← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 154

Sashe 4

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wunin ranan masu gyarannan suka gama komai na side d'insu Saifuddeen kafin azahar sun gama komai na side d'in masu buga kitchen cabinets ma sunzo sun shirya komai ras.
masu fenti kuwa sun fento ko ina na gidan luggu da sak'o da yake sunada yawa kuma akwai kayan aiki kafin magrib dai sun gama komai gidan ya zama sabo fil yayi ras sai shek'i yakeyi da k'amshin sabon fenti.
In da akayiwa gidan fentin Coral color iya rabi daga k'asa kuma dama tayis ne manne royal color hakan yayi masifar kyau ya haska gidan,
cikin gidan kuwa Side d'in Ummi pumpkin color akasa daga saman pop d'in daga k'asa kuma navy blue mai shek'i,
hakama saman inda Hayatuddee yake, inda Saifuddeen yake kuwa ba'a tab'abashi ba dan bai jimaba,
Sai inda Raliya take mai mak'otaka da inda za'a ake shirin sa Zaleeha, mint green and white akayi mata komai yayi ras, sai wojen part d'in duka da aka fente da dark brown and daga d'an k'asan kuma tayis ne manne a jikin ginin,
sai farfajiyar wurin da yakeda d'an zagayeyyen ma dai-daicin lambun da yakeda yabanyar grass carpet wanda yayi kore shar, sai bishiyar mangoro mai fad'i da tsananin duhu wanda yake baje kan bishi yoyin dabino da ayaba da gwaiba dake gefenshi dan bishiyar mangoron bata da tsawo sosai, a k'asan kuwa fulawowi ne jere wanda sune suka zama garkuwan wurin sai ya zama in kana cikin wurin baza'a hangoka ba, cikin wurin kuwa sai wasu fulawi masu halittar tim-tim in ka gansu kamar kujeru, kana ga kan pompoms guda biyu wanda dasu akeyiwa wurin ban ruwa, daga tsakiya ciluk kuma wani k'arfe ne mai tsawo wanda yake manne da fitilar sola mai d'an karen haske.
sai irin kujerun silver nan da ake ajewa a asibitoci da wuraren shak'atawa, kujerun ne suka zageye wurin da k'asanshi ke wadace da koriyar ciyawar, ga sanyin tsirrai gana ruwan dake gudana a wurin ga na inuwar bishiyar mangoro dana dabino da gwaiba, uwa uba ga sanyin bishiyoyin ayaba kusan guda biyar da suka zagaye wurin,
daga cikin wojen wurin kuwa an lailayeshi da intalak, sai babban baranda mai fadin da aka laileyeshi da tayis fari k'al.
kana cikin parlour kuwa yasha fenti purple and cerise color sosai parlour yayi kyau hakama cikin two bedroom d'innan, kitchen d'inta kuwa an k'awatashi da durowowi masu kalar pink and white sosai aka k'awata kitchen d'in.
komai fa yayi ras sai shek'i da k'amshi gidan keyi,
hakama fulawin gidan duk anbi an musu sassariya an dai-dai tasu,
garden dake bayan part d'in Ummi ma an gyarashi sosai,
gida dai ko yanzu amarya tazo...

Juyi take tayi akan makeken gadon nata,  gaba ɗaya damuwa ya cika zuciyarta, wani irin zafi takeji acikin ƙirjinta,  rumtse idanunta tayi, take wasu irin hawaye masu zafi suka kwaranyo daga cikin idanunta, ya zatayi? wazata kaiwa kukanta ya share mata hawaye?  burinta shine koda mutum ɗaya ne ya fahimceta, amma ankasa samun hakan,  sosai zuwa yanzu ƴan uwanta keyi mata kallon wanda aljanu suka kama,  laɓɓanta ta ciza tare da sakin wani marayan kuka mai sauti, ta lura shi wannan nakasashen jikinshine a nakasashe zuciyarsa cike take da jarumta, dan ta fahimci duk baraza da ihu da hargowar da take mishi akan ransa da rayuwarshi a banza, babu alamun karaya bare fargaba ko d'igon tsoro, asalima sai tsoronshi dake cika mata idanu muddin ta kalli kwayar idanunshi koda na one second ne.
Juyi ta kumayi tare taune lip d'inta na k'asa ayanzu tafi buƙatarsa fiye da dacan baya, fatanta burinta, muradinta duk sun ta al'laƙane akansa, sam soyayya batayi mata adalci ba da ta jefata cikin mawuyacin hali,  hannunta ta sanya ta dafe dai-dai saitin zuciyarta dake bugawa, tanajin sonsa na fusgarta, wani irin maganaɗisun ƙaunarsane ke ƙara janta akowacce rana,   yaya zatayi da soyayyarsa dake ƙoƙarin fasa mata zuciya?
Ƙaddara tazo mata ayanda bata taɓa zata ba, ƙaddara ta zautar mata da tunani, har takai ga tanayin komai cikin zaucewar hankali.
Sosai tayi hugging pillow, ahankali taci gaba da rera kukanta, saida tayi kuka sosai kafun wani wahalallen bacci ya É—auketa.

