Sashe 24
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aƙofar gidan yayi parking motarsa, inda yayi knocking gate ɗin gidan, maigadi ne ya leƙo tare da buɗe masa, duban maigadin Ya Habu yayi tare da basa hannu suka gaisa, dai-dai lokacin kuma Ahmad yafito daga part ɗin Ummi zaiyi nasu sashin, ganin Ya Habu yasanyashi ƙarasowa wajen daɗan sauri, nan yabawa Ya Habu hannu sukayi musabaha koda Habun ya gaya mishi saƙon Baba Malam, Ahmad ɗinne yayi masa jagora har zuwa part ɗin Ummi, amutunce suka gaisa da Ummi, bayan sun gama gaisawanne yayi musu bayanin cewa Baba Malam ne yaturosa akan cewa ya tafi da Zaleeha, aikuwa sosai zuciyar Ahmad tayi fess, Ummi ne tace da Hayatuddeen yaje yaƙirawo Zaleehan, don kuwa har yanzu tana nan a part ɗin Raliya.
Koda Hayatuddeen yaje part ɗin Raliya, nan ya iskesu sunata hira, shaida mata ƙiranta da akeyi yayi,
"Aunty Zaleeha Ya Habu yazo yana falon Ummi yace kije."
Cikin tsoro da fargaba tace.
"Ya Habu kuma! Shi da waye?."
murmushi Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Ya Habu fa nace ba dodoba, shi kaÉ—ai mana yazo, kinga yace kiyi sauri gida zakuje tare."
Ƙulullluuuu cikin Zaleeha ya bada sautin murɗa a take cikinta ya ɗuri ruwa, nan ta cika da fargaba haɗi tsoro,
cikin tankwashe wuya ta kalli Hayatuddeen tare da cewa.
"Pleees je kace baka ganni ba."
Sosai suka cika da mamaki,
Kai Raliya ta sunkuyar dan kar dariyan da ke sun kubce mata ya baiyana a fuskarta, cikin mmki tace.
"Ya kuma zaije yace bakyanan bayan kuma gaki?."
kwaɓe fuska tayi tare da cewa.
"Eh yaje yace ina bacci to."
sosai tsoronta ya baiyana a fuskarta ganin hakan yasa yakoma falon Ummi yafaÉ—i cewa.
"Bai ganta ba." Hararan da Ahmad ya watsa masa ne, yasan yashi faÉ—in gaskiya inda yace.
"Tace nace banganta ba, ko kuma ince tayi bacci."
Nanfa Ya Habu yacika da mamaki, take kuma yaji ransa ya ɓaci, ta tabbata mara gaskiya kenan, sake tura Hayatuddeen ɗin yayi akan tazo, nan ma Hayatuddeen yaƙara dawowa, yace tace wai batanan, haka akayi juyin duniya akan Zaleeha tazo, amma ina sam taƙi zuwa, daga ƙarshema ɗakin Raliya ta gudu ta ɓuya.
Rai aɓace Ya Habu yafito yabar gidan.
Yana zuwa gida ya iske Ya Ameenu da Baba Malam azaune, cikin ƙunan zuciya ya kwashe duk abun da ya faru ya faɗawa Baba Malam,
sosai Ya Aminu ya hatsalo gaba ɗaya jikinshi rawa ya ɗauki saboda matsanancin ɓacin rai da zafin zuciya irin nasu na sojoji da kuma fulani ji yake muddin gata gashi zai kakkarya mata ƙafafuwa yaga gobe da wanne sawun zataje yawon.
Me Zaleeha takeson maidasu ne?, me take nufi dasu? Wai ko dai gani take tafi ƙarfinsu ne? miƙewa yayi tare da cewa.
"Bari inje in taho da ita!."
Kai Baba Malam ya gyaɗa mishi dan fitinar Zaleeha tana tafasa mishi zuciya tana gab da ƙureshi.
Ahmad na zaune afalo suna mamakin halin na Zaleeha, saiga ƙiran wayar Ya Aminu yashigo wayarsa, ɗauka yayi ko gaisawa Ya Ameenu bai bari sunyi ba, yace da Ahmad ɗin yana ƙofar gida,
cikin jin daÉ—i Ahmad É—in yasanar dasu Ummi da Saifuddeen.
