Sashe 70
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Can Æangaren Saifuddeen kuwa, tunda yabar falon na Ummi, kaitsaye side É—insa ya nufa, É—akinsa ya wuce yayi kwanciyarsa, koda yaga lokacin sallan azahar yayi, banÉ—aki ya shiga tare da É—auro alwala.
Koda yaje masallaci ana idar da sallah, baiwani ɓata lokaci ba ya kamo hanyar gida. kaitsaye ɓangaren Ummin sa ya nufa, dan kuwa atunaninsa zuwa yanzun Zaleehan ta jima da komawa inda ta fito, ganin babu kowa acikin falon ne yasa shi nufar ɗakin Ummi'n, koda ya ƙarasa jikin ƙofar hannunsa yasa ya ɗan bubbuga ƙofar, Ummi da Adda Rahama wanda suke zaune sun saka Zaleehan agaba, sam aransu basu kawo cewa shi ne ke bugun ƙofar ba, atunaninsu Hayatuddeen ne ko kuma Raleeya, ataƙaice Ummi ta bada izinin shigowa.
Shikuwa Saifuddeen ganin ba'abuɗe masa kofar ba, ya sashi jan handle ɗin ƙofar ahankali ya tura ta ciki, cikin nutsuwa ya turo kekensa zuwa cikin ɗakin, ganin su Ummi zaune akan gado jigum-jigum ya sashi ƙarasowa cikin ɗakin, daf daya kusa iso Ummin nasa ne, idanunsa suka sauƙa akan Zaleeha, dake bacci tana sakin sheshsheƙan kuka, ɗan zaro idanunsa waje yayi da alaman mamaki, dan duk atunaninsa bata gidan.
harzuwa yanzu idanunta basu daina zubar da hawaye ba, kansa ya kawar gefe tare da taɓe bakinsa.
Adda Rahama ne ta dubeshi, cikin sanyi da matuƙar tausayi tace. "Saifuddeen yarinyar nan tana da matsananciyar damuwa, baƙinciki ya mata yawa, wallahi tausayinta nakeji, ka duba fa kaga, lokaci ɗaya tafige ta fita hayyacinta, bata da wani abunyi sai kuka kowa nata ya juya mata baya."
Fuska ya ya mutsa tare da sake taɓe bakinsa,
bata damu da yanayin yanda taga fuskar tasa ba, ta sake cewa. "Yanzu ya za'ayi da ita kenan? kuma ma naji jikinta da zafi sosai, kodai zaka ƙira Abban su Faruq ne yazo ya duba ta."
Cikin halin ko inkula ya É—age kafaÉ—unsa sama, alaman.
"Shifa babu ruwansa da duk wani abu daya shafeta."
Baki Adda Rahama ta saki tana kallonsa, dan kuwa koda wasa bata taɓa tunanin zaiyi fushi da Zaleehan har haka ba, tunda yake a duniya bai taɓa nuna ƙulafacinsa kan komaiba sai a kanta.
Shikuwa Saifuddeen ganin irin duban da Umminsa keyi masa ne,ya sashi murza wheelchair É—insa, kai tsaye ya fice daga cikin É—akin, ko kallon inda Zaleehan ke kwance bai sake yi ba.
Ganin ya fita ne yasa Ummi sakin ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta, hannunta takai inda ta shiga É—an jijjiga Zaleeha'n.
Ahankali taɗan buɗe idanunta wanda suka ƙanƙance saboda tsabar kuka, da wani irin firgici haɗi da tsananin tsoro ta tashi, ɗan lumshe idanunta tayi, take mafarkin da tayi yanzun yadawo cikin tunaninta, kasancewar aɗan kwanciyan da tayi har tayi mafarki wai tasake komawa gidan Baba Malam, sannan awannan karon shi da kansa yaja hannunta ya fitar da ita daga gidan, tare dayin mummunan furuci agareta, inda yace.
"Daga yau ta cire kanta daga sahun Æ´aÆ´ansa, ta manta da cewa shiÉ—in mahaifinta ne, saboda shi ya jima da manta cewa ya haifi wata Æ´a me suna Zaleeha."
wannan mafarkin shiya daɗa hautsuna tunaninta, kana ya ƙara mata fargaba me yawa acikin ranta, ƙoƙarin sakin wani sabon kuka take, Ummi ta dafa ta, cikin sanyi tace.