Washe gari.

Zaune suke su dukansu akan babban dinning table ɗin dake  cikin falon, Saifuddeen, Hayatuddeen da kuma Raliya, sai Ahmad wanda shigowarsa cikin falon kenan.
Ahankali Saifuddeen ke tsakalan abincin yana kaiwa bakinsa,  gaba ɗaya hankalinsa naga wayarsa dake riƙe ahannunsa, sosai yashiga busy tunda aka fara shirye-shiryen bikin, dan ma yanada tarin aminai dake ji da komai wani abinma sai dai kawai yaga anyi sosai suke shiryawa bikin inda ya kama yau saura kwana uku bikin.
Tunani yakeyi akan tirelar dake can harabar gidan nasu wanda aka kawo kayan Zaleeha. Tirelan cike yake dam da kayan Zaleeha wanda Ya Ahmad yayi mata komai na duniya wanda amare zasu buk'ata.
Wanda Habu ya bada shawaran kada a sauk'e kayan a gidansu a wuce dashi gidan Saifuddeen d'in acewarsa k'arin jidaline.
to koda ya gayawa Ahmad sai suka bawa driver'n tirelar hak'uri akan zasu biyashi abar kayan a ciki sai an gama gyaran side d'in amaryar sai su sauk'e kayan to su kuwa jin za'a biyasu yasa suka amince.
to an gama gyara a bisa tsarinsu dai gobe za'a zo a sauk'e kayan sannan tuni Salisu ya nemi masu had'a kayan su shirya za'a biyasu dubu saba'in kud'in aikinsu kana Maryam da Aunty Lubna zasu zo su kimtsa komai duk a goben...

Ummice ta ƙaraso cikin falon, cikin shirinta tsab, sosai tasha ado irin wanda ya bayyana cikar kamalarta, tana ƙarasowa cikin falon gaba ɗaya kallon ƴaƴan nata ya dawo gareta.
Ahankali Saifuddeen ya É—ago da kansa ya kalli Ummin nasa, ganin yanda tayi masa kyau yasanyashi sakin murmushi, tare dayi mata duban tsab, domin yaga alaman cewa fita zatayi.
Ƙarasowa dinning area'n Ummi tayi, hannu tasanya ta shafa kan autanta Hayatuddeen dake ta faman zuba wa cikinsa, spiring roll.
Fuska Saifuddeen ya kwaɓe tare da karyar da wuyansa gefe,
Matsanancin tausayinsa ne ya cika zuciyar Ummin, don sarai ta fuskanci abun da yake nufi, alamune dake nuni yanada yar damuwa can k'asan zuciyarshi wanda kuma baya son ta sani, ita kuwa in taga hakan bata matsa mishi kan ya sanar mata sai dai takanyi k'ok'arin sashi farin ciki, sai dai tasan yanzu koma menene aransa baya rasa nasaba da Zaleeha,
hannu tasa ta shafa kansa shima.
Murmushi yayi inda cikin body language É—insa yayi mata alaman da ina zataje.
Itama murmushin tayi tare da gyara tsayuwarta, duban Æ´aÆ´an nata tayi dukansu, tare dayi musu bayani akan zuwanta Dukku da ta tsarashi yau da safe, sannan kuma ayau É—in zata dawo, sosai suka É—anyi mamaki sai-dai kuma sanin cewa ana tsaka da shirye-shiryen hidiman biki ne yasanya basu damu ba, don atunaninsu wani uzurine wanda ya shafi bikin zai kaita Dukkun.
Haka Ummi tayi sallama da su, inda dukansu suka rakota har compound É—in gidan.
Saida suka ga tafiyarta kafun su dukansu suka koma cikin gida.

