta gyaÉ—a kai alamar eh.
murmushi sukayi baki É—aya kana Ummi tace.
"Ahmad ku tafi ina kunje jirgin karfe bakwai zai tashi".
To Ahmad yace kana duk suka mimmiƙe,
Ameena ce ta karɓi Adeel tare da cewa.
"To Ammin Adeel sai mun dawo".
Cikin sanyi Zaleeha tace.
"Allah ya kaiku lfy yasa ku dawo lfy".
Amin Amin sukace baki É—ayansu kana suka nufi hanyar fita,
Shi kuwa Saifuddeen gefen Zaleeha ya koma ganin hakane yasa suka fita suka barsu.
A hankali ya kamo hannunta duka biyu, mannasu yayi da fuskarta a hankali ya mata alamun zamu tafi.
haka nan taji rauni ya rufeta a hankali ta faÉ—a jikinshi cikin rawan murya tace.
"Ban san me nakeji a kankaba,
inaji bana son kayi nesa dani,
hakanan na fara kewarka tun kafin ka tafi,
inama ace zaka jini da na gaya maka yadda nakeji a zuciyata,
ban taɓajin begen rabuwa da waniba a duniya sai kai,
Hamma Saif anya zan iya jure tsawon wani lokacin ban gankaba,
Ban san meyasaba bana gajiya da ganinka,
bansan yaushe mukayi shaƙuwar da har nakejin cewa kaine farin cikina ba".
Wani irin fitinenne runguma Saifuddeen yayi mata shi kaɗai yasan irin daɗin da yakeji a cikin rai da jikinsa dama dalilinshi kenan na ɓoye mata warakarshi,
kanta ya É—an tallafo ya haÉ—a da nashi suna kallon juna murya a sanyaye tace.
"Ina roƙon Ubangiji mai dukkan isa daya kaiku lfy ya dawo daku lfy, zanyi tayi maka addu'a a cikin dukkan sallolina, Allah ya baka lfy ya dawo mana daku lfy".
Kissing lips É—inta yayi ganin yadda suke rawa, alamun tana gab da fashewa da kuka.
rungume juna sukayi tare da sauƙe ajiyan zuciya a tare,
sun kai 3 minute a haka kafin ya saketa,
kana ya jawo hannunta suka fito.
A harabar gidan su ka samesu baki É—ayansu, nan suka sallamesu suka tafi
Yayinda su kuma suke tayi musu addu'a. Saida sukaga fitansu kafin suka koma cikin gida.
Ita kam Zaleeha side É—inta ta wuce.
Su kuwa bakwai dai-dai jirginsu ya tashi
Sun isa Abuja lfy,
Ƙarfe ɗaya da rabi sukayi sallan azahar biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga daga Abuja Nigeria zuwa New Delhi India.
Sun jima suna keta gajumare kafin suka isa india, inda suka sauƙa a babban birnin india wato New Delhi, inda tuni dare ya fara nisa,
Suna sauƙa a airport ɗin
*INDARA GANDHI international airport New Delhi*
Bayan duk sun firfito, suka samu Dr Malik Khan da kanshi yazo tarbansu, sabida yasan isan dare zasuyi, daga airport ɗin tafiya kaɗan sukayi suka isa babban hotel ɗin Hyatt regency Delhi, wanda yake kusa da asibitin da za'a duba Saifuddeen.
Kusan Dr Malik ne ya musu komai, hatta sim card ya sayawa Ameena dan sauƙaƙa musu, kuma ya kama musu masauƙi mai kyau a ƙasa,
Saida yaga an kawo musu komai da zasu buƙata, sannan ya sallamesu a kan sai da safe zaizo ya ɗauke su.
Yana fita sukayi wanka suka ɗanci abinci, kana suka konta dan tafiya dai duk sunanta tafiya tanada gajiya. Shiyasa suna kwanciya sai bacci.
Washe gari da safe bayan sun gama komai, Dr. Malik yazo ya ɗaukesu,
Kai tsaye asibitin suka nufa,
Sosai Ameena tasha mamakin ganin irin cigaban da suke dashi daga matakin ma'aikatansu da kuma na kayan aiki.
Suna zuwa manya likitoci suka ƙarɓeshi matakin forko goje-goje aka fara yi mishi, ginin MRI scanning da kuma X-ray, CT scan MRI ɗin da sauransu.
Alhamdulillah dukkan goje-gojen da zasuyi suna samun karsashi kan aikinsu, domin ciwon da bayanshi keyi su farin cikine a wurin su, bayan da, da ko reza za'a a yankeshi bazaijiba sai gashi yau kuma yana kukan bayan alamun nasarane babba a wurin.
Kwana uku akayi ana gwaje-gwaje kana ran na huÉ—u, duk sakamakonsa zai fito ta hannun doctors É—in da suka dace.
Shi kam Saifuddeen yanzu gaba ɗaya ma a asibitin yake, Ameena ce dai kan koma masauƙinsu itama gari na wayewa zata dawo asibitin.
