← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 154

Sashe 89

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan sake jingina bayanta da jikin kujeran falon tayi, tare da lumshe idanunta, ta kuma sake riƙe Adeel dake jikinta ƙam, bacci takeji tare da gajiya, amma sam tanajin bazata iya shiga ɗakin nata ba, saboda Goggo Dada dake ciki, kunyanta takeji, musamman ma da takeson kafun ta kwanta tayi wanka. Hayatuddeen ne ya lura da yanda Zaleehan keta lumshe idanunta, alaman bacci.
Hannu yasa ya ɗan taɓa kafanta cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha bacci kikeji, kije ki kwanta mana."
É—an buÉ—e idanunta tayi, tare da sakin sassanyar murmushi. Raleeya dake jinsu ne taÉ—an É—ago kai, tare da duban Hayatuddeen É—in tace.
"Ai tun É—azu Goggo Dada na É—akin." ÆŠan marairaice fuska Hayatuddeen yayi yace. "To Adda Zaleeha ki tashi ki hau saman kujera mana."
Ummi da fitowarta daga É—aki kenan, duk taji abun da suka faÉ—a, duban Raleeya tayi, cikin kulawa tace.
"Raleeya tashi kije kicewa Goggo Dada ta dawo nan ɗakina mu zauna tare, duk ai zai ishe mu, abu ba yaro ba ba komai ba." "To" Raleeya tafaɗa tana me miƙewa tsaye. Saifuddeen da tun shigowar Ummin yake kallon yanayin yanda bakinta ke motsi, hakan yasa shi danna madannanin wheelchair ɗinsa ya nufi hanyar fita daga falon, dama tuntuni wannan damar yake jira shiyasa koda suka kammala dinner bai tafi ba.
Kai tsaye ɓangarensa ya nufa, yana shiga kuwa ya zaro wayarsa, text ya turawa Hayatuddeen akan cewar "Yazo yana son ganinsa." Hayatuddeen na zaune yaga saƙon Hamman nasa, tsam ya miƙe ya fice daga cikin falon, kai tsaye sashin Hamman nasa ya nufa.
Anan falo ya iske Saifuddeen ɗin, yana shan Maltina, ƙarasowa cikin falon yayi tare da cewa.
"Hamma gani." Kai ya jinjina tare da sanya hannunsa acikin al'jihun rigarsa ya zaro key, miƙawa Hayatuddeen key ɗin yayi, nan cikin body language ɗinsa yace. "Ka kaiwa Zaleeha, ta dawo ɗakinta tabarwa Goggo Dada wannan ɗakin."
Yanayin yanda yayi maganan yana wani basarwa, shine abun daya sanya Hayatuddeen yaji wani irin dariya ta kamasa, amma sai ya share, da murna ya karɓi key ɗin, tare da cewa.
"To zan kai mata." juyarda akalan kekensa yayi ya nufi bedroom, Hayatuddeen kuwa binsa yayi da kallo yana murmushi, yana ganin ya shige É—akin, yayi É—an tsalle tare da cewa. "Yess yanzu itama Adda Zaleeha zata koma É—akinta."
juyawa yayi cikin sauri ya fita daga falon. Anan falon Ummi kuwa har yanzu suna nan a zazzaune, gefe kuwa ga Ameena da zuciyarta keta raya mata abubuwa iri iri.
Da murna Hayatuddeen ya shigo cikin falon, yana É—an rawa, harda su shaku shaku, baki Ummi dasu Raleeya suka buÉ—e suna kallonsa, da mamaki Ummi tace.
"Kai Hayatuddeen lafiyanka kuwa?." Murmushi mai ɗauke da dariya yayi, tare da miƙowa Raleeya hannu, cikin jin daɗi yace.
"Adda Raleeya maza maza taso muyi rakiya ."
Hannunsa ya miƙa ya karɓi Adeel dake kan cinyar Zaleehan, ɗaga Adeel ɗin yayi sama tare da cewa.
"Adeel kaima kayi murna yau Amminka ta zama zata bar mana side É—in Umminmu ta koma can É—akinta."
