Sashe 87
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Innati ta sharce majina ta ce "Ƙarara baki babu linzami a dinga Sakin tsurar zance? Dafa a makarantun islamiyya ya faɗi haka a gigice zasu dinga salatin Annabi, ana kaɗa zunubin can wani wajen, ƴar bulala ɗari da tamanin ɗin nan yi masa ita za su yi"
Majeederh ta yi shiru, Aaliyyah sai dariya take ta ce "Ni a shawarce da islamiyyar kika mayar da shi Innati" Ta yi caraf ta ce "Waa? Ubana daya mutu zai dawo kenan ashe, yanzu da an yi magana ya ce Mijin Malama? Haka Kululu take? Asstagafirullah!" Aaliyyah ta ce "To Allah ya shirya shi" Da sauri ta ce "Amin don nabiyyun rahamati, idan ba zai shiryu ba Allah ya ya fe masa" Ta juya ta kalli Majeederh ta ce "Mijin naki batsa ya yi fa? Ko ba ki ji bane?" Kafin ta ce komai Ƙhulud ta shigo da plate wanda yake cike da zallar gasasshen nama.... Washegari aka Raɗawa yara suna Hawwa'u Ibrahim Khalil da Fatima Ibrahimul-khalil, wanda suka ci sunan Fulani da Gimbiya ana kiran su da Noha da Soha, faɗar shagalin da akai ɓata baki ne, duk da cewar family biyun basu da cikakken yawa amma Majeederh ta samu arziƙi daga jama'a, hatta Barrister Aliyu Sufyan sai daya bawa babies gift Khalil dai bai ce komai ba, haka Akeeth wanda suka zama friends shi da Khalil, hatta P.a Hammad sai daya basu mahaukatan kaya wanda suka jone shi da Badi tun a Naija har zuwa matakin da zai aureta.
Sarewar dake tashi a hankali wacce ta karaɗe Palace bakiɗaya cikin ƙanƙanin lokaci shine ya fargar da jama'a zuwa ga abinda yake faruwa acikin masarauta. Su Mami gabaɗaya suka fita domin bawa Idanunsu abinci Majeederh dake zaune kiɗan na ratsata jinin sarautar nata ya motsa ta miƙe a hankali tare da nufar waje, cak ta tsaya daidai window tare da ɗagawa idanunta ya sauka akan gwarzonta Dr Ibrahimul-khalil kuma Mai martaba Ibrahim Khalil na 4, a hankali ta dinga binsa da kallo jinin jikinta na tsinkewa ganin wani irin kyau da ya yi mata wanda bata taɓa ganin irinsa ba, farar jallabiya ce a jikinsa ƴar gasken, an ɗora masa jibgegiyar golden Silver ɗin Alkyabba mai mugun tsada, fuskarsa zagaye da rawanin hiramin daya ƙara fidda tsagwaron kamala da tarin haibar dake kwance a fuskarsa, baya murmushi ko kaɗan ya kame kansa idanunsa ya buɗe tare da lumshe su, komai ya gundire shi tashin hankalinsa bai shige kiɗan da ake masa a ka ba, da surutan jama'a. Jajayen laɓɓansa sun jiƙe da damshin yawu tunaninsa ya tsaya cak sanda ya gama tabbatarwar da kansa fa yau shi ne jagoran mutanen Saudiyya? Nauyi da hak'ƙin nasu yana rataye a wuyansa.
"Ya Allah" Ya furta a zuciya bisa mamakinsa kuma harshen shi ya ƙara nauyi fiye da ko wanne lokaci, jinkimar shi da kame kansa sun ƙaru fiye da ko wanne lokaci da rana na tsayin ranakun da ya yi a rayuwarsa, a hankali wata nutsuwa ke sauk'a tana mamaye jikinsa ya rage babu wani jini da ya yi saura a jikinsa sai na sarauta. Majeederh ta yi saurin ɗauke idanunta ganin ya bar sashin fada ya nufo cikin gidan kai tsaye sauran mutanen fada suka tsaya. Da sauri ta shige bedroom ɗinta tana nufar gaban mirror, Khalil kai tsaye sashin Ummie ya nufa ya sameta zaune akan bed tana duba sauran turarrukan da aka kawo mata, idanunsa da suke yawo a kanta ya tabbatar mata da cewa shi ne, sabon Takawar Masarautarsu, ta ɗaga kai suka haɗa ido ganin nasa ta yi jajur ta ce "Ranka ya daɗe?"
