Sashe 13
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahankali Sule driver ke tafiya dasu acikin motar,  idanu Saifuddeen ya lumshe tare da jingina bayansa da jikin kujeran motar, sosai yake shaƙan daddaɗan ƙamshinta, hakanan haɗewar ƙamshin turarensa da nata suka ba da wani irin yanayi me daɗin gaske, irin yanayin ƙamshin nan mai sauƙar da kasala uwa uba ga sanyi Ac da motar ke busa musu,  cikin nutsuwa ya ɗaura hannunsa ɗaya akan nata hannun, take haɗuwar lallausan fatar jikinsu waje ɗaya ya ƙara sauƙar masa da kasala, cikin ƙunan rai da hatsala Zaleeha tayi yunƙurin janye hannunta baya, amman sai ta gaza hakan jin ya rumtse tafin hannunta cikin nashi sosai zuciyarta ke tafasa, gefe guda kuwa ga ƙamshin turarensa wanda gaba ɗaya yabi ya cika mata hanci yana birkita mata kwanya sai shaƙar daddaɗan ƙamshin nashi takeyi, wanda tsabar tsanan da tayiwa mai turaren yasa take ta son cusawa ranta tsanan ƙamshin turaren nasa har wani abu me ɗaci-ɗaci take rayawa kanta takeji acikin maƙoshinta, zuwa yanzu har rasa yanda zata misalta tsanarsa aranta takeyi, komai bayayi mata daɗi, tana daurewa ne kawai don plant ɗinsu da suka shirya yakai ga ci, ga kuma gargaɗin ya Habu wanda tasan ba mitunci ne dashi ba, bacin haka babu wani abu da zaisanyata zuwa wannan banzan diner'n toma da wanne angon zata taka ta shiga. Ganin tajanye hannunta daga cikin nasa yasanyashi maida kansa jikin lallausan kujeran motar, numfashi yake fitarwa ahankali, yayinda wani irin kasala ke sake lulluɓe masa jiki. Kowannensu zuciyarsa ɗauke take da tunani kala-kala shi ji da gani yake kamar bata tsiraba daga sharrin masu son saceta da haryanzu hidimar bikin bata barshi ya gama bincikosu ba, ita kuwa ji take da zama kusa dashi gwara zama kusa da bakin kura. A haka suka ƙaraso babban wajen wanda aka ƙawatasa iya ƙawatuwa, wato Gombe International Hotel, sosai wajen ya haɗu komai gwanin burgewa ga kuma tsaron da dole yasa yaran Dalla barin wurin. Acan cikin babban hall din da za'a gudanar da diner ɗin kuwa, kowa zuwan ango da amarya kawai yake jira, gaba ɗaya mutanen dake wajen zuciyarsu awanke take da farinciki, yayin dasu Hayatuddeen keta ɗaukan pictures, suma zuwan ango da amarya kawai suke jira kafun nan abasu filin cashewa, don al'ƙawarine yau sai gaba ɗayansu sunnu nawa Hamma Saifuddeen ɗin gata, wannan rana itace ranan da Hayatuddeen dakuma gaba ɗaya dangin da abokan Saifuddeen ke jira, hakan yasa suke fata da burin faranta ran ɗan uwannasu tahanyar ƙawata masa bikin nasa yanda zaiyi armashi. Labarin isowar ango da amarya da MC yajine yasanyashi soma labartawa jama'an wajen cewa. "Allah yayiwa ango da amarya isowa." Nanfa kowa ya zubawa ƙofar hall ɗin ido, gaba ɗaya mutanen wajen sun zaƙu dason ganin amarya da angon. Ishaq wanda yasha dakakkiyar shaddarsa blue tare da wani haɗaɗɗen glass, wanda idan baka san shiba bazaka taɓa shaida cewa makaho bane, don kuwa komai nasa irin na masu gani yakeyi, Ishaq da kuma Ahmad haɗi da Hisham da kuma Aziz wanda yana ɗaya daga cikin abokan Saifuddeen wanda sukayi Gombe State University tare sune suka fita don zuwa taro ango da amarya, wanda dama tuni su Balkeesu da Rashida suna da ƙannan Ya Aminu yaran Yayan Baba malam da yara Goggo Maryam da dai sauran ƴan uwan amarya waje, don kuwa sune suka riƙewa amarya Zaleeha ƙasan rigarta dake da matsanancin tsawo, wanda dole ya