← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 154

Sashe 52

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da misalin ƙarfe 9 kuwa Ameena tashigo cikin ɗakin.    ganin cewa yana gudanar da aiki me mahimmanci,  yasa batayi ƙoƙarin damunsa ba, kan gado kawai ta ɗale tare da kwanciya, sama-sama taɗan latsa wayarta daga haka bacci ya ɗauketa, ko data'n ta dake akunne bata kashe ba.    
Shikuwa Saifuddeen har wajen 12 na dare yakai yana aikin bincike, cikin sa'a kuwa yagama haɗa duk wani information da yake so, dan kuwa ya gano inda mutumin yake, saida ya turawa ogansu komai kafun yake rufe laptop  ɗinsa, nan ya ɗauro alwala sannan yazo ya kwanta, ganinta haka bata rufe jikinta ba, yasashi rufa mata blanket, tare da gyara mata konciyarta, cikin mintuna kaɗan bacci ya ɗauke sa.      

Washegari kuwa ya tashi da ayyuka masu yawa akansa,  hakan yasa tunda ya fita daga gidan bai dawo ba sai wajajen 3pm,  nan ma dai part ɗin Ummi ya zauna.   Koda dare yayi ya tafi zuwa ɓangaren su, nan yasamu Ameena har tayi bacci, yaji daɗin hakan kuwa, don dama baiso ya isketa idanunta biyu, gudun kada ta ce zata ƙara neman wani abu daga garesa.              
Aikinsa ya ɗan taɓa kafun bacci ya ɗaukesa.       

Yauɗin ma dai baitashi da niyan zaman gidan ba, dan yanzu aikin nasa yaɗau zafi wani abun dole sai ya fita da kansa yaje ofishin sirri na DSS.  
Cikin nutsuwa yagama kimtsa wa, cikin wani lallausan yadi me kyau da tsada, yayi kyau matuƙa, Ameena dake tsaye tana kallonsa ne tasaki murmushi, tare da ƙarasowa kusa dashi,ido ya ɗan zuba mata ganin ta sunkuyo kanshi a hankali ta dai-daita fuskarsa da nata, batare da yayi  aune ba sai kawai jin bakinta yayi, acikin nasa tanayi masa tsosan sweet,  sam bai hanata ba saboda haƙƙin tane, saidai kuma baiwani biye mata ba, cikin mayen soyayyarsa ta ɗago idanunta ta kallesa, kallo ɗaya yayi mata yaɗan ɗauke kansa, murmushin yasakar mata tare da shafa gefen fuskarta, cikin body language ɗinsa yayi mata alama kan cewa.
"Saiya dawo."
Fatan al'khairi tayi masa, yana fita tafaɗa kan gado, tare da sakin ajiyar zuciya.       
Shikuwa  Saifuddeen saida ya biya ta wajen Umminsa kafun ya fito, inda sule driver yayi driving ɗinsa suka fice daga cikin gidan.