A hankali ya zame rawanin kansa ya ƙarasa wajenta ya ɗora kansa a cinyarta, yana sakin ajiyar zuciya sun jima haka kafin ya ce "Me kika fahimta a labarin rayuwata Ummie?" Ya ɗan yi jim ya ce "Karki duba bangon labaran cikin littafin kawai"
Ummie ta ce "Idan zan fasalta rayuwarka dole na fara daga farko, bangon littafi shi ne abu na farko da jan hankalin mutane zuwa ga sanin abinda yake ciki, rayuwa dole ce ga dukkan mai rai dake wanzuwa a duniya, mutuwa gaskiya ce hisabi dole ne, a wannan littafin naka dole aga sunan Majeederh zane a ciki, kai tsaye zan iya basa suna MIJIN MALAMA, babu komai cikin littafin zai ZANEN ƘADDARA" Yana sake kwanciya kan cinyarta ya ce "Me hakan ke nufi Ummie?"
"Khalil rayuwa ba tabbas, zanen ƙaddara ne ya yi aikinsa cikin littafin nan, da kuma muhimmaci yarda da ita a matsayin mutum Musulmi, muna numfashi da ƙaddarorinmu a jininmu, kasan me yasa na ce sunan labarin littafinka MIJIN MALAMA? Na farko a ƙaddarorin Majeederh akwai farin jini wanda ya tara mata ma nema da yawa kuma a ɓoye dalilin asirin da akai mata, shi yasa ba a san da su ba, kayi rayuwa da ita kana ƙarami ka sake rayuwa da ita a karo na biyu, kuma a hakan kai ba Musulmi bane, bayyanar warwaruwar baƙin ƙullin daya shuɗe da rufewa ya sanya ma neman yin caa" Ta yi shiru can ta ce
"Kasan zaka sameta matsayin mata? Kasan zaka yi rayuwa da ita? Kasan zata haifa maka wannan zuri'ar?" Gently ya girgiza kai ta ce "Why? Me ya sa baka sani ba?"
Ya yi jim kana ya ce "Ina ganin ban cancanta ba Ummie, akwai wanda suka fini nagarta, shekaru, sanin daidai ga ilimi babban dalilin da bata so na" "Good" Ummie ta furta tana shafa kansa ta ce "Bata auri Alpha ba ƙaddarar su ce haka, Ubangijin bai ƙaddara zata aure shi ba, ta auri Abuturab bata zauna da shi ba, ranar data aure shi, shine ya fara amsa sunan Mijin Malama, da Allah ya ƙaddara wa Majeederh aure da yawa to duk wanda ta aura sunan da zai amsa kenan MIJIN MALAMA daga bakin jama'a, dalili a nan ita ce _MALAMA_ akanta labarin littafinka ya fara rubuta “headline†kasha wahala wacce ta kai ka zuwa matakin da kake a yanzu, dalilin Malama kayi rayuwa bisa saka hannun Ubangiji da yarda haɗi da amincewar shi, dalilin Malama ka samu tarbiyyar daka rasa wajen iyaye, dalilin Malama ka fara sanin daɗin Ahali, dalilin Malama ka fara karatu, Allah ya ƙaddara zaka kasance Musulmi ko wacce ƙaddara mai kyau ko mara kyau akwai sanadi, dalilin Malama ka musulunta, dalilin Malama kasan asalin iyayenka, dalilin Malama kasan waye Mahaifinki" Ta jinkirta ta ce "Idan baka amsa sunan MIJIN MALAMA ba waye zai amsa?" Ya riƙe numfashi da kyau yana riƙe hannun Ummie ya ce "No one has been as lucky as Ibrahimul-Khalil, the son of Ummie, the husband of Hawwa, the father of Alhassan and Al'hussain, the king of Saudi Arabia"