Sannan yafita ya shigo da Ya Ameenu'n, gaisawa sukayi sannan Ahmad ɗin ya dubi Saifuddeen, cikin nutsuwa yayi wa Saifuddeen ɗin alama kan cewar yayi haƙuri, zasu tafi da Zaleehan, Baba Malam ne ke nemanta, cikin body language Saifuddeen yace.
"Bakomai" dan shi kanshi yana cike da son sanin ina take zuwa ta kwana.
Shikuwa Ya Ameenu kai tsaye cewa kawai yayi anuna masa É—akin da Zaleehan take, a bashi izinin shiga zata fito, nan Ahmad mugu yace.
"Ba komai ya Ameena ai kai ba baƙo bane, tana ɗakin Raliya muje in nuna maka ɗakin".
cikin zafin jini Ya Ameenu yabi bayan Ahmad da yake ta dariyar zuci so yake adaka mishi hegiyar yarinyar nan mai ladabin kura
Zaleeha na rakuɓe ajikin bango suna magana da Raliya sai gani tayi an turo ƙofar ɗakin, koda takai dubanta ga ƙofar kuwa saida numfashinta yakusan ɗaukewa ganin Ya Ameenu a bayan Ahmad sam bata tsammaci ganinsa ba, aruɗe tasoma ƙoƙarin guduwa, taku ɗaya yayi ya cafkota tare da wanka mata wani irin gigitaccen mari, wanda yasanya tasaki wata irin razanannen ƙara, take tasoma ƙoƙarin shiɗewa, aharzuƙe Ya Ameenu yace.
"Wato har kinyi girman da Baba Malam zai aiko ƙiranki kiƙi zuwa ko?, wuce muje kona kakkaryaki anan wajen, mahaukaciya kawai muje yau sai kin gaya mana gidan ubanwa kike zuwa ki kwana?!!."
Cikin É—imaucewa Zaleeha ta wuce gaba, tare da fara tsalle tana yarfa hannu cikin kukan gano yau sai dai buzunta dan ta lura zargin yawo Ya Aminu da sauran Æ´an uwanta suke mata.
jin ya sake yarfa mata wasu tagwayen marukane tare da ce mata.
"Gidan ubanwa kike zuwa ki kwana? Wato mu zaki maida sakarkaruko? Wato yawon lalata kikeson ki koyaka?."
wani irin tsalle ta rinƙayi tana yarfa hannu cikin tsananin kuka da tsoro tace.
"Wallahi Ya Ameenu ba yawon lalata nakeyiba, a cikin gidannan nake kwana cikin garden nake kwana wlh bana fita ko ƙofar gidan."
Ummi kam dake falonta jin kukan Zaleeha ne yasata saurin juyowa ta kalli Saifuddeen dake kallonta tace.
"Kai Saifuddeen dukanta fa sukeyi ,kada ka bari su tafi da ita zasu illatata,wannan sojanefa ya saba dukan garadai kar ya illatamin yarinya mai biyayya."
kai ya jujjuya mata tare da haÉ—e hannunshi wuri É—aya ya mata alamun dan Allah kada ta fita ta barsu su tafi da ita.
Shikuwa Ya Ameenu a zafafe yace.
"Maza mu tafi gida ba ni zakiyiwa bayani ba."
da sauri-sauri gudu-gudu tayi hanyar fita, kana shi kuma biyo ta.
Suna ƙarasawa wajen motarsa ya buɗe tare da hankaɗata ciki, ransa amatuƙar ɓace ya ja motar sukabar ƙofar gidan.
Gudu yake sosai hakan yasa cikin mintuna kaɗan suka iso G.R.A yana gama dai-dai-ta fakin ɗin motar, ya fito tare da zare belt ɗin wandonsa, ƙofar da take ya buɗe tare da figota waje, nan yashiga zuba mata belt ɗin ajikinta, kuka da ihu mai firgitarwa Zaleeha keyi tare da gudu ta nufi cikin gidan, kai tsaye ɓangaren Baban nata ta nufa.
Tana shiga tafaɗa bayan Mamy dake tsaye acikin falon, gefe kuma Baba Malam ne zaune, sai kuma Ya Ahmad da kuma Mama wanda tacika tayi fam, ƙiris take jira ta fashe ta tarwatsa musu buhun bala'i.
