← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 154

Sashe 64

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke dukansu afalon Ummi suna hira, lokacin dawowar su Saifuddeen da Ahmad kenan daga sallan magriba.
Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, jikinta amatuƙar sanyaye.
Da mamaki Ummi ke kallonta, dan kuwa tasan bayanzu ne lokacin dawowanta ba, kasancewar duty'n dare takeyi sai nanda kwana uku zata koma na rana, cikin kulawa Ummi tace. "Ameena lafiya kuwa naganki haka asanyaye."
Hawaye ne suka zubo daga cikin idanunta, hakanne yasa hankalin su Ummi tashi, hannu Raliya tasa ta amshi Adeel dake riƙe ahannunta, cikin sanyin murya tace.
"Ummi É—azu fi ta na aiki nasamu ankai Adda Maryam É—in su Zakariyya haihuwa, kuma bazata iya haihuwa da kanta ba, sabida yaron ya rasu a cikinta sai anyi mata theater, kuma anyi mata theater'n, an ciro É—an ba rai, bayan anfito da ita daga É—akin theater'n ne kuma Allah yayi mata rasuwa, Ummi Adda Maryam É—in su Zakariyya ta rasu."
Ta ƙare maganan tana kuka, don dama ita akwaita da tsoron mutuwa, kona wanda bata sani ba ma kuwa. Salati su Ummi suka sa, cikin matsanancin tashin hankali Ummi tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Maryam ta rasu? Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!." taƙare maganar hawaye nabin kan fuskarta, Raliya ma salatin tayi take kuma sai idanunta suka kawo ƙwalla, Kuka Ummi ta fashe dashi, tare da sanya hannu ta rufe fuskarta, haka nan rasuwar maryam ya daki zuciyarta, yatuno mata rasuwar Abbansu Saifuddeen da Ya Nuruddeen ɗinsu sosai kuka yaci ƙarfinta.
Saifuddeen kuwa hankalinsa ne ya tashi matuƙa, sakamakon jin rasuwar Adda Maryam ɗin, Ahmad ma dake gefe shi da kansa saida yaji ƙwalla a idanunsa, saboda alokacin bikin Zaleeha da Saifuddeen sosai suka ɗan saba da Adda Maryam ɗin, kasancewar itace ta tsaya akan duk wani abu da ya shafi bikin, macece me sauƙin kai, da sakin fuska.

Hayatuddeen ne ya shigo falon afujajan fuskarsa gaba ɗaya tayi caɓa caɓa da hawaye, dan yanzun Zakariyya ke sanar dashi, rasuwar Adda Maryam ɗin, yazo faɗawa su Ummi kenan ya iske su ahaka, faɗawa jikin Ummi yayi tare da sakin kuka, cikin kukan yace.
"Ummi dagaske Adda Maryam ta rasu, yanzu Zakariyya ke faÉ—amin, Ummi Zakariyya kuka yake sosai har kaman zai shiÉ—e."
ɗan shafa bayansa tayi, tare da ciresa ajikinta, dan kukan nasa, ƙara mata nata kukan zaiyi.
Duban Saifuddeen wanda yayi ƙasa da kansa tayi, kana ta kai duban ta ga Ahmad, cikin sanyin murya tace. "Ahmad kuje can gidan Baba Malam ɗin da Saifuddeen"
Jin jina kai Ahmad yayi, nan ya miƙe tsaye, zunbur Hayatuddeen yayi tare da cewa zai bisu, basu hanashi ba, haka suka shiga mota, kai tsaye suka nufi gidan Baba Malam, zuciyoyinsu cike da alhinin abun da ya faru.

Ummi kuwa miƙewa tayi ta shige ɗaki, dan taji mutuwar Maryam din sosai, tabbas Maryam yarinyace me hankali, da kuma daɗin zama, uwa uba mutunta na gaba da ita, Ameena ma asanyaye ta koma ɓangarenta, Raliya kuwa bayan Ummi ta bi, ɗauke da Adeel akan kafaɗanta.

Koda su Saifuddeen suka isa gidan, Ya Habu wanda idanunsa suka kumbura shi yayi musu jagora zuwa falon Baba Malam, domin anan gaba ɗaya mazan familyn suke tare, sun saka gawan agaba suna tayi mata karatun alƙur'ani, bayan sunyiwa Baba Malam ɗin ta'aziyya da kuma Ya Ameenu wanda har yanzu idanunsa ke tsiyayar da hawaye, nan dai sukayiwa sauran jama'an dake cikin falon gaisuwa, alƙur'anin suma suka ɗauka suka soma karantawa, muryan kowa na tashi amma banda na Saifuddeen, danshi koda yaushe saidai yayi karatunsa azuciyarsa.