"Ma sha Allah, rayuwa cikin farin ciki no more challenges, babu wani tashin hankalin da zai ƙara zuwa ya rusa farin cikin, Ibrahimul-khalil, Ɗan Ummie, mijin Malama, uban Alhassan da Al'hussain sarkinmu na yau da gobe Takawa Khalil" Ya ɗan sauk'e numfashi yana jin wani abu na tsarga masa, a hankali ya miƙe ya fice tare da nufar sashin Queen Majeederh, takunsa bisa duga-dugensa wanda ke nuna tsantsar lafiyar gangar jikinsa dana zuciya. Tsaye ya ganta ta juya baya tana kallon makaken photonsa wanda Fatymerh ta maƙala yanzu, ya ɗaga kansa ya kalli photon a karo na biyu ya sake ware gajiyayyun idanunsa akan frame gabaɗaya ba a jima da yin photon ba, har an yi frame? Aikin Rohaan ne da dukkan alama photon daya gama zaga internet ko wanne sarki gwamna da manya suna posting a twitter akan taya sabon Sarkin Saudiya murna. Ta juya ta kalle shi shima ita ɗin yake kallo cike da sahihin so wanda yake fitowa daga ƙasan zuciyarsa idanunsa ke bayyanar da motsin ji, na daga tafiyar gudun zuciyar tasa, komai nasa ya bubbuɗe. A nutse yake bin jikinta da kallo kayan sunbi jiki tare da zama daram, ya kalli ƙirjinta daya sake cikowa hakan ya haifar da dagulewar riƙon da ya kewa yanayinsa a fili, rauninsa ya bayyana, ya zubawa yatsun ƙafarta dake shimfiɗe zane da ƙunshi kallo, ya juya idanunsa zuwa faffaɗan mazaunanta da suka buɗe sosai asalin dirinta ya bayyana, baya jure kallon idanunta. ganin bashi da niyyar motsawa ta nufe shi tana tafiya jikinta na rawa wanda ta ke yinta cike da gayya hannayenta ta buɗe tare da zagaye shi ta rungumesa tsam a jikinta, hot tears na bin kuncinta, full of love and passion for her husband, she hugged him again, slowly take magane "Ma sha Allah, Alhamdulillah ina taya Takawa murna, Ubangiji ya baka wuyan ɗauka da sauk'e hakƙin jama'a, na yi farin ciki sosai Takawa" Khalil ya kasa cewa komai saboda jinkansa yake kamar ba Khalil ba, wani daban ne, nauyin kansa ya masa yawa, He believes that any success that a man will get in life, it does not happen without a woman by his side, dalilin Majeederh ya cimma burikansa, duk wani long and short terms na goals ɗinsa ya yi Achieving dalilin Malama ba zai taɓa manta sunan Mijin Malama ba, a shekarun da basu shige huɗu ba ya samu cikar victory ɗinsa, me zaiwa Ubangiji banda godiya? Ba zai taɓa butulce masa ba ga tarin darajojin daya bashi.
Majeederh ta ɗan bubbuga bayansa a hankali tana shafa kansa ta ce "Ba lokacin ƙunci ko damuwa bane yanzu a gareka ba Takawa, lokacin farin ciki ne ka zama mai godiya a koda yaushe Sarkina" Ya sauk'e numfashi he needs a shoulder to lean on and cry, he feels like he's going to cry but he can't, ya sake matseta a ƙirjinsa, naman jikinsa na rawa zufa na yanko masa laɓɓansa na karkarwa saboda maganar da yake tattarowa cikin tsananin wahala yana matseta a fusge ya ce "Thank you My Queen" Yana ƙara riƙeta ya ce "Thank you, thank you And i love you"