Ya faɗi maganar yana me cilla Adeel ɗin sama. Jin abunda Hayatuddeen ɗin ke faɗa yasa Ummi sakin murmushi tare dayin ƙwafa, dama ai ita ta jima dagane shirin Saifuddeen ɗin, kuma zatayi maganinsa ne. Ameena kuwa kalaman Hayatuddeen ɗinne suka zuciyarta tsananta bugawa, wani irin fitinannen kishin Zaleehan ne ya taso mata, take taji komai na duniya ya daina yi mata daɗi, ashe duk adacan baya ba kishi takeji ba haukan banzane kawai takeyi, ayanzu yanda ƙirji da zuciyarta ke tafasa, nanne ta tabbatar da cewar kishi take, idanunta ne suka kawo ruwa, sakamakon wani irin ɗaci da takeji azuciyarta, lokaci ɗaya ta shiga cikin yanayi marar daɗi, miƙewa tayi jiki asanyaye ta fice daga cikin falon.
Tana fita Ummi ta gyara zama tare da cewa.
"Babu inda Zaleeha zataje, ai É—akina zai ishemu nida Goggo Dada'n, saboda haka bama sai taje ko ina ba." Goggo Dada wanda duk taji abun da suke faÉ—a ne ta fito daga cikin É—akin, cikin kulawa tace.
"A'a Ya zakiyi haka kuma, ki hana yarinya komawa É—akinta, ai baiyi ba."
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"A'a Goggo Dada barta dai anan É—in".
Kai Goggo Dada ta girgiza tare da cewa. "Sam baza'ayi haka ina gidan nan ba, ki barta ta koma ɗakinta, ai babu ma inda zatafi sakewa kamar ɗakin aurenta." Murmushi Ummi tayi, tare da cewa. "Shikenan, Zaleeha tashi ki koma sashinki, Allah ya muku al'barka." Wani irin kunyane ya lulluɓe Zaleeha'n, hakan yasa tayi ƙasa da kanta, Raleeya ne ta miƙe cikin jin daɗi tace.
"Yauwa Aunty Zaleeha tashi mu rakaki." Akunyace ta tashi tsaye, Raleeya ne ta kama hannunta, Hayatuddeen na biye dasu abaya, kafaɗansa rungume da Adeel, suka fice daga cikin falon, Goggo Dada da Ummi suka bisu da kallo suna murmushi. Ummi kam bataso ace Zaleehan ta koma cikin sauri ba, so tayi ta bashi wahala sosai akan komawar Zaleeha'n, tun da dai da farko babu yanda batayi dashi ba akan ya kawo key ɗin ɗakin Zaleehan ta koma, amma yaƙi, sai yanzu daya ga dama zai zo ya wani ce ta koma. Su kuwa koda suka ƙarasa part ɗin, Hayatuddeen ne ya sanya key ya buɗe ƙofar falon, nan suka shiga, Raleeya harda sata ta shiga da bismillah da kuma ƙafar dama, saikace wata sabuwar amarya, har cikin bedroom ɗinta suka wuce, wanda ko ina keta tashin ƙamshin airfreshener, anan kan gado Zaleehan ta zauna, tare da war ware gyalen da ta yane kanta dashi. Wayar Raleeya ne ta fara ƙara alaman shigowar kira, koda ta duba ganin sunan Raihana yasa ta ɗaga wayan tare da karawa akan kunnenta, bayan sun gaisane Raihana da yaji kaman Raleeyan na cikin farinciki tace.
"Mekuka samu ne haka keda Hayatuddeen, kuketa nishaÉ—i, daga nan mafa ina iya jiyo muryar Hayatuddeen." Murmushi Raleeya tayi tare da cewa.
"Mun rako Adda Zaleeha ne yau ta dawowa É—akinta."
tsuka Raihana tayi daga can cikin wayar tace.
"Aikin banza akan wannan shine kuketa wani farinciki? ai ni wallahi tunda tace batason Hamma nima banasonta."
ɗan murmushin yaƙe Raleeya tayi, dan batason kowa ya fahimci abun da Raihanan ke cewa.
