Sashe 39
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sake shagwaɓe fuska yayi, duk yanda yaso Ummi ta fahimce sa, ƙiyawa tayi, daga ƙarshe ma juyawa tayi ta koma cikin ɗaki.
Ganin haka yasashi komawa part É—insa, ransa duk ba daÉ—i, wani haushin Ameenan nema duk ya cika masa zuciya, wannan rana haka dai yayi bacci zuciyarsa duk ba dadi.
Washegari.
Yana gamayin break fast ya shirya kansa, inda ya É—auki Sule driver suka nufi gidan su Ishaq, don tun adaren jiya ya tsara cewa zai je yasamu DirankaÉ—i da maganar, wato Baban Ishaq kenan."
Koda yaje Ishaq ne yayi masa jagora zuwa falon mahaifin nasa, bayan sun gaisane Saifuddeen yayi masa bayanin duk wani abun daya kawosa, ta hanyar yi masa rubutu a laptop ɗinsa.
Koda DirankaÉ—i ya karanta murmushi yayi tare da duban Saifuddeen É—in.
Cikin son basa ƙarfin guiwa yace.
"Tayaya kake tunanin cewa, bazaka iya auran mata biyu ba? Kai jarumi ne Saifuddeen, saboda haka kada kasa wani damuwa aranka zaka iya."
Nan fa Saifuddeen ya tubure masa kan cewar lallai shi bazai iya ba, ganin haka yasa Dirankaɗi ɗaukar wayarsa, inda ya ƙira Bappa Ali, shi kuma Ishaq dariyan Saifuddeen ɗin kawai yake.
Gaba É—aya abun da Saifuddeen É—in ya faÉ—a, shi DirankaÉ—i ya maidawa Bappa Ali, nan Bappa Ali yace da DirankaÉ—i, ya faÉ—awa Saifuddeen É—in, aure babu fashi, tunda Baba Malam da kansa ya yanke hukunci.
Koda DirankaÉ—i ya faÉ—awa Saifuddeen É—in, take yace.
"To Baba nifa banida kuÉ—in auren ma in da ba sadakanta iyayenta zasuyi ba".
Nan DirankaÉ—i da Ishaq suka saka dariya, dubansa DirankaÉ—i yayi tare da cewa.
"Ae dama ba kaine zaka sayi komai na auren ba, auren gata za'ayi maka ae."
Haka duk yanda Saifuddeen yaso ya kaucewa auren, Dirankaɗi da Bappa Ali sunƙi basa dama, dama shi Baba Malam baisan wainar da ake toyawa ba.
Dole haka Saifuddeen ya dawo gida, zuciyarsa cike da tunani kala-kala.
Haka akayi ta kai ruwa rana da Saifuddeen inda yaketa cemusu wai aifa Dr yace bazai iya zama da mata biyuba, Ya Adnan kuma yace a a ba wani Dr daya faÉ—i hakan.
Æangaren Baba Malam kuwa, tuni ya turawa Yaya Ahmad kuÉ—i, kan cewar ya bawa Aunty Lubna ta shiga cikin shoprite na Abuja, tayi musu sayayyan kayan lefe, wanda za'aiwa Saifuddeen sabon aure dashi.
Yaya Ahmad ne yace da Baba Malam ya amshi kuɗinsa, shi zai haɗa lefen da kansa, nan Baba Malam yace "a'a so yake komai na auren yayi da guminsa, da kuma haƙƙinsa, don ya ƙudurta aransa cewa, auren huce haushi da kuma gata zai yiwa Saifuddeen ɗin."
Can ɓangaren Zaleeha kuwa, rayuwarta mai sauƙi take gudanarwa acan garin na Numan, zuwa yanzu bata da wani abinci sai kayan fruits, dangin su apples da kuma ayaba, goiba dabina sai su water meloon, acikin ƴan kwanki kaɗan ɗin, tuni abubuwa da yawa sun sau ya mata, zuwa yanzu abu biyu ne ke damunta, wato tana jin can ƙasan zuciyarta bata son gudowan da tayi tana kewan kowa hatta su Ummi tana kewansu, ji take kamar ta koma amman da zaran ta tuna ta koma ɗin sai taji kanta yana juyawa sai taji ta gigice lokaci ɗaya taji kamar an ɗaure mata zuciyarta.
Sai kuma nata soyayyar mutumin da har yanzu takasa sake sanyashi acikin idanunta, sosai soyayyarsa ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, dashi take kwana kana dashi kuma take tashi, yayi mata tsaye acikin rai.