Can Abuja kuwa, Ya Ahmad hankalinsa amatuƙar tashe yake, yayi kuka harsaida yaji numfashinsa na ƙoƙarin ƙwacewa, haka Aunty Lubna ma tsakaninsu babu me rarrashin wani, sam baiduba cewa dare yayi ba, haka ya haɗa kayansa, inda yasa Aunty lubna ma tahaɗo nata kayan dana yaransu, duk da ƙaramin yaronsu data ƙara haihuwa, nan suka zuba yaransu amota suma suka shiga, kaitsaye suka kama hanyar Gombe, dan bayajin zai iya bari har gobe kafun ya taho, gaba ɗaya ma ya manta da wani batun hawa jirgi, ya ƙudurta aransa cewa bazai taɓa tsayawa ba harsai ya gansa acikin garin Gombe, haka yake tuƙin mota yana hawaye, tsananin tausayin mahaifinsu yakeji, dan yasan Baba Malam ɗin saiya fisu jin mutuwan Maryam ɗin, saboda kowa yasan Baba Malam, to yasan akwai ƙauna me zafi tsakanin sa da Maryam, daga gefe guda kuwa idan ya tuna da ɗan uwansa Ameenu, sai yaji kukan nasa ya tsananta, saboda yasan mutuwar Maryam ɗin zata wujijjiga Ameenu, domin kuwa yasan Ya Ameenu'n nayiwa Maryam wani irin ninkekken so.

Zakariyya kuwa wanda yasha kuka har dana fitar hayyaci ne, ya jawo wayarsa, number'n Zaleeha ya nema tare da danna mata ƙira.
Dai-dai lokacin kuwa Zaleeha na kwance akan ƴar katifarta, gaba ɗaya yau ɗin tun safe tarasa mekeyi mata daɗi, hakanan take yawanjin faɗuwar gaba, da kuma tsinkewar zuciya, wanda bata san dalili ba, saidai addu'a kawai take ta yi abakinta, kasancewar kwana biyun Balkeesu na yawan matsa mata da ƙira, hakan yasa, yau ta sanya wayarta a silent, dan kwata-kwata bata son damuwa, wannan dalilin yasa, sam bataga ƙiran da Zakariyyan keyi mata ba.
Zakariyya kuwa saida yayi mata 10 missed calls, ganin bata ɗaga ba yasashi fashewa da wani sabon kuka, da ƙyar Hayatuddeen ke iya tausansa.

Su Saifuddeen basu bar gidan Baba Malam ba, sai wajen ƙarfe shaɗayan dare.
Dan bayau ne za a kai Maryam din makwancinta ba, dole sai tayi kwanan keso, gobe kuwa da ƙarfe goma insha Allah za ayi sallan jana'izar ta, koda suka koma gida direct ɗakinsa ya wuce, inda ya murzawa ƙofarsa key, sam yau baison Ameena ta dameshi, dan ƙwarai rasuwar Adda Maryam ta daki jiki da zuciyarshi.

Ɓangaren Mama kuwa taso tahowa yau ɗin, amma babu abun hawan da zata hau tazo, haka taci kuka har idanunta suka kumbura, Zahira ma kukan take sosai, bata iya rarrashin Mama, haka Maman ma bata iya rarrashinta Maman Mama da Babantama sosai mutuwar Maryam ta shigesu.

Agidan Baba Malam kuwa kwana akayi anawa gawan Maryam karatun alƙur'ani, yanda suka ga safiya haka suka ga dare, kab gidan babu wanda ya iya runtsawa, Mamy tayi kuka harta godewa Allah, idanunta sunyi luhu luhu dasu, sam bata banbance su Maryam da ɗanta na cikinta, har gaban abada kallonsu take mazaunin ƴaƴanta na cikinta, haka suma sun ɗauketa uwace, basa taɓa banbantata da mahaifiyarsu, wannan dalilin yasa shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakaninsu, sau da yawa Maryam saitayi shawara da Mamy, batayi da Mama mahaifiyarta ba, haka ma Zakariyya duk wata damuwarsa koda ta kuɗi ce, Mamyn yake faɗawa, dan gaba ɗaya uwa suka ɗauketa.