Ameena kuwa yau a ɓangaren Ummi ta wuni, ba ita ta koma sashinsu ba sai da magrib ta gabato.      
Tanayin sallah kuwa ta ɗauki tsumin ta ta sha, tare da turara jikinta da turaren ƙamshi.
Nan dai ta kimtsa kanta tsab, dan tana matuƙar begen mijinta, kwana uku kacal amma tayi mugun missing lallausan jikinsa.     
Duk da cewa ya jima da dawowa amma bai shigo gidan ba saida  yayi sallan Isha, ɓangaren Ummi yaje suka ɗan taɓa hira, kafun ya komawa part ɗin nasu.        
Yana shiga ɗakinsa ya iske Ameena zaune akan gado, tasha ado cikin sleeping dress masu kalar pink.                 Yau ita da kanta ta haɗa masa ruwan wanka. 
Koda ya fito daga wankan, amsan towel ɗin hannunsa tayi, nan tashiga goge masa ɗan danshin ruwan dake jikinsa, haka dai yaɗan kimtsa inda ya hau kan gado ya kwanta. Itama Ameenan kwanciya tayi akan gadon, tare da  zagayowa ya zama suna fuskantar juna,     ɗan ranƙwafowa tayi tare da kamo hannunsa ta ɗaura akan waist ɗinta,   bakinta ta ɗaura akan nasa,  inda ta kamo laɓɓansa tana sucking,  lumshe idanunsa yayi cikin ransa yace.  
"Oh ni Saifuddeen naga takaina, nadawo kaman wani alawa, ko yaushe tana cikin tsostsotseni ita ko gajiya ma batayi ne."     
Ameena kuwa gaba ɗaya ta fara manta inda take, sosai take romancing ɗinsa,  gane abun da take nufi yasashi, kasa hanata abun da takeso, saboda haƙƙinta ne, idan ya hanata sai Allah ya tambayesa.                     Kamar dai wancan daren haka awannan daren ma Ameena ta more Saifuddeen,
Ido ya lumshe dai-dai lokacin data zauna kan cinyoyinshi suna fuskantar juna,
Zaleeha yake jida gani a cikin jikinshi da zuciyarshi, shiyasa a take lafiyarshi ta harba ya miƙe ƙam yana ta harbawa da cika,
Ajiyan zuciya ya sauƙe da ƙarfi jin ta haɗe kanta dashi, yana mai mmkin duk abinda fa  Ameena zata mishi baya tashi har sai dai in ya tuno Zaleeha ya kawota cikin ransa,
Haka nan yake jin tausayin Zaleeha dan wallahi Allah yasan karonta dashi bazai mata ta daÉ—iba, ya guturta kashe bakin tsiwar nan a dare É—aya,
yanaji a jikinsa tabbas Zaleeha matarsace zata dawo da ƙafafunta zai kuma yi maganinta yana dai-dai ƙugunta, a haka dai yana cikin tunanin Ameena tayi ta bidirinta a jikinshi, ido ya ɗan lumshe sai da aka ɗan zo bakin boda ne, sai ya jawota jikinshi ya ruggumeta da ƙarfi tare da sauƙe tagwayen numfarfashi.

Dan gane da gajiyar jiki kuwa, sai ma abun daya ƙaru, don kusan yau zaice yamafi ranan jin gajiya, sam bayason wahala, bazaice Ameena bata gamsar dashi ba, sannan bazaice bayajin daɗin kasancewa da ita ba, saidai ajikinsa yanajin tabbas akwai wani  babban gurbi wanda bata iya cikewa, hakanan yakeji kamar akwai wani abun da ta rasa baijin irin gamsuwar da yake buƙata ba, hakan kuma baya rasa nasaba da bata iya jure tsawon lokacin da yake buƙata, yana buƙatar gamsuwa ta sosai da sosai ita kuwa Amina macece dole tanada rauni.         
Wanka yayi sannan ya dawo ya kwanta, ajiyar zuciya yaketa sauƙewa dan yagaji sosai, itama Ameenan kwanciya tayi bayan tayi wanka, haka takejin ranta ƙal, bata da wani sauran damuwa.
Hannunshi ya É—an sa a hankali ya s....!

*Uhummm yanzu aka fara kabcen, ana dara sai ga dere yayi, ƙaƙa tsara ƙaƙa!?.*

LITTAFINA NA KUÆŠINE duk wacce ya/ta karanta bata biyaba tasan na ne ta karanta, É—ari ukune dai nace kuÉ—in ba miliyon uku ko dubu É—ari uku ba ko dubu ukuba É—ari uku zaki turo katin mtn na 300 ta number nan 09097853276 ko kimin transfer 300 ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta no nan 09097853276

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: sbpeny. Shafa gefen fuskarta, yayi har zuwa wuyanta,
ido ta zubawa jajayen laɓɓansa da bata gajiya da tsotsansu. Shi kuwa janye hannunshi yayi a hankali kana gyara kwanciyarsa.