A harzuƙe Ameenu yashigo cikin falon, ganin haka yasa Zaleeha yin tsalle ta faɗa jikin Ya Ahmad ɗinta, ƙan ƙamesa tayi ƙam tare da ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, kuka take sosai kamar ranta zai fita don sosai ya tsutstsula mata bel ɗin,
Ya Ameenu na ƙoƙarin ƙara mata wani dukanne, Ahmad ya girgiza masa kai, alaman yabarta hakanan, da ƙyar Ahmad ya iya lallashinta tayi shiru, nan Baba Malam ya tambayeta ina take zuwa da bata kwana agidan aurenta?.
Cikin matsanancin kuka tare da tsoro murya na rawa take cewa.
"A garden nake kwana, Baba Malam wallahi ko ƙofar gidan ban taɓa fitowa ba ,
wallahi Baba Malam babu inda nake zuwa, a cikin gidan nake kwana."
Sosai sukasha mamaki, amma sanin halinta da taurin kae irin nata yasa suka yarda cewa zata aikata hakan, a hatsale Habu yace.
"To meyasa bazaki kwana cikin ɗakin kiba ko dai ƙarƙashin sirran aka nuna miki akace miki nanne ɗakin kwananki?."
kai ta jujjuya cikin tsananin tsoro dan a duniya dai Zaleeha bata son abinda zai taɓa mata lafiyan jikinta murya na rawa tace.
"Ni tsoronshi nakeji shiyasa nake fita woje."
kai kawai Baba Malam ya jujjuya dan har ga Allah shi ya yarda Zaleeha tsoron takeji dan ya santa matsoraciyace bata son abinda zai taɓa lfyarta, kana kuma duk mace budurwa akwai tsoron namiji a ranta musamman in ance mijintane tofa akwai wannan tsoron da taraddin haɗuwar forko dana biyu wasu harma na uku.
Wannan tunanin yasa Baba Malam yayimata faÉ—a tare da Nasiha, haka tayi kuka harta godewa Allah.
Mama kuwa yau saboda tsaban ɓacin ran dake cinta kasa cewa komai tayi, tuni ma tabar musu falon, don idan ta tsaya zata iya dannawa Ameenu daya dakar mata ƴa ashar babu ruwanta da surkuntaka.
Nan take Baba Malam yasa Mamy tashirya inda taɗauki Zaleehan ita da Ya Ameenun suka maida ita gidan su Saifuddeen, har gaban Ummi suka kaita, nan sukaiwa Ummi bayanin cewa wai agarden take kwana, nan sukaita bawa Ummi da shi Saifuddeen ɗin haƙuri, suka sa itama ta basu haƙurin nan su Ummi suka nuna cewa bakomai ya wuce, sosai Ummi taji tausayin Zaleehan ya kama zuciyarta, don kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa andaketa, don ga jikinta nan duk yayi wani iri, sam Ummi bataji daɗin hakan ba.
Nan Su Mamy suka kai Zaleehan har ɓangarenta, sannan suka ƙarayi mata nasiha, daga haka suka barta, inda takwanta tana meda numfashi, sosai takejin wani irin tsanar Saifuddeen ya ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, ayanzu tanajin zata iyayi masa komai don baƙanta masa, domin akansa ne aka mata irin wannan azaban.
Haka ranan dai ta wuni kuka , da yamma Belkeesu tazo nan tai ta ƙara zugata,
hakama Mama ta kirata tai ta zageta wai me take jira da gidan tunda dai ba gidan ubanta bane to tabar musu gidan.
Kada kuma ta bari wannan nakasashen ya rabata da budurcinta, harda cewa ta kwana duk inda takeso amman dai ta kare budurcinta.
Koda dare yayi kamar kullum nan ta kwana cikin garden É—in,
shiko Saifuddeen yanzu abin natama dariya yake bashi, dan in gari ya waye ta fiti kamar ba itaba, shida kanshi ya yarda tana son Æ´an uwanshi da Umminshi.
Yau kwana uku da faruwan abun ,wanda yayi dai-dai da cika kwanaki goma da tayi a gidan,
da yamma Adda Rahma tazo, duk da Raliya ta sanar mata komai amman sai takega kamar sharri sukewa Zaleeha dan yadda take nuna muso da kulawa.
ita kuwa Zaleeha harga Allah har cikin ranta take son kowa na ahlin Saifuddeen ita dai shine bata so.