← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 154

Sashe 138

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kai tsaye sashin Ummi ta nufa.
Da sallama É—auke abakinta ta shiga falon, rashin ganin Ummi afalon yasa kai tsaye ta nufi É—akin Ummin.
Ɗan knocking ɗin ƙofar tayi.
Daga ciki Ummi ta bada go ahead É—in shigowa.
Hakan yasa ahankali ta tura ƙofar ciki, ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
A zaune Ummin take akan gado, Raleeya kuwa fitowarta kenan daga cikin bathroom É—in Ummin, da alama wanke mata tayi.
Ganin Zaleeha yasa Ummi sakin murmushi. Ƙarasowa cikin ɗakin tayi, tare da ɗan durƙusawa agaban Ummi'n, cikin girmamawa tace. " Ummi dama inaso ne naje saloon, shine nace bana tambayeki idan kin barni sai naje." Murmushi Ummi tayi cikin kulawa tace. "Haba Zaleeha idan zakije saloon ɗin kuma sai kin nemi izinina, ai idan dai mijinki ya yardan miki kije kawai." Ƙasa ta ɗanyin da kanta, cikin wasa da ƴan yatsun hannunta tace.
"Shine yace duk inda zanje ina tambayanki, idan kinbarni sai naje." Murmushi Ummi tayi, tare da jinjina kanta, fuskarta É—auke da zallan fara'a tace.
"Na amince miki, kije saloon É—inki, Allah ya kiyaye hanya, akwai Sule driver, nasan zai kaiki ko kinaso kiyi driving da kanki?." Raleeya ce tayi carab ta cabke maganan cikin sauri tace.
"Ummi dan Allah nima zanje, dama two days ban yi saloon ba, kinga idan yaso bama sai Sule driver ya kaimu ba, ita zatayi driving É—inmu ko?." tafaÉ—a tana kallon Zaleeha'n.
Kai Zaleeha ta jinjina mata tana murmushi, dan taji daÉ—in hakan, saboda itama bawai tanason fita ita É—ayan bane, dan ance wata tafiyar bibbiyu tafi dadi. Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Kai Raleeya son yawo, to shikenan ai saiki tambayi mijinki idan ya barki ƙofa abude take." Cikin zumuɗi Raleeya tace.
"Ai namasan zai barni, bari naje na ƙirashi a waya."
taƙare maganan tana me fita waje. Zaleeha na ƙoƙarin miƙewa, Ummi ta zage zip ɗin jakan dake aje gefenta, kuɗi ta ciro wanda aƙalla zasu kai 10k miƙawa Zaleehan tayi, murya atausashe tace. "To gawannan sai ki biya saloon ɗin dashi." Idanu Zaleehan taɗan zaro tare da cewa. "Ummi ai kuɗin sunyi yawa."
Murmushi Ummi tayi, tare da girgiza mata kai, cike da ƙauna tace. "Idan Raleeya ne na bata, bazata ce sunyi yawa ba, saboda haka kema banaso kisake faɗin haka, ki amsa maza ku tafi sai kundawo, sannan kuyi driving a hankali." Cikin mutuntawa tasa hannu ta amshi, kudin tare da yiwa Ummin godiya, sannan ta fice daga cikin ɗakin, taji daɗin kuɗin da Ummin ta bata, duk da cewa ma tana da kuɗi, amma duka basu wuce 12k ba, dan koda Saifuddeen ma yace da ita, akwai kuɗi a drawer ɗinsa, idan tana da buƙata ta ɗauka, sam bata ɗauka ba. Tana zama afalo kuwa Raleeya ta fito itama cikin shirinta na doguwar riga, saidai nata me kalan ja ne, dan ta tambayi Ahmad ya barta, dama shi bame hana fita bane.
Atare suka fito compound ɗin gidan, zuƙeƙiyar motar Saifuddeen ƙiran mercedess benz Zaleehan tasawa key ɗin data ɗauko a ɗakinshi ta buɗe musu, Zaleehan ne ke driving, Raleeya kuwa na gefen me zaman banza, me gadi ne ya wangale musu gate ɗin gidan suka fice. Kaitsaye babban shagon saloon ɗin da Zaleehan ta saba zuwa suka nufa, suna zuwa kuwa akayi musu saloon ɗin, harma da wankin ƙafa akayiwa Zaleeha.
Basu wani É—au lokaci ashagon ba, kwata kwata basu wuce 1hour and 30minute ba, aka kammala musu komai.

