← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 154

Sashe 47

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fitowarta daga wanka kenan, body lotion ta shafa ajikinta, tare da É—an murzawa fuskarta powder, wata nighty gown me fitar da shape É—in jiki ta sanya, babu laifi kuma dama tana da sura me É—an kyau, nan rigar ta lafe ajikinta, inda tayi mata kyau, É—an madaidaicin gashinta ta É—aure sannan tayiwa jikinta wankan turare.
Koda ta kalli kanta amadubi tasan cewar tayi kyau.
Cikin nutsuwa tafice daga ɓangarenta batare da ta sanya mayafi ko wani abu ta rufe jikinta ba, yau dai kam ta ƙudurta aranta cewa, zata bawa kanta nutsuwa daga garesa koda ƴar kaɗance.
Ahankali ta tura ƙofar ɗakin nasa ta shiga.
Yana zaune a tsakiyar gado yasa system ɗinshi a gaba wayarsa na riƙe ahannunsa yana dannawa.
Jin ƙamshinta ya cika masa hanci ya sashi ɗago da kansa, inda ya sauƙe idanunsa akanta.
Dai-dai lokacin ta maida ƙofar ɗakin ta rufe.
Ƙura mata idanu yayi yana me bin ko ina na jikinta da kallo, sosai shape ɗinta ya bayyana har takai ga yana iya hango komai na ƙirjinta.
Cikin salon jan hankali tashiga takowa zuwa garesa, inda ta kafesa da idanunta wanda suke cike da mayen soyayyarsa, shiÉ—in ma yau dai kasa É—auke idanunsa daga gareta yayi.
Ahaka taci gaba da ta kowa zuwa garesa, tana isowa kusa dashi ta lumshe idanunta tare da haurawa kan gadon, kanshi ya É—an kauda ya maida ida nunshi kan wayarshi,
shiru yayi ya bar daddanna wayar tashi jin ta matso kusa dashi gab da gab,
juyowa yayi ya ɗan kalleta kwaɓe fuska tayi tare da cewa.
"Zan kwanta bacci nakeji."
Da idonshi ya nuna mata wurin kwanciya,
Madadin ta kwanta inda ya nuna matan sai kawai tasa hannu ta ture system É—in na shi,
da sauri ya sunkuyo dan tare system ɗin daga faɗawa ƙasa, sunkuyowan da yayine ya bawa jikinsu daman haɗewa,
fuska ya haÉ—e tare da yi mata kallon zaki min ta'adi.
A hankali tace.
"Sorry."
Daga nan ta koma ta kwanta,
shi kuwa ya ɗan jima a zaune yana chat da Ishaq, in da yake ce mishi yanzu dai saura shida Mudassir suyi aure, tunda shi dai sun nace sun liƙa mishi mata.
Jin hakane ishaq yace.
ina amaryar.
É—an juyowa yayi ya kalleta, da sauri ya kauda kanshi ganin har yanzu batayi bacciba kuma shi ta zubawa ido.
Taɓe fuska yayi tare da rubutawa ishaq.
"Gata nan a gefena ta zuba min ido kamar mayya ina ga dai yau kam cinyeni zatayi."
Ishaq na karanta saƙonshi ya turo mishi amsa.
"In ta cinyeka ma ai halal É—inta taci,
Pleess Saifuddeen mu bar wasa, kayi ƙoƙarin yiwa yariyar nan adalci."
Da sauri ya maidawa ishaq amsa cewa.
"To naji me nayi mata na rashin adalci, me ta nema ta rasa ban zagetaba ban doketaba,
Da tace ɗakina take son kwana ma ban hanataba, kuma gadona na bata ba'a ƙasa nace ta kwanta.
Me ya rage zan mata?."
Da sauri ishaq yace.
"Haƙƙin aurenta mana wanda yake kanka, waji bine bayan ciyarwa da shayarwa ka biya mata buƙayar ta na ƴa mace ka kawar mata da buƙatan Namiji."
Uhum Saifuddeen yace lokacin daya karanta batun ishaq cikin sanyi yace.
"To ai batace tana soba. Ni kuma banji inada buƙata ba, amman in tace tana so ai gani gata ba sai tayiba tunda ai tasan komai, kuma a ɓurme take tunda ta taɓa aure wani gardin ya taɓa ɓurmata, ni ba rami kawai aka kawo min ba."
Sosai ishaq yayi dariyar daga bisani yace,
"Tana mace ya za'ayi tace tana so."
Cikin ƙosawa da zancen yace.
"Uhum baka santa bane wannan da idanu a tsakar ka, ai fyaÉ—e ma zata min. Kuma na gaji sai da safe."
Yana faɗin haka ya rufe data sannan ya ajiyo woyar da laptop ɗin bisa bed side kana a hankali ya kwanta tare da yin miƙa, a hankali yake sauƙe nufamshi dan ya daɗe a zaune gugunshi ya gaji.

Shiru sukayi baki É—ayansu a tunaninshi Amina tayi bacci.