zama sai an riƙe mata shi. Sule driver ne ya ya buɗewa Saifuddeen ƙofar motar tare da ware masa sabuwar kekensa mai azabar kyau, har wani ɗauke ido da ƙyallinta keyi Cikin azama da alamun iya sarrafa kai da cikar nitsuwa ya hawa kan keken Saifuddeen ya dai-daita zamanshi hakan kuwa sai yayi bala'in ƙarawa kwalliyar tasa armashi, don kuwa wani irin kwarjini ne yasake bayyana atattare dashi, zamansa akan wheelchair ɗin nasa sai ya ƙara masa girma da wani irin kima, ya fito tamkar jinin sarauta sule driver ne ya buɗewa Zaleeha murfin motar, ahankali ta zuro da kyawawan ƙafafunta wanda sukaji tsadaddun takalma masu kalan pitch, tana gama fitowa daga cikin motar, su Rasheeda suka tattaro ƙasan rigar nata inda suka riƙe mata shi, ahankali Saifuddeen ya danna madannin wheelchair ɗin, take yasoma tafiya dashi, cikin nutsuwa yaƙaraso inda Zaleehan ke tsaye, kasan ceqarshi dogo, kuma wheelchair ɗin yafi sauran tudu, kana tanada maddan da za'a ƙara tunda ko a rage sai ya zama yayi tsawo in ka hankosu zakayi zaton a tsaye yake hannunshi yasa ya kamo nata ya ɗan haɗe tafukan hannunsu ya rumtse. Ahankali suka soma takawa inda yake sarrafa wheelchair ɗinsa cikin nutsuwa, wani irin haɗuwa da burgewa tsarin tafiyan tasu ya bada, duk dacewa shi yanakan wheelchair ne, amma kuma sai hakan yaƙarawa kwalliyar tasu armashi, don kuwa zamansa akan wheelchair'n ya bayyana tsantsar ajinsa da kuma kwarjininsa da kima da kamala uwa uba ƙasaita, hakan yasa mutane da yawa zasuyi masa kallon zallan ajine da kasaita yasanyashi naɗewa akan kujeran, wanda saima ka lura sosai zaka iya gane cewa wheelchair ne don kuwa kujera ce mai tsananin tsadan gaske, musamman aka kawo masa ita daga Germany. Ishaq da Ahamad ne ke biye dasu, saikuma su Rashida dake riƙe da jelan rigarta, bayansu kuwa Aziz da wasu matasa wanda sune zasu bada tsoro a wurun dan yanzuma akwai mashunan UD da suke zargi a wurin. Jabeer ne da kuma Hisham ke biye dasu Ahmad ɗin a baya, sosai tsarin nasu yayi kyau, cikin nutsuwa suka kutso kansu cikin hall ɗin. Lokaci guda mutane suka somayin hanmdala sakamakon ganinsu, dan sunyi bala'in burgesu, nanfa Diamond Photograpgy suka soma aikinsu na ɗaukan hoto, sosai akeyi musu hoto, ga wani sassanya kiɗa dake tashi. Ahmad da ishaq da Salisu da Aziz kuwa da yayyafin kuɗi suka biyo bayan ango da amrya, yayinda rashida kuwa ke fesa wani abu mai ɗan karen ƙamshi kana yana bada kalan wal-wali. ɗaukansu hotuna tako ina, don sun bala'in yin kyau da dacewa, yanayin yanda Saifuddeen ke hakimce akan kujeransa shiya ƙara zautar da mutane, don hakan ya masifar ɗago ajinsa, sosai yayiwa kowa kwarjini, take ƴan matan da suka samu halartan wajen diner'n suka mato akansa, sosai dayawan mutane ke hamdala da godewa Allah, don kuwa tabbas Saifuddeen ya cika cikakken namiji kuma ingarma, maiji da tashen kyau haɗi da kwarjini, haka kuma mutane da yawa ke yaba tsananin kyawun da amarya Zaleeha tayi, don kuwa kowa na iya hango beauty face ɗinta ta cikin wani ɗan abun da aka ɗiga mata akanta wanda yaɗan rufe gefen fuskarta kaɗan, sosai su Adda Rahama ke yaba kyawu da haɗuwar Zaleeha, tabbas sai yanzu suka tabbatar da cewa bawai abanza Saifuddeen ya nace akan cewa sai ita ba, haƙiƙa Zaleeha tacika mace abunso ga kowani irin ɗa namiji, sannan kyawunta ya isa kyau, sosai kowa yaga dacewarsu da Saifuddeen ɗin, don kuwa kyaune ya gauraya da