"Dan Allah na roƙeki Zaleeha kibar kukan nan haka, kuka baya taɓa maganin damuwa, addu'a shi ya kamata kiyi ako da yaushe, nasan da cewa Baba Malam na fushi dake, amma hakan bawai yana nufin cewa bazai taɓa yafe miki ba ne. Insha Allah zai yafe miki, sannan kada ki manta Baba Malam yana fushi dake ne saboda kin baƙanta ransa, kin kuma ƙi yi masa biyyya, to idan har Baba Malam zaiyi fushi dake har haka, Allah' n daya halicceki kuma fa, wani irin fushi kike tunanin yakeyi dake? nasan kinsan da cewa fushin Allah Yana tare da fushin iyaye da miji, saboda haka kiyi sallah ki roƙi Allah gafara, sanadin haka sai kiga Allah yasa Baba Malam ya yafe miki, sannan kisawa zuciyarki nutsuwa, da salama, tashi maza kije ki ɗauro alwala kizo kiyi sallah." Ummi ta faɗi maganar cikin yanayin lallashi. cikin sheshsheƙa ta gyaɗa kanta, tare da soma yunƙurin tashi daga kan gadon, sai-dai gaba ɗaya babu ƙarfi ajikinta, Adda Rahama ne ta taimaka mata, ita ta kamata ta kaita har cikin bathroom.
acikin toilet ɗin ma kuka take haka ta ɗauro alwala. Koda ta fito nan ta samu Ummi ta shumfuɗa mata darduma tare da aje mata sabon hijab, ganin bakowa acikin ɗakinne yasa, jiki asanyaye ta ƙarasa ta ɗauki hijab ɗin ta sanya, tare da tada sallah.
Da ƙyar ƙafafunta suke iya ɗaukanta, saboda yanda takejin jikinta ba ƙarfi.
Koda takai sujjadar ƙarshe na cikin sallan nata, fashewa tayi da wani irin kuka mai tsananin taɓa zucia, kuka take sosai tana me neman gafara awajen Allah, saida tayi kuka sosai har da shiɗewa kafun ta ɗago daga sujjadan, tana sallame sallan kuwa ta jingina bayanta da jikin gado. Ummi da tunɗazu ke tsaye abakin ƙofar shigowa duk wani kukan na Zaleeha akan kunnenta, hawayen da suka cika idanun ta ne suka samu daman gangarowa, saurin share hawayen nata tayi tare da ƙarasowa cikin ɗakin. Zama tayi tare da aje plate ɗin abincin dake hannunta, cikin sanyi ta ƙira sunan Zaleeha'n. Ɗago jajayen idanunta tayi ta kalli Umm'in, plate ɗin abincin Ummi ta turo mata gabanta, cikin kulawa tace. "Kukan ya isa haka, ki samu kici abinci." girgiza kanta tayi cikin muryarta dake rawa, haɗe da sarƙewa tace. "Bazan iyaba Ummi, bazan iya cin abinci ba, banajin daɗin bakina, komai na duniya baya min daɗi, inajin kamar ma babu yawu acikin bakina, banajin komai acikin zuciyata sai ƙunci da baƙincikin rayuwa, bana sha'awar komai yanzu aduniyata sai yafiyan Baba Malam da Hamma Saif, bazan taɓa iya cin abinci naji daɗinsa abakina ba harsai ranan da Baba Malam ya yafemin, zuciyata zafi takemin Ummi, Babana mafi soyuwa agareni yana fushi dani, Ummi Baba Malam bayason ganina, naje gidansa yasa Ya Habu ya koreni, ƴan uwana duk sun tsaneni, gashi ƴar uwata ta tafi tabarni, Adda Maryam ta bar duniya batare dana sake sanyata acikin idanuna ba, shikenan yanzu bani da wata Adda aduniya, Inama mutuwa ni ta ɗauka ba ita ba, inama da ace mutuwa zatamin gata wajen kusantani da ƴar uwata, bazan iya jure fushin Baba Malam akaina ba Ummi, nima mutuwa zanyi Ummi.....".
Kasa ƙarasa maganan tayi, sakamakon kukan me tsananin ƙarfi da ya ƙwace mata, Ummi kanta kasa daurewa tayi, hakanne yasa ta jawo Zaleehan jikinta ta rungume.
Jinta ajikin Ummi yasa ta ƙanƙame Ummin tana kukan fitar hayyaci, mai ɗauke da tsananin dana sanin abun da ta aikata a baya.
Hawayene suka silalo daga cikin Idanun Hayatuddeen, wanda duk wani kalaman da Zaleehan ke faɗa, ya jisu raɗau akan kunnuwansa, dan yajima tsaye abakin ƙofar batare da sun san da zuwan sa ba, sosai jikinsa yayi sanyi, dajin kalaman nata, domin dama Raleeya ta faɗa masa cewa, Zaleehan har suma tayi ɗazu, shine Ummi ta ɗauketa takaita ɗakinta, jin cewa Adda Zaleehan na ɗakin Ummin ne yasashi nufo ɗakin, saboda halin ko inkula daya nuna mata ɗazu, yasan dole zataji ba daɗi acikin ranta.
Ahankali ya shiga taka ƙafafunsa wanda sukayi masa nauyi, ƙarasawa inda suke yayi, tare da zubewa akan guiwowinsa, cikin wata irin murya dake fitar da tsananin rauninsa yace "Adda Zaleeha, meya sameki? meyasa kike kuka, dan Allah kibar kuka kinji."