Yanzu ma zaune take akan katifarta, laptop ɗinta ne agabanta, inda ta saka earpiece akunnenta, wani series film take kallo acikin laptop ɗin nata, don tahakane take samun rage kewa, wayarta dake gefe ne ta soma ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Balkeesu ne ke yawo akan screen ɗin wayar, saida ta kusa katsewa ta ɗauka tare da kara wayar akan kunnenta.
Daga can ɓangaren Balkeesu tace.
"Mutanen ƙauye."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da faɗin.
"Ya akayi ne."
Balkeesu kuwa dariyar dake cinta arai ta danne tare da faÉ—in.
"Lafiya lau, ya kike kwana biyu ina ƙiran number ki baya tafiya."
Ajiyar zuciya Zaleeha ta sauƙe, cikin halin rashin kulawa tace.
"Maybe matsalan network ne."
Dariya Balkeesu tayi inda cikin zuciyarta tace.
"Ko kuma matsalan wuta ba." Afili kuwa cewa tayi.
"Dama Rabeel ne yace nayi miki magana, yana ta ƙiran wayarki amma bakya ɗauka, sannan yayi miki text duk babu reply, meyasa bazaki ɗauki wayarsa ba, ko kin manta cewar abokin aikin ki ne?."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da cewa.
"Tayaya kike tunanin zan ɗaga ƙiransa, halan ya manta cewar ina da aure ne? igiyoyin auren wani ne fa akaina, to me yasa zan ɓata lokacina nakuma ɗaukarwa kaina zunubi wajen magan, da Rabeel wanda kuma bai zama lalle dole sai munyi magana ba."
Hararan wayar Balkeesu tayi, kamar Zaleehan na ganinta, taɓe baki tayi tare da faɗin.
"Uhummm su aure manya, dama naƙira ne kawai don naji ykk, da kuma dalilin ƙin ɗaga wayar Rabeel da kikayi."
ÆŠan jim Zaleeha tayi tare da cewa.
"Bani da wani dalili naƙin ɗaga wayarsa sai na darajar auren dake kaina, kuma ma koda zai ƙira sau 100 bazan ɗaga wayarsa ba, saboda ina da aure, kuma shi ba muharrami na bane babu yadda za'ayi nayi magana dashi ina matar aure."
"Okay." Balkeesu ta faɗa ataƙaice tare da kashe ƙiran,
ita so take taga rayuwar Zaleeha tazama lalatacciya ta yadda zata samu damar maye gurbinta a ma'aikarsu da kuma gidan Saifuddeen, amman ta kaicinta ɗaya Zaleeha nada riƙo da mutuncinta na ɗiyamace musulma tana kare budurcinta da lallaɓashi tamkar ranta ga ibada.
Ita kuwa Zaleeha aje wayar tayi tare da maida hankalinta akan laptop É—inta.
Itan kuwa Balkeesu tana kashe wayan, ta saki dariyan mugunta, inda a fili tace.
"Ko ahaka aka tsaya awasan nasamu kaɗan daga cikin abun danakeso tunda ko yanzu shirinki na mushaƙata ya dawo hannuna."
Can ɓangaren su Baba Malam kuwa, gaba ɗaya sun fita daga sha'anin Zaleeha, ko zancenta ma Baba Malam baiso ayi masa.
Maryam kuwa sosai take cikin damuwa, domin kullum da tunanin Æ´an uwa da kuma mahaifiyarta take wuni, ganin yanda ta damu sosai ne, yasa Ya Ameenu É—aukan ta ya kaita wajen Baba Malam, nan Baba Malam yayi mata kalamai irin na mahaifa masu kwantar da zuciya, tare da sa mata al'barka, hakan kuwa yasa zuciyarta ta saki, kaÉ—an daga cikin damuwarta ya kau.
Rayuwar Mama a Æilliri kuwa abun yazo mata cikin wani irin yanayi, komai ba yayi mata daÉ—i, zaman takura kawai takeyi agarin nasu, yayinda Zahira kuwa kullum bata da wani aiki, sai Æ™worafi da mita, kan cewar ita lallai saida Maman ta maida ita gida, ita kuwa Mama har yanzu gani take kamar Baba Malam É—in zai sauÆ™o yace su dawo gidan, don tasawa kanta aÆ™idar cewa bazata taÉ“a Æ™iransa ta basa haÆ™uri ba, har sai shida kansa ya gaji yace su dawo.
