← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 154

Sashe 144

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Da dare kuwa ƙarfe 8 dai-dai za'a fara diner, wanda kuma shida Zaleeha ne zasu je, koda ya dawo daga sallan isha, part ɗinsa ya wuce, sabon wanka yayi, koda ya fito daga wankan rigar wankane irin fara ƙal ɗinnan ajikinsa, gaban dressing mirror ya ƙarasa, mai ɗinsa me daɗin ƙamshi ya shafa sannan ya feshe jikinsa da turare, ƙarasawa gaban drawer'nsa yayi, wata irin haɗaɗɗiyar getzner me masifar kyau da tsada ya zaro, wanda taji ɗinkin half jamfa da kuma wando, sosai aka ƙawata gaban blue colour getzner ɗin da haɗaɗɗen aiki me burgewa, koda yasa kayan sosai suka zauna ajikinsa, yayi matuƙar kyau, wani haɗaɗɗen blue half cover shoe ya sanyawa fararen kyawawan ƙafafunsa, wata haɗaɗɗiyar hula mai ɗan ratsin blue ya sanya akansa, tare da ɗaurawa wrist ɗinsa tsadadden agogon apple, yayi kyau sosai sai baza ƙamshi yake.

Acan sashin Zaleeha kuwa saida tayi wanka, sannan tayi sallan isha, tana idar da sallan mai ta shafa, kana tabi jikinta da daddaɗan humra me ƙamshin gaske, zama tayi akan stull inda ta shiga tsantsarawa fuskarta meckup, take zallan kyawunta ya sake bayyana, tana kammalawa kuwa ta ƙarasa gaban drawer glass ɗinta, wani tattausan yadi me kalan blue and peach colour ta ciro, yadi ne me azabar kyau da tsada, dan sai shining yake yana ɗauke ido, ɗinkin doguwar riga akayiwa yadin, wato fitted shape gown, dikine da yayi matuƙar kyau, koda tasa kuwa ɗas ya zauna ajikinta, yayinda ya bayyana haɗaɗɗen surar jikinta, ga kuma shape dinta daya ƙara bayyana, hips ɗinta sun ƙara girma sabida jaririn cikin dake gareta, tubke dogon gashinta tayi, sannan ta kafa ɗaurin ɗan kwali me kyau akanta, take ta fito ɗas da ita, wani haɗaɗɗen sarƙa da ɗan kunnen gold ta sanya, wanda ya ƙarawa shigar tata armashi, dogon takalmi ƙiran kamfanin Italy ta sanya aƙafanta, wanda yake shima blue ne me ratsin peach, ganin yanda shape ɗin jikinta ya bayyana yasa, ta yane jikinta da wani zazzafan lafaya babban mayafi me shara shara, saidai har sama ta ɗaura mayafin akanta ta yane kanta tamkar balarabiya, tayi kyau sosai sai baza ƙamshi take, ƙoƙarin fita daga cikin ɗakin take, ya rigata, ahankali ya turo ƙofar ɗakin nata ya shigo.
Idanunta taɗan lumshe sakamakon wani daddaɗan ƙamshinsa da ya bugi hancinta, ahankali taɗan ware idanun nata ta sauƙe su akansa, yayi mata masifar kyau, har batasan sanda ta saki wani irin ƙawataccen murmushi ba, shiɗinma idanunsa ya zuba mata, dan hakanan yake ga kamar yaune ranan daya fara ganinta, tasake kyau da cika, ga wani irin hasken da ta ƙara, fatarta so smoth har ɗauke ido take, murmushi ya sakar mata, tare ta bude mata duka hannuwansa alaman ta zo, babu musu kuwa cikin nutsuwa ta ƙarasa garesa, saidai bata shiga jikinsa kaman yanda ya buƙata ba, saboda yana zaunene akan wheelchair ita kuma tasaka hill shoe, hannunsa ta kama ɗan ƙasa tayi da kanta, cikin nutsuwa tace.
"Kayi kyau sosai, saidai kuma gaskia am jealousy."
Idanu yaÉ—an zaro cikin body language É—insa yace.
"Because of what?." Idanunta taÉ—an juya, akasalance tace "Saboda nasan bani kaÉ—aice zanga wannan kyawun naka ba, nasan Æ´an matan wajen diner É—inma zasu gane mana kai"
ƙasa-ƙasa tayi maganan tayanda tasan bazai fahimci abun da take faɗa ba, saidai abun da bata sani ba shine, yajita raɗau da kunnuwansa, wani irin haɗaɗɗen murmushi yayi, ahankali yaɗan murza ƴan yatsunta dake cikin tafin hannunsa, yi yayi kamar baiji maganan ba, cikin body language ɗinsa yace. "Kema kinyi kyau sosai, kina ta shining like sabuwar amarya." Murmushi kawai tayi masa, tana ɗan satan kallonsa, cikin ranta kuwa moment dinsu na ɗazu take tunowa, tabbas yasata acikin wata duniya me daɗin gaske, batasan cewa sex na da daɗi ba sai ayau, duk da cewa ta ɗanji zafi, amma zafin ɗan kaɗanne daɗin da taji yafi zafin yawa. Hannunta dake cikin nasa ya kama suka fita daga cikin ɗakin, kaitsaye sashin Ummi suka nufa, ganin sun kusa kaiwa falon Ummi yasa ta janye hannunta daga nasa, suna shiga falon kuwa suka iske Ummi da Raleeya da kuma Ahmad azaune suma cikin shirgarsu ta alfarma da shirin fita, gefe Hayatuddeen ne ke zaune yasaka roban Ice cream agaba sai sha yake, yana jujjuya kai, dan earpiece ne akunnensa.
Ummi na ganinsu haka ta saki murmushin jin daÉ—i, dan tabbas sunyi kyau sosai, ga kayansu kala É—aya, sunfito ras dasu gwanin burgewa. Saida Ahmad yaÉ—an tsokane su sannan sukayiwa Ummi sallama, har bakin mota Hayatuddeen ya rakasu, saidai awannan karon ba Saifuddeen É—in bane zaiyi driving, Sule driver ne Ahmad kuwa da Raliya suma motarsu suka shiga,
saida Hayatuddeen yaga tashinsu sannan ya koma cikin gida shima ya ƙarisa shirinsa dan Khamis zai biyoshi suje suda Imran, Sulaiman, Isma'il Zakariyya.