Ita kuwa idonta biyu, jin motsin ya kwanta ne yasa, ta É—an buÉ—e idonta a hankali ta mirgono ta matso kusa dashi.
ƙara matsoshi tayi cikin tsananin ƙaunarsa ta manna ƙirjinta da bayanshi,
yana jin hakan a jikinshi yace.
"Uhummm ta nan kikafi ƙarfi."
A zahiri kuwa juyowa yayi da niyar yaga fuskarta sai kuma yayi lub bisa gadon jin ta ruggumeshi da kyau, wani irin yam tsikar jikinshi ta bada,
ita kuwa Amina kanta ta É—an nago ta kalli fuskarsa cikin sanyi ta mirgino jikinta kanshi gaba É—aya tayi mishi rumfa,
hannunta tasa tana shafar sajenshi,
har zuwa haɓarshi a hankali ta lumshe ida nunta kana ta manna bakinta kan nashi,
da ƙarfi ya sauƙi numfashi lokacin da yaji ta lome tattausan lips ɗinshi tanayi musu wani irin zazzafan tsotso wanda yasan hucewa takeyi a kansu.
Shiru yayi mata kamar baisan me takeyi ba ya dai bata jikinshi tayi yadda takeso dan bashi da hurim hanata,
ita kuwa lallatseshi tayi son ranta sannan ta sahirta mishi ta koma ta konta, tana sauƙe numfashi.
shi kuwa gaba É—aya yama rasa meke gudana a jiki da zuciyarshi.
A haka duk sukayi bacci.

Washe gari da safe, koda suka haɗu a falon Ummi ƙin yarda yayi su haɗa ido ya lura so take ta titse mishi idanu.
Ganin ta dameshi da kallone ya sallamesu ya fita.

Kasan cewar yau jumma'a kai tsaye shirin zuwa masallaci yayi.
Wata ɗanyar shadda mai kalan sararin samaniya ya sanya, sosai shaddan tayi masifar yi mishi kyau, hulan zanna bukar ya kafa akansa, inda ya ɗaura tsadadden agogon apple watch a hannunsa, yayi kyau ƙwarai, sai tashin ƙamshi yake, ƙwarai Saifuddeen ya iya tsantsara gaye sosai.
Direct wajen Ishaq ya nufa.
Daga wajen ishaq É—in kuwa gidan Baba malam suka wuce,
dan kai mishi gaisuwar jumma'a kamar yadda suka saba.
Nan suka samu Ya Aminu da Ya Habu kana da Malam Adam, cikin mutunci suka gaisa, kana suka ɗan taɓa hira,
a nan Ya Aminu ke cewa zai kawo Maryam taga amaryarshi,
sosai kuma yaji daÉ—in nasihar da Baba Malam da Malam sukayi mishi suma dai sun jaddada yayi mata adalci a cikin zaman nasu.
Daga ƙarshe duk suka tafi masallaci kofar sarki a tare kasan cewar Baba malam ne limamin masallacin.

Daga masallacin gidansu Ishaq É—in suka wuce wanda a nanne ya samu Hayatuddeen Zakariyyah da isma'il da Sulaiman
Da Khamis sabon abokin Hayatuddden, daga ganin yaron Saifuddden ya karan ceshi ɗan banzan yarone da fuska kamar faskaren wawa ya ƙudurta yana gama aikin da yakeyi, zai maida akalan ƙoƙƙofinshi kan autan Ummi da wannan abokin nashi dan sam bai konta mishiba.

Zaleeha kuwa sosai ta saba da Aisha wanda zuwa yanzu mahaifin Aisha Man liman da kanshi yace a ajiyewa Zaleeha kwaryan abinci daga gidanshi wanda kullum yara ke kai mata.
Wannan abin yayi matuƙar yiwa Zaleeha nauyi inda taso taƙi amman fir dottijon ya hana,
To yau kusan a nan ta wuni ita da Aisha sai yamma ta tafi.
Bayan tafiyarta ne, Inna ta kalleshi cikin son fahimtar wani abu tace.
"Meyasa ka sawa lamarin yarinyar nan ido ne?."
Kanshi ya jujjuya tare da cewa.
"Lamarin yariyar akwai abin tausayi, ta gefe biyu ake jefanta da sihiri,
Asali zuwanta garin nanma ture akayi mata,
kana kuma an kafata anan É—in bazata iya komawa inda ta fitoba in ba an karya abinda ke jikinta ba, kuma aikine mai wuya dan matsafine yayi aikin,
Sannan akwai wani sashin da ake binta da sihirin lalata rayuwarta, wanda badon tana da ƙarfin imani da riƙo da ibadaba da karuwa aka a maidata,
ina son ku jata a jiki kuji meya kawota nan, yarinÆ´ar abar tausace dan akwai fushi a kanta."
Wani nannauyan ajiyan zuciya Inna ta sauƙe tare da cewa.
"In sha Allah za'ayi haka, zan sanarwa Aisha manufarka."
Kanshi ya rausayar tare da cewa.
"Ƴar birni kamrta mai cikar gata da jin daɗi da wayewa musulma mai ibada me zai sa ta baro inda take cikin jin daɗi tazo ƙauye tsakiyar kafurai ta zauna ai dole da walakin goro a miya."
Cikin gamsuwa inna tace.
"Gsky kam baza'a rasa ba."
daga nan Man liman yaci gaba dayi mata bayanin abubuwan da yake gani a jikinta, wanda duk sihirin Mamane da Ruda sai Bilkeesu dake yi mata dan ta lalace.

A haka kwanaki suka ɗan miƙa.

Saifuddeen kuwa ya gama tsinkewa da lamarin Amina don yanzu kullum dere da salon da take zuwar mishi, ta kai matakin da tana iya kama kamoi na jikinshi ta tsotsa ko ta kamo hannunshi ta kai inda bai zataba a jikinta.

Yau kuwa tun da Yamma Amina keta shirya kanta dan yau dai tayi niyar malaka mishi kanta,
ya isheta zamansu a haka zata mori ƙuruciyarta da santalelen mijin da Allah ya azirta-ta dashi.
Chapter 47 · 0% Book details