Koda suka dawo gida kuwa, lokacin har anyi sallan azahar, sallah kawai sukayi, suka wuce kitchine, sosai Zaleeha ta baje basiranta wajen shiryawa su Saifuddeen É—in abincin tarba me rai da lafiya.
Basu gama abincin ba kuwa har tsawon awa 2 harma da wasu mintuna. Koda suka kammala agajiye suke hakan yasa kowacce ta wuce ɗaki taɗan kwanta, Zaleeha kuwa koda aka ƙira sallan la'asar, tashi tayi ta ɗauro alwala, tana idarwa kuwa ta sake komawa ta kwanta. Da misalin ƙarfe biyar da rabi kuwa ta kuma faɗawa bathroom, wanka tayi me rai da lafiya. Tana fitowa ta shafe jikinta da mai haɗi da turaruka masu azababben ƙamshi me kama zuciya,
zama tayi agaban mirror tare da tsantsarawa fuskarta kwalliya me kyau, duk da bata cika meckup ɗin akan fuskarta ba, amma tayi kyau sosai, drawern ta ta buɗe, inda ta zaro wani jan yadi na mata me masifar kyau da kuma tsada, dan aƙalla kuɗinsa yakai kusan 30k, ɗinkin riga da sket pieces akayiwa yadin, wanda aka ƙawata gaban rigan da black ɗin stones, sosai kayan suka zauna mata ajiki, sun kuwa fito da zallan kyawun surarta, dogon gashinta ta tubke, kana ta ɗaureshi da ribbom me golding colour, saboda akwai ratsin golding ajikin kayan nata. Wani irin haɗaɗɗen material saree me kalan golding ta ɗan yane jikinta dashi, kasancewar yana da shara shara sosai hakan yasa ko kaɗan bai ɓoye ado da kwalliyan nata ba, saima ƙarawa shigar tata kyau da yayi, dan tafito kaman sarauniya.

Ɓangaren su Saifuddeen kuwa ƙarfe 5:40 pm jirginsu ya sauƙa cikin Gombe International Aiport,
Ahmad da kuma Ishaq sune waƴanda sukaje tarosu, ƙwarai sun ji daɗin ganin yanda jikin Saifuddeen yayi kyau, suna shiga mota kuwa suka kamo hanyan gida. Acan gidan nasu kuwa, tuni sashin Ummi ya karɓi baƙoncin su Adda Rahama, harma dasu Wareesu, Zakariyya ma yazo suna nan tare da Hayatuddeen da kuma Khamis.

Horn ɗin motarsu da Zaleeha taji alaman cewa sun iso, yasa ta cikin sauri ta ƙarasa jikin windown ɗakin nata, ɗan yaye labule tayi waiko zata hangosu, amma gaba ɗaya shuke shuken dake wajen sun hanata ganinsu, hakan yasa ta koma cikin nutsuwa ta cigaba da kimtsa kanta. Saifuddeen kuwa, sashin Ummi suka wuce, baƙaramin farinciki Ummi tayi ba da ganinsa, musamman ma yanda taga jikin nasa ya miƙe ya samu lafiya, yana zaune abunsa, yasake kyau da burgewa, da'alama bashi da wani abun dake damunsa. Shima yaji daɗin ganin Ummin nasa sosai. Gasu Adda Rahama da farincikinsu ya kasa ɓoyuwa.