Suna ɗaukan titi taɗan jinginar da kanta akan kafaɗansa, lumshe idanunta tayi tana shaƙan ƙamshin jikinsa, ganin haka ne yasa shi zura hannunsa a ƙugunta ya rungumota, ahankali yake ɗan hura mata iskan bakinshi akan fuskarta, hakan kuwa sosai yayi mata daɗi, gaba ɗaya sun shagala hannunta tasa tanata shafa sajenshi, ahaka suka ƙaraso wajen da za'ayi diner'n, wato Madugu Guest Palace, sosai wajen ya ƙawatu da decoration me kyau da burgewa, gaba ɗaya wajen cike yake da jama'a, kusan kowa yazo, amma Ishaq yakafe kan cewar baza'a fara gudanar da diner ɗin ba, har sai anjira Amininsa wato Saifuddeen ya ƙaraso.
Da isowarsu kuwa MC yafara shelan zuwansu, nanfa jama'a suka zubawa ƙofar shigowa ido, dan ganin wanene shi Aminin Ishaq ɗin, da kusan inbashi babu biki. Cikin nutsuwa suka raso cikin hall din, hannunsu sarƙafe acikin na juna, sunyi wani irin fitinannen kyau da dacewa.
Suna shigowa kuwa waje ya ɗinke da surutu, dan kowa ganinsu yake tamkar taurari ne suka sauƙo ƙasa, saboda tsabar haɗuwa, kyau, da kuma dacewa, har wani irin yanayin kama sukeyi, wanda hakan yasa suka ƙara ƙayatarwa. Har suka ƙarasa wajen zaman da aka tana da musu na musamman, MC baidaina wasa suba, mutane da yawa saidai kawai suce.
"Masha Allah." dan kuwa su Saifuddeen ɗin sunyi kyau matuƙa. Suna zama kuwa aka soma gudanar da diner ɗin, sosai abun ya ƙayatar, dan babu laifi Ishaq ya kashe kuɗi sosai, hakama Saifuddeen kusan komai shiyayi, dan wani abun ko Ishaq yace bazaiyi ba, saboda kashe kudin zaiyi yawa, Saifuddeen ne ke tuburewa, yace sai anyi, babu wani nuƙu-nuƙu kuma ya buɗe bakin al'jihunsa, dan yanason bikin abokin nasa kuma amininsa yayi armashi. Alhamdulillah anyi diner lafiya, taro yayi daɗi, haka kuma anci ansha ankuma yi ɓarin naira, biki dai saidai ace masha Allah.
Chapter 144 · 0% Book details