← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 90

Sashe 90

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Majeederh na tsaye tana haɗa fruits salad,ta idar da sallar zhur ɗinta kenan ga zuma a wani ɗan silver kwano mai kyau tun daga bakin ƙofa ta ji ana cewa "Aby, Mimi we're back" Ta sauke lallausan murmushi tana juyawa idanunta ya sauka akan jaruman yaran nata wanda suke da shekaru 20 20, amma girman jikinsu yafi na ɗan 25 zuwa 30 Al'hussain ya ƙarasa ya rungumeta ya ce "I miss you so much Mimi, Our Fulani Kingdom" Ta rungume shi ta ce "Welcome darling" Alhassan ya haɗe fuska hannunsa zube cikin Aljihu suit ɗinsa sai ɗaɗɗaga shoulders yake daidai nan Takawa ya fito an fara manyanta ya ɗan saki tattausan murmushi idanunsa akan Alhassan da sauri Alhassan ya rungume Takawa ya ce
"Aby.." Takawa ya ce "Prince! my photocopy" Gabaɗaya suka zauna Arjun ya shigo ya nufi wajen Majeederh domin jin kansa yake kamar auta gabaɗaya a lokacin shi kansa Takawa bai san akwai shigar ƙaramin ciki a jikin nata ba, ta ce "To ƴan Singapore ya ƙasar?" Al'hussain ya ce "Good" Alhassan baiyi magana ba idanunsa rufe bacci ya ke ji can ya buɗe ido ya ce "Where is Soha?" Daga baya aka ce "am here brother" cikin masifa ya ce "How many times zan faɗa miki ki daina posting pictures ɗinki a social media, more especially Twitter? How many times eh?" Ta yi shiru Yaa K ya ce "Masifaffen gidanmu ya dawo, Allah ya baka haƙuri ba zata sake ba daga yau" Takawa Khalil kallon yaran nasa yake musamman da Noha ta shigo yanzu daga school itama ya juya ya kalli Majeederh ya lumshe idanunsa a hankali ya ce "Alhamdulillah" Da daddare Takawa yana turakarsa ya gama shirin kwanciya Majeederh ta shigo ya bita da kallo sosai can ya ce "You're pregnant" Ta buɗe ido sosai ta ce "How do you know?" Ya ɗan watsa mata kallon So kafin ya ce "Idan kina da ciki kinfi buƙatar Takawa fiye da ko wanne lokaci" Ya miƙa mata hannu ta kama ya zauna tare da ɗorata a cinya yana shafa cikinta can ya ce "Queen Majeederh" Ta ce "Sarkina" Idanunsa rufe ya ce "ALLAH ya yi miki Albarka, ke ɗin ƴar Aljanna ce" Ta rungumesa ta ce

"Mata da yawa na cewa; duk wacce ta ɗauki Miji uba zata mutu marainiya, Jarumin mijina ya rusa wannan faɗar tasu a zuciyata, haƙika babu wani abu mai muhimmanci ga rayuwar mace wanda ya a shige gidan mijinta, domin shi ne ni'imarta, kai ɗin tsagina ne, kamar yadda bango ba zai zauna ba sai da tsaginsa, kamar yadda kifi ba zai rayuwa ba sai yana cikin ruwa, haka zalika rayuwa bata yiyuwa sai da numfashi a ƙirjin mutum, mizani da idan ba ruwa ba ɗan adam gwargwadon yadda ƙaddarori suke juyewa zuwa abu mai kyau shi ne tubalin yadda Majeederh ba zata iya rayuwa babu mijinta Mai martaba Ibrahimul-khalil ba, duk wanda yake tunanin zai rabamu ya ɗauka mafarki yakeyi, kamar yadda duk wanda ya ce wutar kara ta kwana to shi ne ya kwana bai yi bacci ba, Malama da MIJIN MALAMA mutu ka raba, ko ita ina fatan ta fara ɗauke ni kafin Takawa". Takawa ya rasa bakin magana sai kawai ya rungumeta sosai yana jin ta cike masa komai na rayuwa baya buri daya shige ya kyautata mata ta zama cikakkiyar House Wife bata da aiki sai na kula da mijinta da yaranta, a hankali ya shiga kissing ɗinta tun suna zaune har suka zame suka sauka ƙasan carpet daga nan kuma suka faɗa wata duniyar ta daban, kasancewar sun jima rabon su da Naija ga kuma yanzu Fatymerh ta haihu yasa Takawa saka Alhassan ya fara musu shirye shiryen tafiya cikin kwanaki biyu jirginsu ya ɗaga, Alhassan farin cikinsa ɗaya akwai wacce idanunsa yake son gani, Soha bata wani farin ciki domin bata damu da wasu family ba. A gidansu suka sauka a daren kuma Majeederh ta nufi gidan Fatymerh domin shirye-shiryen suna, Takawa ya dinga juyi ya kasa bacci matarsa kawai yake buƙatar gani da jin ɗumin jikinta ya duba agogo yaga ƙarfe biyu, jallabiya ya saka ya fito ya shiga mota, yana fita Alhassan ya fito a daidai lokaci guda suka isa gidan Akeeth kowa ya yi parking motarsa daga nesa da gidan, Khalil ya manta matsayinsa na sarki ya leƙa yaga ba kowa sai mai gadi ya kama katanga ya durga ciki, Alhassan ma ya durga Khalil bai san da zuwan Alhassan ba, amma shi Alhassan yana ganin mahaifin nasa. Ɓangare daban-daban suka nufa Alhassan wajen Abra, ya bi ta window ya shiga bedroom ɗin ta. Majeederh na tsaye tana ƙoƙarin kwanciya a gajiye take sosai kamar daga sama taga an diro ta window an kuma kashe switch na bedroom ɗin, tana ƙoƙarin yin magana aka rungumeta ta baya, a hankali ya manne mararsu waje guda a kiɗime ta ce "Who are you, wa..waye?" Yaƙi magana hannunsa ya sanya ya farke ƴar rigar baccin dake jikinta yana sake rungumeta tare da shinshina wuyanta ta ce "Waye?" Muryarsa na rawa saboda abubuwan da yake ji da ƙyar ya iya furta maganar cikin ƙasa da murya ya ce "MIJIN MALAMA".