kyau. Wani irin cool music na Ed sheeran mc ya sakar musu irin mai taɓa zuciyar nan, hakanne ya ƙara bawa tafiyar da sukeyi armashi, Hayatuddeen da abokansa ne suka zo sunayi musu live vedio, Ahaka har suka ƙarasa wajen da aka ƙawata domin zaman ango da amarya, wajene wanda aka ƙawatasa da decoration mai kyaun gaske, wanda akayi amfani da colours irin na kayan dake jikin ango da amarya, cikin nutsuwa Saifuddeen yayunƙura ya sauƙa daga kan kekensa cikin nutsuwa haɗi da salon mai armashi ya hau kan wata rantsatstsiyar royal chair wanda tagaji da haɗuwa, Rasheeda ne ta zaunar da Zaleeha agab dashi har takai ga jikinsu naɗan gogan na juna. Kamar yanda aka saba ango da amarya na zuwa wajen diner ake fara gudanar da shagulgula hakanne yasanya babu wani ɓata lokaci MC yabuƙaci da babban abokin ango akan yazo yaɗan basu biography na ango. Ishaq wanda fuskarsa ke ɗauke da murmushine yataso inda ya ratsa cikin yawan jama'an tamkar wanda yake gani haka yaƙarasa gaban MC, mike ya karɓa inda yayi gyaran murya, cikin nutsuwa haɗi da kamala yasoma bada ɗan taƙaitaccen tarihin Saifuddeen ɗin, sosai biography'n na Saifuddeen ya taɓa zuciyar kusan gaba ɗaya mutane dake wajen, duk da cewa in brief Ishaq ɗin yayi komai, amma tabbas rayuwar Saifuddeen cike take da al'amura masu sosa zuciya, dayawan mutanen da basusan Saifuddeen ɗin ba, sai alokacinne ma suka san da cewa shiɗin kurmane, koda Ishaq yagama bada ɗan taƙaitaccen tarihin na saifuddeen, take jama'an wajen suka soma tafi, sosai aka jinjina gwarzantaka irin na Saifuddeen don haƙiƙa yacika Namiji. Ishaq na komawa, still Mc yasake buƙatan babbar ƙawar amarya don tazo ta bada biography na amarya. Tsulum Balkeesu tasoma ƙoƙarin miƙewa zuciyarta cike da mugunta, don kuwa dama tuni tagama kitsa kalaman da zata faɗa agame da amaryan, haka kuma tashirya gasawa Ango magana afakaice, saidai kafun ta farga sai tsintar muryar Rasheeda tayi acikin kunnuwanta, wanda sanin halin Balkeesun da mugun nufinta ne yasanya Rasheeda rigata zuwa, don tabbas tasan balallai abun da Balkeesu zata faɗa yazamanto al'khairi ba, wannan ranan kuwa ta farinciki ce, sam batason aɓata ran kowa, sudai da suka ɗaukawa kansu dala ba gammo sai suyita fama. Cikin nutsuwa Rasheeda ta ɗan bada taƙaitaccen tarihin Zaleeha, wanda kuma iya abun da ta sani ta faɗa, nan mutane da yawa suka ƙara gaskata cewa lallai Amaryar Saifuddeen ɗin ƴar ƙwalisa ce, don aɗan biography ɗinnata da Rasheeda ta bayar, zaka fahimci cewa, itaɗin ƴar ƙwalisa ce, sannan mai aji da kuma wayewa, uwa uba ƴar gidan hutu ce, sam bata wani san baƙin cikin rayuwa ba kuma ƴar gidan mutunci ce. Koda aka gama gudanar da biograpy nanfa mc yasake musu music mai daɗi da taɓa zuciya, inda aka ɗan soma ƴan ciye ciye wanda aka kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tsara abunci dana sha. Haka suka shiga gudanar da diner ɗin cikin nutsuwa, bayan ankammala ciye ciye ne, mc ya sanya wata waƙa mai daɗin gaske, nanfa ya buƙaci da ƴan uwa suzo don nunawa amarya da ango ƙauna. Aunty Rahama, Raleeya, da kuma Raihana, Aunty Kubra sune wanda suka fara miƙewa tsaye, don filin nasune na musamman, cikin yanayin taku haɗi da ɗan rawa mai burgewa suka ƙarasa kan step ɗin da ango da amarya suke, sosai suka burge kowa musamman shigar alfarman dake jikinsu tunkan su ƙaraso Saifuddeen ya miƙowa Adda Rahama hannunsa, cikin nutsuwa