Washegari ana idar da sallan asuba kuwa Ya Ahmad wanda suka kwana ahanya suka samu isowa gidan, nanne fa wani sabon kuka ya tashi, dan ganin gawan Maryam da kuma yanda ƴan uwansa ke kuka yasa gaba ɗaya hankalinsa yayi masifar tashi, haka yazauna yana kuka kaman ƙaramin yaro.

Zakariyya kuwa koda ya sallame sallan asuba, wayarsa ya ɗauka still ƙiran Zaleeha yayi amma no answer, nan ya shiga rubuta mata saƙo kamar haka.
_"Adda Zaleeha Ina ta ƙiranki bakya ɗagawa ko, kowa yaƙira wayanki bazaki ɗaga bako?, saboda kinsawa kanki zuciyar kafurci aranki, kin bijirewa Baba Malam, kin bijirewa kowa, kin gujewa gaba ɗaya danginki, kinƙi bin umarnin mahaifin mu, kin tafi can wata uwa duniya cikin kafurai kinje kin zauna, wataƙila ke kam bazaki dawo ba harsai gaba ɗayanmu mun ƙare, har sai kin rasa kowa naki na a faɗin duniya sannan zaki dawo, shikenan kici gaba da zama Adda Zaleeha, Adda Maryam kam tatafi ta barmu, tabar mana duniya'n, tayi nesa damu inda bazamu ƙara ji da ganinta ba yadda kika gujewa dangi duk suma sun guje miki gashi babu wanda ya tunaki,sannan nidana tunakin na kiraki baki amsaba."_
Yana rubuta saƙon yana kuka sosai, yana gamawa kuwa ya tura mata, inda ya kifa kansa ya cigaba da kuka."

Da duru-durun Asuba Mama da Zahira da wasu ƴan uwanta suka samu isowa gidan, ganin gidan nasu acike shiya ƙara ɗaga musu hankali, Nan Mama ta buɗe ɓangarenta ta shiga, anan falonta ta zauna tana wani irin kuka me cike da ban tausayi da tsantsar nadama.

Zaleeha kuwa yau makara tasoyi, tana tashi tayi alwala tayi salla, tana nan zaune akan sallaya tajiyo sallaman Aisha, cike da É—an mamaki ta amsa mata tare da bata izinin shigowa.
Aishan ne ta shigo ta zauna hannunta É—auke daÉ—an kula, agaban Zaleehan ta aje kulan tare da cewa.
"Kinganni da sassafe ko, wallahi kinsan yau ƙarfe 6 dai-dai muke da lecture shiyasa da zan fito nace Inna tabani abun karin kumallonki na kawo miki."
Murmushi Zaleehan tayi, tana ƙoƙarin cewa wani abune taga screen ɗin wayarta ya kawo haske, hakanan taji ƙirjinta ya buga, zuciyarta ta tsinke, jawo wayartata tayi tare da dubawa, text message ta gani da sunan Zakariyya, nan ta cire wayan a key, tare da shiga cikin message ɗin.
Hannunta na ɓari jikinta na rawa, haka tashiga karanta message ɗin, maganansa na kusa da na ƙarshe shine abun dayasa taji gaba ɗaya duniyar ta tsaya mata kanta yayi wani irin mugun sarawa duhu ya wulgawa ganinta, azabure ta miƙe tsaye, cikin wani irin gigita haɗi da kiɗima da tsananin tashin hankali ta dannawa numbern Zakariyyan ƙira, bugu biyu kuwa ya ɗauka, yana kara wayar akan kunnensa ya saki kuka, abun dayasa hankalin Zaleeha tashi kenan, lokaci guda bakinta ya soma ɓari, murya asarƙafe tace. "Zak....kar iya, ina Adda Maryam, meya sameta, mekakeson faɗamin Zakariyya?"
Cikin matsanancin kuka Zakariyya, yace.
"Adda Maryam tarasu Zaleeha, Adda Maryam ta rasu tun daren jiya, tatafi inda bazata ƙara dawowa ba, tayi nisa nisa irin na har abada....."
Kuka ne ya ci ƙarfinsa hakan yasa ya kasa ƙarasa maganan.
Chapter 64 · 0% Book details