Allhamdulillah!
Komai ya yi farko yana da ƙarshe, ba zan ce labarin nan ya yi 💯 hundred patient ba, duk iyawarka dole ne ka samu kuskure ta wani gefen, ɗan adam ajizi ne mu zama masu uzuri. Bana da ƙarfin qiwar cewa na iya, amma ina da yaƙini na abinda zuciya ke ayyana mini harna rubuta, ba zance Rubutana yafi na kowa ba, domin ban san kowa ɗin ba, abu ɗaya na sani nawa Al'ƙalamin a kaifafe yake musamman ta ɓangaren zanen ƙaddara, ban yarda akwai happily ever after ba, ba kuma zan taɓa gasgata akwai zama na har abada tsakanin ma'aurata babu wani tasgaro ba, ba zan lamunci rashin jarabta ba, domin ƙara gasgata imanin mutum ƙaddara take, ban yarda jarumi baya mutuwa ba, domin kullum akan idanunmu mutane sun sha mutuwa, Miji ya mutu, mata ta mutu,ko iyaye, kenan zanen ƙaddara na rubutun ƙagaggen labarin daya samu nagarta ga mai yinsa done zanen ya zo mana haɗe da sunan mutuwa, a zamantakewa dole mu yarda da Sadaukarwa kuma tilastawa kanmu fahimtar ba komai muke nema mu samu ba, ko da alheri ni garemu SOYAYYA a zane take da rubutacciyar Tawada a rayuwar ko wanne. Kullum mata sune masu rauni, kullum sune suke wahala a labari shin baza kuzo rawar ta sauya zani ba? Kullum cikin force marriage ake ba zaku so wani abu wanda ba wannan ba? Me ya sa kawai namiji ke ganin mace ya ce yana so, ita macen bata da zuciya ne?.... Mu tara a littafina na gaba.

Na gina labarin Mijin Malama akan tasirin Ƙaddara, yarda da ita a matsayin mutum Musulmi, illar da ƙawaye sukewa aminansu, da kuma sadaukarwa, komai girman tawadi'unka da ilimin Addinin da kake da shi Ubangiji na iya jarabtarka, haka JINKIRIN AUREN na zuwa ta hanya daban-daban.

Godiya.
Na gode sosai bisa jumirin bina da kukai tun daga farko har ƙarshe, godiya ga Arewabooks followers wanda bakwa gajiya da sanya kuɗinku wajan siya, ALLAH ya ƙara arziƙi wadata da imani y sanya kuci gaba da bibiyata a ko wanne littafi.

Tambaya?
1.Mene kuskuren labarin?
2. Dame ka ƙaru a labarin?
3. Mene yafi birgeka a labarin?
4. Mene saƙonka zuwa ga marubuciyar MIJIN MALAMA?
5. Wanne kallo ku kaiwa rayuwar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan da Dr Ibrahimul-khalil?

6. Wanne salo kuke son na sauya a labarina zuwa gaba?.

Ina da labarai uku masu inganci ko wanne yana da amfani kuma sun sha banban da Mijin Malama na rasa wanne zan muku next faɗi zaɓi ka wanne kafi so?

1.JOURNALIST LATIF
{Allah yana gani}
2. RUHI BIYU
3. MUNAFIKIN MIJI
4. ÆŠAN MALAM

Yi comment da wanda ka fi so, wanda aka fi zaɓa shi za a fara yi, kuma zai fara sauka ne a Arewabooks.

COMMENT
FOLLOW MY ACCOUNT ON AREWABOOKS

NA'IMA SULAIMAN SARAUTA
NIMCYLUV
08119237616
Kuyi magana na yi adding naku group É—ina mu tattauna.
Chapter 90 · 0% Book details