To gatanan dai rayuwar batayi mata daÉ—i, abinci ma bata samun wanda takeso, gaba É—aya komai yayi mata duhu, badon komai ba kuwa saidan tana rayuwa acikin mutanen da gabansu da kuma bayansu duk duhu ne, basa É—auke da haske ko kaÉ—an, zaman Æillirin sam baya yi mata daÉ—i Babanta kuwa duk da kafurine yaga rashin kyauta warta, shiyasa ya tsananta mata yace gata ga Æ™auyen ta zauna kuma damuna na dawowa noma zatayi, Zahiri kuwa ji take kamar a rami take gida ba wuta bare fanka ko AC ba Radio bare tv babu firij bare kayan more rayuwa babu gado bare lafiyayyan katifa babu Æ™amshin komai sai warin burkutu, rayuwa dai ta masu tsamari gashi ita Zahira an katse mata karatu ta. Ruda kuwa Addan Mama daÉ—i hakan taji dan ko yanzu ta samu sun zama dai-dai da Æ™anwar tata, itama ta wahalan dai.
Bayan Kwana Uku, da turawa Ya Ahmad kuɗin lefe, Baba Malam da kansa ya kimtsa, inda ya tsara tafiyarsu Abuja, shi da Dirankaɗi, da kuma Bappa Ali, yayinda za suje nemawa Saifuddeen auren Ameena, Alhaji Naseer Maichanji shine mariƙi ga Ameena, wanda yake ɗan kasuwa ne sosai, hakan yasa mafi yawancin mutane sun sanshi, koda zasuyi tafiyar tasu ta yanzun da expriance ɗinsu zasu tafi, kasancewar Dirankaɗi yasan Alhaji Naseer wanda a binciken da Dr Adnan yayi akan Amina a wurin Dr Aliyu ne sukaji komai na Amina.
ananne Dirankadi ya gane É—iyar tsohon abokin kasuwancishi shiÉ—in, har ma number'n wayarsa yana dashi, domin sun sha haÉ—a busineess dashi Alhaji Naseer É—in tun shekarun baya.
To kuma bisa jagorancin Dirankadin zasuyi tafiyar da tuni sun sanarwa Alhaji Nasir Daddy kenan zuwan nasu.
Æangaren Saifuddeen kuwa shi har yanzu ganin abun yake, kamar almara, musamman idan ya tuna da cewar.
"Ameena É—in bazawara ce." Sai yaji sam shi bazai iya mu'amala da ita ba.
Ƙarfe 10 na safiya dai-dai jirgin da zai ɗaga zuwa Abuja, ya kwashi su Baba Malam da Bappa Ali. Inda suka tafi da niyar cewa bazasu dawo nan Gombe ba sai an tsaida lokaci da kuma ranan aure, don suna sa ran cewa.
"Insha Allah Alhaji Naseer É—in bazai hanasu É—iyarsa ba."
Sun isa garin Abuja lafiya, inda Ya Ahmad da kansa yaje É—auko su a airport, nan fa dukansu suka shiga motar, kaitsaye unguwar Asokoro suka nufa, wanda anan gidan su Ameena yake.
Yayinda duk abinda akeyi Amina bata da labari.
Maigadi ne ya wangale musu gate ɗin gidan, nan cikin parking space ɗin gidan Ya Ahmad yayi parking, dai-dai lokacin wani ɗan Dattijon mutumi me cike da kamala, wanda yasha adonsa cikin manyan kaya, yafito daga cikin wata ƙofa, ganinsu da yayi yasa ya nufosu cikin sauri, fuskarsa ɗauke da fara'a ya miƙa musu hannu, nan suka shiga gaisawa cikin mutunta juna, kai tsaye yayi musu jagora zuwa ɓangarensa, wani babban falo ne mai kyau, inda anan yake tarban baƙinsa masu mahimmanci.
Zama sukayi, tare da sake sabon gaisuwa.
Duban DirankaÉ—i Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Alhaji Ma'aruf ashe rai kan ga rai?."
Murmushin manya DirankaÉ—i yayi tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa Alhaji Naseer, gashi bayan lokaci mai tsawo da muka ɗauka gashi kuma mun sake haɗuwa."
Shima Alhaji Naseer É—in murmishi yayi tare da cewa.
"Allah Mai iko, gashi kuwa harda Malam Bashir Sulaiman Dukku kuka zo, a gaskiya yau gidana yana ɗauke da manya manyan baƙi, masha Allah sannunku da zuwa."
ya ƙarishe maganar yana miƙawa Baffa Ali hannu