A gida Nigeria kuwa sosai su Ummi suka sha mamakin lamarin Zaleeha, dan ko bata faɗaba ana gane tana cikin kewa, duk ta ƙara zama shiru-shiru, tunda suka tafi batayi mgna da shiba, tana dai jin lbrinsu a wurin Ummi, amman kullum sai sun gaisa da Ameena takan tambayi ya mai jiki.
Yau Rashida ta kawo mata ziyara dan yaune za'a kai lefenta bisa al'adar gombawa kuwa in za'a kai lefenki zaki ɓuya.
To shiyasa yau É—in tazo wurin Zaleeha.
Zaune suke bayan sunyi sallan la'asar hira sukeyi tayi kan batun auren, jin wayar Rashida na tsuwane yasa suka ɗan tsagaita, amsa kiran tayi tare da karawa akan kunnenta, ahankali tace.
"Barka da yamma Ya Habibi".
Daga can gefen Ishaq kuwa gyara zama yayi tare da cewa.
"Barka dai Matar kirki, wato dan kinji za'a kai lefe ne kika gudu ko?".
dariya ta É—anyi kana tace.
"A a ba guduwa nayi bafa gani gidan Zaleeha".
Dariya ya É—anyi kana yace.
"Kice gidan gwauruwa, bata waya mugaisa".
Miƙawa Zaleeha wayan tayi wacce ita kuma ta maida hankalinta kan wayarta.
jin ta kara mata waya a kunnenta ne yasa ta É—an É—ago, jiyo muryar Malam Ishaq na ce mata.
"Zaleeha ya gida ya labarin mutanen India?".
Kai ta É—an rausayar tare da cewa.
"Gidan ba daÉ—i Malam Ishaq, tunda Adeel ya tafi bana jin daÉ—in gidan.
Mutanen India kuma banyi magana da suba, sai dai naji labarin yau zasuga Dr.Mahesh Deera".
Cikin nitsuwa Ishaq yace.
"Eh gaskiya koni tunda yaje bamuyi magana da shi ba, sai dai ina jin labarinshi wurin Dr.Malik, sabida a sabiti yake woyoyinshi kuma suna masauƙinsu, amman ana zaton gobe zasu fito dashi".
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Dama ɓoyeshi akayi ne?".
Dariya ya É—anyi kana yace.
"Eh to kusan haka dan likitocin physiotherapist suke dubashi a tsawon kwanakin, saboda sune ke ƙoƙarin farfaɗo da aikin lakar ga wanda akaiwa aiki.
To sun bada yaƙinin yanzu kulawarsu yake buƙata, shiyasa suka duƙufa kanshi, kuma Alhamdulillah sunce yanzu bayan nashi da sauƙi sosai".
Ajiyan zuciya mai ƙarfi ta sauƙe tare da cewa.
"To Allah yasa mudace ya bashi lfy".
Amin Amin yace kana yace ta bawa Rashida waya nan yake ce mata anjima zaizo ya É—auketa.
Randa sukayi kwana biyar da tafiya a ranar Saminu da Raihana suka koma KD.
To Alhamdulillah shiyasa Zaleeha ta É—an samu sakewa a tsakiyar gidan dan ta lura sam Raihana bata sonta.
Yau kwanansu bakwai a India kuma yaune Dr Acash prasat ya shigo New Delhi da Doctor'n, da zai ƙara duba Saifuddeen.
Bayan duk sun gama aune-aunensu ne,
suka nufi wani É—akin kuma da Saifuddeen, kafin su wucene Dr. Malik Khan ya kira Ameena aka wuce da ita.
A wani É—aki na musamman aka shiga dashi Ameena kuwa Office É—in Dr. Acash prasat suka nufa ita da Dr. Malik.
Su kuwa sauran Doctors É—in suna shiga,
Dr. Arjun ya kalli Saifuddeen cikin kula yace ya tashi zaune.
yunƙura yayi tashi jin bayanshi sakayau ba azabebben ciwon da yake jine yasashi yunƙurin miƙewa tsaye.
Kusan atare Doctors ɗin suka bashi hannunsu da nufin ya riƙe,
kai juya alamun su bari, miƙa tsawonshi yayi ya tsaya cur kan ƙafafuwan shi, sai dai ƙafafuwan sai rawa sukeyi kar-kar.
Tafi sukayi a tare domin wannan shine matakin nasara,
wasu rubuce-rubuce sukayi tayi a na'urorin dake gabansu,
Dr Acash prasat kuwa kiran Dr Aleeyu yayi video call ya saita komai yadda zaiga Saifuddeen a tsaye car da ƙafafuwanshi,
kabbara Dr Aliyu yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah jiki yayi sauƙi da izinin Ubangiji".
Kai Dr. Acash ya gyaÉ—a mishi alamun haka.
Bayan sun gaba duddubashine sukace ya gwada takawa da ƙafafuwanshi, to amman ina ya kasa ɗaga ƙafafuwan dole suka haƙura, nan suka bashi magunguna da allurai na tsawon sati uku, cur wanda kullum sai an mishi allurar biyu ɗaya da safe ɗaya da yamma,
Alluraine da ko wanne ɗaya kuɗinshi ya kai dubu ɗari da ashirin. Nan suka bashi damar komawa masauƙinshi.
Koda suka fito suka dawo Office É—in Dr Acash inda suka samu Ameena da Dr Malik.