Washegari kuwa gidan nasu ya karɓi baƙoncin Adda Maryam da kuma Ya Ameenu, dan dama Ya Ameenun turawa Saifuddeen ɗin saƙo dakansa yasanar masa da zuwansu.
Aɓangaren Ummi Maryam ɗin ta sauƙa, cikin girmamawa kuwa suka gaisa da Ummi, nan taƙara basu haƙuri akan abun daya faru, tare da yi wa Ummin murnar ƙarin auren Saifuddeen.
Hayatuddeen dakansa ya je ɓangaren Ameena inda yace tazo su gaisa da Adda'n Zaleeha, wato Adda Maryam ɗin, jin haka yasa Ameena tasanya hija binta, nan ta nufo ɓangaren Ummi'n.
Cikin girmamawa suka gaisa da Ameena', sosai Adda Maryam tasaki jikinta suka sha hira da Ameena'n, hakan kuwa yasa Ameena taji daɗi sosai, take taji ƙaunar Adda Maryam ɗin ya cika zuciyarta.
Hira sosai suka sha, sai wajajen Sallan la'asar Ya Ameenu yazo ya ɗauki Adda Maryam ɗin suka koma gida, turarukan wuta masu ƙamshi Ummi ta haɗawa Adda Maryam ɗin, nan tayi ta mata godiya, saboda Maryam macece da bata rena kyauta, komin ƙanƙantan abu idan kabata zata nuna maka farin ciki kana kuma zatayi maka godiya sosai.
Bayan zuwan Adda Maryam da kwana huÉ—u ne.
Saifuddeen ya turawa Ameena saƙo kan cewar tashirya yanaso zasu fita.
Koda Ameena taga text message É—in sosai zuciyarta yayi fari, wani irin daÉ—i taji, karon farko kenan da zata fita tare dashi.
Wanka tayi inda ta kimtsa kanta cikin wani haÉ—aÉ—É—en lace mai laushi, babu laifi kuma tayi kyau.
Koda zasu fita saida tabiya ɓangaren Ummi tayi mata sallama.
Nan ta fito dan Saifuddeen ɗin yace tasameshi amota, tana ƙarasawa jikin motar tasa ta buɗe, nan tashiga ta zauna agidan baya, inda shima anan yake zaune, sosai yayi kyau cikin shigar shadda dake jikinsa, inda ya kafa hula mai kalan coffee akansa.
Yayi kyau ƙwarai, hakanne yasa ta kasa ɗauke idanunta akansa, shikuwa kallo ɗaya ya mata tare da ɗan gutun murmushi kana ya kauda kanshi dan ya lura in yabar lips ɗinshi kusa da ita zata cafesu yanzu tayi sabon nata.
Sule driver ne ke driving É—in motar.
Kaitsaye G.R.A gidan Baba Malam suka nufa.

Agaban tanfatsetsen gate É—in gidan sule driver ya tsaya tare da danna horn, cikin mintuna kaÉ—an aka wangale masa gate É—in ya tura hancin motar ciki.
Yana gama dai-dai-ta parking É—in motar kuwa ya buÉ—e motar ya fito, zagayowa yayi inda ya buÉ—ewa Saifuddeen É—in murfin motar, tare da fito masa da kekensa.
Cikin nutsuwa Saifuddeen ɗin ya hau kan keken, Ameena kuwa da kanta ta buɗe murfin motar ta fito, sosai tashiga ƙarewa yanayin gidan kallo, tabbas gidan yayi kyau, cikin ranta tace.
"Zanso ganin wannan Zaleeha, idanuna sun zaƙu dason ganinta sosai, inason ganinta sosai a zahiri ido da ido kodan naga me take dashi wanda ya ɗauke hankalin Saifuddeen da dangishi ji wai an kwasota tazo ta gaida iyayen kishiyarta, wannan abu yayi masifar ci mata rai badan ma Ummy ta gaya mata gidansu Zaleeha zasuje ba ai ita a zatonda ko ɗan wani garding zasu je to koma meye haɗina da gidan".
sosai tsarin gidan ya tabbatar mata da nagarta da darajar masu gidan.
Chapter 52 · 0% Book details