← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 154

Sashe 130

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sun gaishe da Saifuddeen ɗinne. Raleeya tayiwa Aunty Lubna jagora xuwa ɓangaren Zaleeha. Zaune suka sameta akan sallaya, tayi jigum, ganin Aunty Lubna yasa ta kwaɓe fuska, sai kuma ga hawaye sun soma tsiyaya daga cikin idanunta.
Ƙarasowa cikin ɗakin Aunty Lubna tayi tare da zama akan wani ɗan stoll ɗin dake gefen gado, a hankali ta kamo hannun Zaleehan cike da kulawa tace.
"Sannu Zaleeha ya jikin naki".
Kasa amsa mata tayi, saima samun kanta tayi da ɗan jan jikinta, ta ɗaura kanta tayi akan cinyar Aunty Lubna'n, lokaci ɗaya ta kwaɓe fuska cikin zallan shagwaɓa tai rau-rau da ido.
Ganin haka yasa Aunty Lubna ta É—anyi murmushi dan tasan mai neman kukane aka jefa da kashin awaki, ahankali ta soma shafa kanta, cikin sanyi da kuma lallashi tace.
"Ya isa haka Zaleeha kada kiyi kukan, ciwon me kuma yake damunki harda kuka?" ɗago kanta daga cinyar Aunty Lubnan tayi cikin naƙe murya tace.
"Zafi nakeji Aunty duk jikina ciwo yake min, sabida muguntar da Hamma Saif yamin."
Danne dariyarta tayi tare da cewa.
"Kenan nima sai ince ya Ahmad É—inki ma mugunta yaita min".
Kai ta jujjuua tare da cewa.
"Allah nasan da kinyi ta magiya da roƙon ya Ahmad ya barki yadda nai ta mishi jiya da dare nasan zai barki.
Shi dai mugune, babu irin kuka da roƙon da banyi masa ba, amma yaƙi jina, zafi nakeji sosai Aunty ko tafiya mai kyau bana iyawa, gashi ma harda zazzaɓi nakeyi."
Sosai Aunty Lubna ta gane sanadin ciwon Zaleeha'n, É—an sake shafa kanta tayi.
Cikin kulawa tace.
"Kiyi haƙuri Zaleeha kowa ma yaji hakan, amma da sannu yake wucewa, banaji Ummi tace likita ta dubaki ba." Ashagwaɓe ta gyaɗa kanta, cikin lumshe ido tace.
"Amma Aunty Lubna meyasa zaimin haka, yanzu fa ko ƙarfi banaji ajikina."
ÆŠan guntun murmushi Aunty Lubna'n, tayi, tare da cewa.
"To yanzu ai yayi mgnin guduwa da bakin tsiwa.
Ai haƙuri kawai zakiyi , shima dakike magana akai ai ba daɗi yakeji ba, yanzu haka ma fa shi mukazo dubawa, jikinsa babu daɗi, ciwonsa ya tashi, ko ɗazu ma su Baba Malam harma da Mama sunzo dubashi." Idanunta ta zaro waje, cikin yanayin damuwa da fargaba tace.
"Bashi da lafiya kuma Aunty, to me ya sameshi?." "Bayansa ne ke ciwo, dan ma naji ance sai an fitar dashi India, yanzu dai ki lallaɓa kije ki duba shi, yana can sashin Umminsa."
Hakanan taji wani irin matsanancin tausayinsa ya dirar mata azuciya, take taji zuciyarta ta karye taji tana son ganin shi.
Miƙewa tsaye Aunty Lubna tayi tare da cewa. "Ni kam zan wuce, dan tare ma muke da Yayanki, nace bari na shigo naɗan dubaki." Hannun Aunty Lubnan ta kama sannan ta miƙe tsaye, cikin yanayin shanye ciwon da takeji, tace.
"Aunty muje na gaishe da Ya Ahmad, tunda dai yaƙi shigowa."
A cikin ranta kuwa cewa tayi.