Zaleeha wanda ta fito daga sashinta, ahankali take tafiya tamkar wata tauraruwa, tayi kyau matuƙa, ƙamshi ne kawai ke tashi ajikinta, kaman wanda akayiwa ɓarin turare.
Tun isowarta kusa da sashin Ummin take jiyo surutan su Raleeya da kuma nasu Ishaq, idanunta taɗan lumshe sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar, cikin ƴar siririyar muryarta tayi sallama anutse ta shigo cikin ɗakin, jin daddaɗan muryarta ya sashi juyowa, sauƙe idanunsa da yayi akan kyakkyawar fuskarta yasa shi ɗan lumshe idanunsa, zuciyarsa ce ta amsa saboda yanda yaga tayi kyau sosai. Wani irin lallausan murmushi ya sakar mata, tare da ɗan sake lumshe tsumamun idanunsa. Itama idanun ta lumshe dan ganinsa, yasa taji wani irin sanyi acikin ranta, ƙarasowa cikin falon tayi, kaitsaye wajen Ameenah ta nufa, fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Barka da dawowa Ummun Adeel ya hanya?".
Murmushi Ameena tayi tana meƙarewa Zaleehan kallon dan ko ita kanta, tasha jinin jikinta da kyawun Zaleehan. Cikin sakin fuska tace. "Yauwa Ammin Adeel, sannu da gida, hanya kam munshata saidai gajiyan zama da kuma ciwon jiki, shima nasan asannu zai watse." Murmushin Zaleehan tayi tare da sanya hannu ta ɗauki Adeel da tun shigowarta yake ta wuntsil wuntsil da hannunsa, yanaso yazo wajenta. Rungumeshi tayi tanayi masa wasa, ɗan juyowa tayi inda Saifuddeen ɗin ke zaune taɗan saci kallonsa, idanunsune suka gauraye acikin na juna dan dama shidinma kallonta yake, saurin lumshe idanunta tayi, asanyaye cikin daddaɗan muryanta tace.
"Sannu da dawowa ya jiki?."
Shiɗinma idanunsa ya lumshe saboda yanda yaji zazzaƙan muryarta ta ƙara daɗi, ga kuma ƙamshinta da gaba ɗaya ya cika masa hanci. Kansa ya jinjina mata alaman lafiya, tare da binta da wani irin fitinannen kallo, mai ɗauke da zallan kewa da kuma ƙauna.
Zama tayi agefen Zakariyya da kuma Hayatuddeen, sama sama take ɗan satan kallonsa, dan baƙaramin kyau taga ya ƙara ba, shiɗin ma dai satan kallonta yakeyi, dan tayi masa kyau sosai. Basu wani jima afalon Ummin ba, aka soma ƙiran sallan magriba. Saida ya koma part ɗinsa yaɗan watsa ruwa sannan ya wuce masallaci, Zaleeha kam kasancewar tana da alwala anan part ɗin Ummi tayi nata sallan ita da Raleeya, dan Ameena ma tatafi part ɗinta saboda tanaso taɗan watsawa jikinta ruwa.

Basu dawo daga masallacin ba saida akayi sallan Isha, atare dukansu dasu Ishaq suka dawo daga masallaci, nan falon Ummi suka baje, Zaleeha da kanta ta jere musu gaba É—aya abincin da ta girka musu kala, da kuma drinks.
Ita da kanta tayi seving ɗinsu, duk motsin da zatayi kuwa akan idanunsa, dan baya ko ƙaunar ɗauke idanunsa akanta. Atare suka zauna dukansu sukaci abincin, hira sukeyi sosai, saidai duk acikin hiran nasu, Saifuddeen da body language yake magana, kasancewar Zaleeha na wajen.
Suna kammala cin bincin, Zaleeha ne ta tattare wajen, É—aukan Adeel tayi ta É—aura akan kafaÉ—anta, sannan ta fice daga cikin falon.
Chapter 138 · 0% Book details