Kusan ƙarfe shabiyu da wasu ƴan mintuna Ummi suka iso cikin garin na Dukku me al'barka.
Kaitsaye gidan Bappa Ali suka sauƙa.
Sosai Aunty Mina tayi murnar ganin Ummin, nanfa lokaci É—aya tacika mata gabanta da kayan ciye ciye, hadda dangin su fura da nono,
Sosai Ummi da Auntyn ke shan hiransu, kasancewar Bappa Alin bayanan, sunje gaisuwan wani abokinsu wanda bashida lafiya, shida Malam Ashiru.
Cikin ikon Allah Kuwa Ummi na idar da sallan azahar saiga Baffa Alin ya shigo, koda yaga Ummin yaji daɗi, saidai kuma zuciyarsa ta basa kan cewa ba lafiya ba, domin lafiya ƙalau babu abun da zaikawo Ummi Dukku ana tsaka da shirye shiryen bikin Saifuddeen kana kuma jiya-jiya nan sukaje amsa kiran nata.
Bayan sun gaisa da Bappa Alin ne Ummi ta gyara zama, lokaci É—aya damuwa ya bayyana akan fuskarta, dubanta Baffa Ali yayi cikin sanyin murya yace.
"Lafiya kuwa? badai wanine bashida lafiya acikin gidan ba?."
Kai Ummi ta girgiza cikin ƙunan zuciya tace.
"Akan maganan auren Saifuddeen da yarinyar nanne, kamar yanda na faɗa muku kaida Malam Ashiru jiya cewa yarinyar nan batason Saifuddeen, tana masa barazanar matuƙar ya aureta zata kasheshi, to fa yanzu abin k'aruwa yakeyi dan bata daina ba, awancan karon kun tausasheni ta hanyar cewa nayi haƙuri nabari ayi auren, na haƙura badon raina yana soba, saidai ayanzu bazan iya haƙura ba, inamatuƙar jin tsoron abun da zai faru anan gaba, inatsoron rasa Saifuddeen, Bappa Ali kasan yanda Saifuddeen yake awojenmu dan Allah Kayi wani abu!."
Nan ta kwashe duk kan abun daya faru da kuma text message É—in da ta karanta wanda Zaleehan ta turowa Saifuddeen ta faÉ—a masa.
Ajiyar zuciya maiƙarfi Bappa Ali yayi, tare da sanya hannu ya ɗan dafe kansa, tabbas zuwa yanzu yakamata yabita maganan Ummi, don kuwa tabbas ayanda Zaleehan ke faɗa da kuma bayyana tsanar Saifuddeen afili tabbas zata iya aikata koma miyene don ganin ta cutar dashi, tabbas shima zuwa yanzu kam yafara tsorata da al'amarin.
ÆŠan jim yayi tare da gyara zamansa, cikin kulawa yace.
"Insha Allahu Ayau yau ɗinnan zan ɗauki Malam Ashiru mu tafi Gombe tun lokaci bai ƙure mana ba, haƙiƙa wannan lamari yayi tsaurin da dole sai manya sun shiga cikinsa, ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zamuje mu samu shi Malam ɗin, zamuyi magana ta fahimta dashi, bakuma zamu ɓoye masa komai dake faruwa ba, tabbas nasan zai fahimce mu, shi kuma Saifuddeen Allah yabasa wata mace tagari wacce ke ƙaunarsa!."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ummi ta sauƙe tare da cewa "Ameen!."
Har cikin ranta taɗanji sanyi, haka dai suka ɗan taɓa hira kaɗan kafun daga bisani tace zata koma.
Haka suka rakota har wajen mota inda Sule driver ke jiranta.
Haka Ummi suka kama hanyar shigowa cikin garin Gombe zuciyarta wasai, tanajin kamar ta raba Saifuddeen da ƙaya.
Tafiyar 1 hour ne kacal ya kawosu Gombe, inda ta koma gida zuciyarta cike da salama, saidai kuma ta wani ɓangare, cike take da tausayin Saifuddeen, domin kuwa koda sau goma zata kalleshi, to akowani kallo ɗaya, saita hango zazzafar ƙaunar da yakeyiwa Zaleeha acikin ƙwayan idanunsa.
Amma addu'a bata bar komai ba. Zata tayi masa addu'a akan Allah Ya musanya masa da mafi alkhairi.
Chapter 4 · 0% Book details