"Daga nan zan ganshi ai, in banda Hamma Saif kai kamin fyaÉ—e kuma kaima wai baka da lfy mu duka mun zama majinyata".
Murmushi Aunty Lubna tayi, tace.
"Baƙin shigowa yayi ba, suna tare da me sunansa ne."
(Wato Ahmad mijin Raleeya.) Kaita É—an jinjina, sannan ta kama hannun Aunty Lubna'n, haka suka fito daga cikin sashin nata, ahankali take tafiya, sai faman ciccije baki take, kasancewar tana É—anjin zafi acikin jikinta.
A compound É—in gidan, suka iske Ya Ahmad da kuma Ahmad atsaye, suna É—an tattaunawa, wanda kuma duk akan matsalan Saifuddeen É—inne, kana anan Ya Ahmad ke ce mishi suma gobe zasu koma Abuja.
Ganin Zaleeha yasa Ya Ahmad É—in sakin murmushi, cikin kulawa yace.
"Ha'a marar lafiyance da kanta, har kin warke kenan?."
Ɗan shagwaɓe fuska tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, asakalce tace.
"Nidai Ya Ahmad nayi fushi, kazo har gidan nan shine kuma sai kaƙi zuwa sashina, bayan kuma kasan cewa bani da lafiya."
Murmushi yayi tare da kamo hannunta, ya shafi gefen fuskarta cikin kulawa yace.
"Sannu ko, Mangana yanzu ya jikin naki? Ko dai yanzu kam Mangan Hamma Saif ne?."
Jin yace mata manga, Hamma Saif ta sake shagwaɓe fuska, cikin mamul mamul da baki tace.
"Da ɗan sauƙi kaɗan."
ɗan murza hannunta yayi tare da cewa. "Good Allah Ya Ƙara sauƙi."
Kanta taɗan jinjina sannan tace Ameen. Bayan motarsa ya buɗe inda ya ɗauko wata leda miƙa mata yayi, yana murmushi yace.
"Gashi dama saboda ke kaɗai kawai na saya, ki kula da kanki kinji Shagwaɓaɓɓiyar Mijinta." Amsan ledan tayi tana murmushi, jin yace da ita wai Shagwaɓaɓɓiyar mijinta, yasa tayi saurin basa baya, wai ita adole taji kunya. Murmushi yayi, kawai nan sukayi sallama, Saida taga fitansu daga cikin gidan kafun suka juya ita da Ahmad suka nufi sashin Ummi. Ahmad ne ya ɗan kalli yanda take tafiya, tausayinta ya ɗanji saboda ya tuna da Raleeyansa, haka itama tayi first night ɗinsu. "Ya jikin?."
Ya tambayeta, yana ɗan sakin ɓoyayyar murmushi.
A hankali tace.
"Da sauki."
Murmushi Ahmad ɗin yayi, tare da girgiza kansa kawai, dan yasan daga Zaleehan har Saifuddeen ɗin jirgi ɗayane ya kwasosu, dan komai nasu iri ɗaya ne, sakalci, raki, da kuma zallan shagwaɓa.

Koda suka ƙarasa falon Ummi, Raleeya suka samu da Adda Rahama azaune sai Hayatuddeen. Ganin Zaleehan yasa Adda Rahama tace. "Masha Allah Jiki yayi sauƙi kenan."
Ɗan ƙasa tayi da kanta, dan wani irin kunyansu takeji, su dukansu sabisa sai take ga ai duk sun fahimci sanadin ciwonta. Hayatuddeen wanda yake kusa da Adda Rahama ne kuma shi sam bai fahimci sanadin cutar ta duba ne yace.
"Ba dole jiki yayi sauƙi ba, tunda rabin ranta ba lafiya, ae yana buƙatar kulawanta".
Daga jin maganan kasan zallan tsokana yakeson takalowa. ÆŠan sunkuyar da kanta tayi tare da É—an hararan wasa,
Daga Raleeya har Ahmad dariya sukayi, Adda Rahama kuwa cewa tayi.