Dai-dai lokacin kuwa Zaleeha ta É—ago kai ta kalli Raleeya, cikin sanyin muryarta tace.
"Raihana ce ko?".
GyaÉ—a mata kai Raliya tayi alamar eh itace.
Cikin yanayin sanyi tace. "Kice ina gaishe ta." Murmushi Raleeya tayi, take kuwa tace wa Raihana'n.
"Aunty Zaleeha tace na gaisheki."
A gyatsine Raihana tace.
"Banaso ta riƙe gaisuwarta."
jin hakanne yasa Raleeya ta fice daga cikin É—akin, falo ta koma, nan cikin son nusar da Æ´ar uwarta ta tace.
"Wallahi kedai Raihana kincika masifa, kuma kidaina ganin baƙin Zaleeha, wallahi tana da daɗin zama, saidai idan baki fahimceta ba, kuma koda da tace batason Hamma Saifuddeen me ta taɓayi mana? tana zaune damu lafiya, sannan kuma bata taɓa raihana mana mahaifiyar muba, kullum biyayya ne atsakaninta da Ummi, aganina ai hakan baizama abun da zaisa muƙita ba koda albarkacin hallacin mahaifinta."
Baki Raihana ta taɓe tare da cewa.
"Ohon muku dai, nidama naƙiraki ne dan naga tunjiya bamu gaisa ba, sai anjima ki gaishemin da Ummi na da autanta da Hamma na."
da haka sukayi sallama, Raleeya ta koma É—akin Zaleeha'n.
Sun ɗan taɓa hira kafun suka tafi, inda suka barta ita da Adeel.

Ummi kuwa da Goggo Dada É—akin Ummi suka shiga suna hirarsu ta manya kuma Æ´an uwa suna cikin hirane kiran Adda Rahma ya shiga wayar Ummi,
da sauri ta É—aga bayan sun gaisa ne Adda Rahma tace.
"Ummi ni kam yaushe ne Saifuddeen zai koma India a yaga likita?".
Ajiyan zuciya Ummi taja tare da cewa.
"Uhummm ke dai barni da Baba na Rahma, kingafa wancan karonma da kyar na sashi yaje bayan aurenshi da Ameena da wata shida kinga lokacinma watanshi takwas da dawowa kafin yaje, wai shi ya worke me sai yayi ta bin kan likitoci ai haka Allah ke son ganinsa kuma shi yama worke gara harda cemin shifa lafiyar shi lau."
Cikin sanyi Adda Rahma tace.
"To Amman kuma ai in anyi dace zai sake miƙewa tsaye fa suke cewa.
Ni yanzu nema Ya Adnan ke cemin Dr Acash prasat ya mishi mgna kan cewa, date É—in kowanshi fa yayi har ya É—an wuce, shine yake cemin in gaya miki kisashi ya fara shirin zuwa".
ÆŠan gajeren tsaki Ummi taja tare da cewa.
"Bazai yarda bafa, mu barshi kawai tunda yaji ya gani yace shi ya godewa Allah a hakanma tunda yana iya yiwa kanshi komai, in na matsa mishima sai dai yaje don dole badon yasoba, shiyasa ni kuma ban fiye son takurashi ba."
Kai Adda Rahma ta É—an jinjina tare da cewa.
"Uhum lfy yakeji ai in yaji ciwo ba sai ance ya komaba, Allah ya ƙara bashi lfy, dan na lura shi jin wannan kujerun nasa yakeyi kamar kujerun mulki".
Dariya suka É—anyi kana Ummi tace.
"Ga Goggo Dadanku ma tazo".
Cikin kula tace.
"Bata waya".
Cikin kula ta gaita kana ta ƙara da cewa.
"Goggo Dada zamu kwana biyu ko?".
Dariya tayi tare da cewa.
"Tab ai gobema da safe zan koma".
Cikin shaƙuwarsu tace.
"Ayyah dai Goggo Dada zaki idoni ko?".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Eh kafin in tafi zansa Ahmad ya kawomin".
cikin happy tace.
"To sai kinzo".
Da haka sukayi sallama, sukuma sukaci gaba da hirarsu.
Chapter 89 · 0% Book details