"Manta da Autan Ummi kinji, jeki É—akin Hayatuddeen É—in ki duba Saifuddeen dan shima yana fama da jiki." Kanta ta jinjina, tare da É—an kallon Hayatuddeen ganin yana binta da idone yasa ta É—an haÉ—e fuska kana ta juya.
Cikin sanyi ta nufi ɗakin Hayatuddeen din. Murmushi Ahmad yayi, cikin zuciyarsa yace. "Marar kunyan ƙarya, lokacin da kikaji maza, ina da ga kwance saida najiyo ihunki, fitsarerriya ai yamin mgnin ki, ko yau na mutu ban mutu da baƙin cikin ba yamin dai-dai dan daga yawau bakin ya mace."

Ahankali ta tura ƙofar ɗakin Hayatuddeen, bakinta ɗauke da sallama, taɗan kutsa kanta ciki.
Kwance yake akan gadon Hayatuddeen, ya ɗan jingina bayansa da jikin pillow, dan Dr.Aleeyu yace masa yanayin hakan, zai ɗan taimaka bayan nasa ya ware. Gefensa kuwa Ameena ce, zaune tana ƙoƙarin ɓare magunguna zata bashi yasha.
Ahankali tayi ƙasa da kanta, cikin muryarta da ta ɗanyi sanyi tayi sallama.
Ameena ce ta amsa, tare da cewa.
"Masha Allah jiki yayi sauƙi kenan Ammin Adeel."
Kanta ta jinjina kana ta ɗanyin guntun murmushi, tare da kama ƴan yatsun hannunta ta shiga yin wasa dasu, Idanunsa ya ɗago ya watsa mata, wani irin so, ƙauna, haɗi da zallan tausayinta ne suka cika masa zuciya ya kamata ace a irin ya wannan ranar ta samu kulawarshi irin kulawa mai nuna jin daɗi to ciwo ya hana.
A hankali ya ɗan nago hannunsa ɗaya ya miƙa mata alaman tazo.
lumshe idonta tayi, kana ta buɗesu ganin har yanzu yana miƙo mata hannun ne sai
taji bazata iya ƙi ko musa masa ba, ahankali ta ƙaraso tare da sanya hannunta acikin nasa, jawota yayi ya zaunar da ita kusa dashi, har gaba ɗaya jikinsu na manne da juna.
Kanta taɗan ɗaura akan kafaɗansa, tare da ɗan lumshe idanunta. Wani irin ajiyar zuciya suka sauƙe atare su dukansu uku,
ganin haka yasa Ameena ɗanyin ƙasa da kanta, tana ambaton sunan Allah acikin ranta, kana sai ta kumayi ɗan murmushi jin ya kamo hannunta.
Ahankali ya kamo hannun Ameena'n, ya riƙe acikin nasa gam ya haɗe tafukan hannunsu wuri ɗaya,
Murmushi tayi, cikin son basu waje tace. "Bana bari to kuɗan gana, nasan ma Adeel nacan yana neman nono, anjima ina dawowa." Ɓuɗe idanunsa yayi, ya kalleta, tare da ɗan yi mata murmushi sannan ya jujjuya mata kai alaman "A a shi dai karta fita."
Tafin hannuntan yasa tsakanin wuyanshi da kafaÉ—anshi cikin yanayin mai wuyar fasalta sirrin zuciyarshi.
yayi mata wani irin kallon da taji tamkar ta faÉ—a jikinshi,
zaro hannun nata yayi ya É—aura shi kan bakinshi a hankali yayi mata wani fitinenne kissing bayan hannunta,
ido ta lumshe cikin tsananin farin ciki ta ɗan janye hannunta tare da miƙewa cikin sakin fuska da zuciya tace.
"To bari inje in É—auko Adeel kajishi can yana kuka".
Kai ya gyaÉ—a mata alamar to.
Tana fita kai tsaye side É—insu ta wuce, dan Adeel kam wurin Ummi ma yake.
Chapter 130 · 0% Book details